Sashe 44
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ranar kawai yace na shirya muje gidan Adda Fati mu gaisheta nan da nan na fara Murna, bayan la'asar muka tafi muna hanya ya kalleni ya na fad'in"Haka zaki je baki rike musu komai ba?
Sai nace"To me zan siya musu?
Kallona ya yi batare da ya yi mgana ba, sai da ya ga mun zo wani shago yace mu tsaya ya fita da kansa sai gashi ya Dawo da Leda cike da Biskit da Chaculet da Sweets.
Wani abu na bani mamaki game da Assadiq bayan kashe wayarsa da kuma rashin yin waya a gabana sai kuma yadda ya ke kashe kudi ahalin nasan ba shi da sana'a mai karfi asalima ya na karkashin wani ne.
Kuma a yanayin kashe kudinsa bai yi kama da wanda ke karkashin wani abu.
Duk da yace gwamnati na Biyansu ammh kudin da ya kashewa ya fi karfin kudin da ya ke da shi.
Na kasa yi masa mgana ganin kamar ba Hurumina ba ne
Adda Fati da Mijinta kamar su goyamu Adda Fati Bakinta yaki Rufuwa ita da Habiba da ta Dawo daga Islamiya.
Tare suka fita masallaci da Baban Hanif suka dawo suna falo suna Hira ni kuma muma ciki muna Hira da Adda Fati ta na faman tambayana ya yanayim zaman mu? Nace mata lafiya lau ko matsalan su Ummi ban fad'a mata ba.
Kallona ta yi kafin tace"Ya mganar zuwa dake chan garin na su?
Sai na kasa ce mata ban masa mgana ba sai kawai nace mata yace zamu je in ya samu Lokaci.
Adda Fati tace"Gaakiya ki takura masa ya kamata kuje ki ga yan'uwansa suma su ganki."
Sai na jinjina mata kai alamun to ina jinta ta na ta min bayanin Fa'idar haka ciki har da Tunanin kada mu zo mu fara tara zuru'a.
Sannan ta tambayeni ko a waya bai tab'a had'amu mun yi mgana da kakar tasa ba?
Nace mata a'a bai taba bani ba araina nace shi wannan wayar tasa ma ai ban taba ganinta ba koda yaushe tana jikinsa.
Achan falo ma haka Baban Hanif ya tasa Saddiq da Tambayoyi shi kuma ya na bashi amsa a takaice.
Tambayar da ta basa mamaki shine da Baban Hanif yace"Wani aiki ku ke yi ne kai da megidan naka?
Sadiq ya kallesa kafin yace"Gwari mu ke yi harkan gwari ne"
Baban Hanif ya kallesa ya na mamakin kalamansa shi dai a jikin Sadiq bai yi kama da mai gwari aikin Wahala ba.
Sadiq da ya Fahimci haka sai yace"Muna zuwa gari gari har kudu ma muna zuwa."
Sai Baban Hanif yace"Allah ya taimaka shi megidan naka anan garin ya ke?
Sadiq ya yi saurin cewa"A'a a chan kano ya ke."
Tun kafin Baban Hanif ya watso masa wata tambayar ya mike ya na fad'in nazo mu tafi kada mu yi dare a hanya mu kasa samun abun hawa.
Sai Baban Hanif ya tashi yaje kirana muna Tsaka da Hira da Adda Fati ya leko yace mijina yace na fito mu tafi.
Hijabina kawai na saka na fito Adda nata Godiyar tsaraban yara.
Har waje suka rakamu ita da Habiba da Baban Hanif.
Da kafa muka taka har bakin Titi sannan muka samu Adaidaita zuwa gida.
A hanya ya tsaya ya siya mana gashashiyar kaza da Madaran Holladian, muka koma gida muka ci sannan muka kwanta sai na lura kamar Assadiq yana cikin Damuwa yau ko kallon bai kunna mana ba ya kwanta ya rufe ido.
Ganin haka nima sai na shiga ciki na kwanta.
Sadiq ya dad'e bai yi barci ba ya na Tunanin wani abu tunda yan'uwan Hasiya suka fara damuwa da Sanin Danginsa yasan akwai matsala.
Shi gabadaya ma yan'uwan nasa Fushi ya ke da su tun abunda ya faru kafin tahowarsa.
Sun kikkirasa duka yaki Daga wayarsu, Umma ce kawai ya ke Daukan wayanta sai Abba sannan Sultana ma na kiran shi abun da ke ba shi mamaki sai ganin sakoninta ma su kama da na Soyayya da kulawa da ta ke Tura masa shi kuma bai tab'a kiranta ko sau daya ba.
Yasan shi ne karami ne acikin su ammh yasan yadda Mata suke jan Ragamar bata gida in dai suka yi yawa a waje.
Bazai bari su shiga rayuwarsa su takura masa ba, kowacce taje taji da gidanta da Mijinta da ya'yanta.
Sannan ya fara lura da in bai jajirce ba Ko auran Sultana ya yi su za su rika Tafiyar masa da matarsa shiyasa ya Tauna aya domin tsakuwa taji Tsoro.
Big sis ce ta Turo masa sakon ya yi hakuri ya kirata za su yi mgana shi kuma baya so Hasiya ta Fahimci wani abu Shiyasa sau tari ya ke barin wayarsa a kashe.
Sun yi mgana da Tahir sau biyu kuma bai taba sanin baya Gusai ya na zariya ba sun yi mganar zasu dawo zariya Lokaci d'aya.
Ya kwana da tunanin yadda zai tambayi Hasiya abunda ta ke so ta fara sana'a in ta samu jari so ya ke komai ya kare kafin yan'uwanta su gano abunda ya ke boyewa.
Sannan Tausayinta ya ke ji shiyasa har alokacin ya kasa aiwatar da Tsarinsa.
Washegari kuma Ramatu ta kirani tana gayamin Noor ba lafiya sai na gayamasa sai yace anjuma muje mu gaisheta
Kamar zuwan Adda Fati da Yammah mukaje gidan Ramatu cikin sa'a muka samu Nura ya dawo suka had'e da Sadiq suna ta Hira ni kuma muka kule ni da Ramatu ita kadai na fad'a ma yadda muka kare da su Ummi.
Ramatu ta yi mirmishi kafin tace"Kin manta na taba fad'a miki gangariyan miji na nan zuwa gare ki Hasiya?
To shine Sadiq ina da tabbacin shine wanda zai zama bango gareki har Abada Hasiya kuma shi zai zama kariyar kuma wanda zai tayaki wajen karb'an duka Kaddarorin ki."
Sai na kasa musama Ramatu saboda nasan gaskiya ta fad'a Assadiq mutun ne mai hange nesa da sanin Zahirin Rayuwa.
Nan ma sai Dare muka koma gida sai da muka ci abinci shinkafa da wake da Miya da Salat, tare duka muka ci abinci da su muna cikin cin abinci ne Ramatu ta kalleni ta na fad'in"k'awata ba ni shawaran wani sana'a zan fara Abban Noor ya bani jari"
Tun kafin na kalleta Assadiq ya kalleni domin yaji me zan ce, sai kuma yaji nace"To wani sana'a zaki fara?
Kai Tsaye tace"Shine na ke nemen shawaran ki"
Shuru na yi kamar me nazari kafin nace"kina da Fridge ko?
Sai ta dagamin kai sai na cigaba da Fadin"To ki fara saida Ruwan sanyi mana ki gani? Ko kuma ki had'a da Suya milk in ya amsu shikenan."
Ramatu ta yi jim kafin tace"Eh to zan gwada na gani kaji Shawaran Hasiya Abban Noor?
Nura na gefe yace"Sai ki gwada ki gani Allah yasa albarka."
Sadiq na gefe ya kalli Ramatu kafin yace"To ita ki tambayeta in ta samu jari wani sana'an zata fara?
Ramatu ta kalleni nima na kalleta sai na nuna kaina ina fadin"Wai ni?
Ta na Dariya tace"Hasiya mamman kona ba."
Cikin daga ido nace"Tab ai in na samu wasu kudad'e yanzu dubai zani na Saro zannuwa da kaya dogayen Riguna da su takalma ina so na zama yar kasuwa Sosai."
Ramatu ta yi dariya kafin tace"Lalle wa yahga Hajiyar Dubai."
Nura ya kalli Sadiq kafin yace"To kaji sai ka Shirya ka kusa zama mijin Hajiya."
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba daganan sai aka Rufe mganar sana'ar muna gidan har wajen goma saura sannan suka rakamu muka tafi.
Har na ma mamta mun yi wannan mganar sai washegari da rana ya kirani ya na zaune afalo.
Bayan na zauna a gabansa ya Tattara natsuwarsa ya fara fad'in"Da gaske kina son ki fara kasuwanci Hasiya?
Kai Tsaye nace"Sosai ina son na zama babbar yar kasuwa watarana"
Cikin jinjina kai yace"Baki sha'awar ki cigaba da karatun ki ne?
Sai na yi shuru ban yi mgana ba sai da ya kara maimaita tambayarsa sannan nace"In na samu damar haka bazan ki komawa makarantar ba."
Daganan bai karamin maganar ba ni kuma sai na Dauka kawai ya Tambayeni ne saboda hirar da muka yi a gidan Ramatu.
Shi kuma har ga Allah alkwarin da ya yi ya ke son cikawa in yace zai maidani makaranta lokaci ya kure sannan maganar kasuwancin da nace zan fara sai yaga kamar yafi sauki gwara dai ya fara bani jarin da zan fara kafa kaina kafin ya rabu da ni.
A daran ya kunna mana wani Turkish Film muna kallo muna zaune a saman kujera na zaman mutum biyu.
Na'urar na saman Cinyarsa ni kuma ina ta gefensa muna kallon tare.
Gajiya nayi da Tura kaina, duk wuyana ya sage ganin haka yasa da kansa ya ja kaina ya Dora saman kafad'arsa.
Muka bi juna da kallo shi ya fara Dauke idanuwansa kafin yace"Zaki fi jin dadin kallon a haka."
Sai ban yi mgana ba na gyara kaina saman kafad'arsa.
Ana cikin kallo kawai ni bansan ya akayi ba sai ganin nayi jaruman Film din namiji da macen suna kissing din juna.
Gabadaya sai falon ya yi shuru daman ba Wuta kuma mun kashe Fitila ssai hasken kallon ne ke haska Fuskokin mu.
Kura musu ido nayi ina kallonsu shima ta bangaransa kamar kuma an dasa idanuwana, shi ma kuma ya kasa tariye wajen.
Shine kuma a baya in dai yaga za'ayi irin wannan abun sai ya yi saurin Tariye wa zuwa gaba.
Ammh yau kuma kamar an dasa Hannunsa ya kasa gaba ballatana baya ammh a cikin jikinsa ya na jin Saukan Numfashina wanda ya had'e da Dumin jikina ya fara sauya yanayinsa gabadaya.
A tare muka d'ago muna kallon juna shi idanuwansa da wani ruwa ruwa aciki ni kuma idanuwana Tarai tarai sai dai sun fara kankancewa.
Bazan iya sanin ta ina abun ya faru ba ni dai naji hannun Assadiq acikin hannuna ya Damke daganan bansan yadda akayi ba sai ganin bakinsa na yi Daf da bakina.
Daganan kuma sai na tsinci kan mu da aikata abunda na cikin Film din da muke kallo suke aikatawa wato kissing kuma kissing din na baki cikin baki ne.
Bansan yadda akayi ba ni dai nasan na fita Hayyacina shima Assadiq din jikinsa na rawa ya kama kaina ya Rike gam yana totsan bakina da Harshena kamar Allah ya aikosa
Ba dadi nake ji ba sai dai tsoro da bazatan yanayin sannan da Zafin da Radad'in da Harshena zuwa bakina ya ke yi.
Allah bai kwaceni ba sai dai muka ji karar fad'uwan abu sannan ya iya sakin bakina.
Ashe Laptop din ce ta sha kasa ni kuma ina ganin haka na kwace jikina na ruga da gudu cikin d'aki na Rufe kofa kunyar duniya duk ta gama sauka a kaina.
Kan gado na kwanta ina maida Numfashi ina kuma shafa bakina inda ya Dau rad'adi D'au saboda azaban tsotsa.
Sadiq achan falo kuwa mamakinsa kansa ya ke yi me ya same shi ya kai shi ga aikata abunda baya cikin Tsarinsa? Laptop din ya Dauke ya kashe ya ijiyeta nan saman kujeran shi kuma ya koma ya kwanta ya na kokarin yaki da abunda yake ji na son kara jin Dumin bakin Hasiya acikin bakinsa.
Duk juyawar da zai yi sai yaji kamar alokacin ne yake kissing dinta ya taba bakinsa yafi a kirga shi kad'ai kawai ya na ta Mirmishi in ya Tuna.
Wannan ne Kiss dinsa na Farko a Rayuwarsa kuma ya zama wani na musamman.