← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 75

Sashe 51

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakyar a Daddafe ya yi sati biyu a gusai ya yi ma su Abba karya Tahir bai jin dadi zai je Daura ya Dubasa.
Da wannan Damar kawai ya tsinci kansa a zariya Saboda Hasiya.
Yaje ya iskeni duk na Rame saboda kadaici da rashinsa.
A tunanina wani abu ne munmuna ya same shi tunda ni an riga an canfani ina da Farar kafa da bakin Fenti.
Da na ganni gani ga Assadiq bansan sadda na daga tsalle na Rumgumesa ba.
Shima haka ya kamkameni yana jin wani farincikin da tunda ya koma Gusai ya rasashi.
Ranar ko girki ban yi ba tare muka fita mukaje muka ci abinci, washegari kuma Tun safe har dare muna tare da juna bansan haka zuciyata ta shaku da Assadiq ba sai a lokacin nake jin araina zan iya shiga wani mummunan Hali in na rasaahi.
Shima kuma hakan ne ya shaku da ni sosai, ballatana bakina da baya gajiya da saka bakinsa cikin nawa sannan Hannayensa basa gajiya da kara kaina a sassan jikina.
Sai ga Shi daga kwana Biyu sai da ya yi hud'u sannan ya Dawo gusai bayan ya yi min cefane mai yawa kuma ya karamin wasu kud'ad'e ina kuka haka ya tafi ya barni.
Shima din su Umma ne suka Damesa da waya yana Tunanin kada su ce zasu kira wayar Tahir komai ya Lalace.
shiyasa ya koma ammh ba domin ya gaji da Hasiya ba.
Yana komawa ko sati bai yi ba yaji Gusau ta fita kansa Burinsa da Tunaninsa ya koma Zariya ya zauna tare da Hasiya
Duk ya gama Tunaninsa ya Hango cewa ba shi da wata mafita sai na bin abunda zuciyarsa ke muradi.
Ba tare da sanin su Umma ba Abba kad'ai ya yi mganar da shi ya fara neman Gurbin Masters d'insa sannan kuma ya karbi tayin da kamfani Dismento Nigerian Limited da ya yi bautar kasar suka yi masa na aiki da su.
Da wannan Damar ya samu cikakken Lokacin tafiya zariya, ammh sai yace ma su Umma wasu takardunsa zai karbo achan cikin makaranta.
Kuma da hakan ya ke samun zama tare da Hasiya ko da wani lokaci.
Bai fad'a ma kowa mganar karatunsa ba sai da komai ya kamallah sannan har kamfanin sun ba shi Accepted Letter aiki kawai zai fara da su.
Umma najin batun komawa Zariya tace bai isa ba ya maganar sultana? Ba shi da mafita Tunda cikar Burinsa ya ke so sai yace A tsaida mganar auransu nan da shekara Biyu in ta shiga SS3 sai ayi bikin nasu.
Da wannan mganar Umma ta amince da komawarsa zariya a karo na biyu.
Innani kuma jin an saka Lokacin bikinsa da Sultana sai bata damu ba ita bata ma tsaya jin shekarun ba ta fara Murna ta na lissafin wad'anda zata gayyata.
Sauran yan'uwansa mata ba su da Sanin abunda ke Faruwa sai da kanin nasu ya sake tattaraawa ya koma zariya sannan suka sani.
Surayya ta ciji yatsa acikin jikinta kawai taji kamar Sadiq yana Boye wani abu kuma koma menene yana da nasaba da garin da ya nace ma zama.
Ita kad'ai ta acikin ranta ta shirya sai tayi bincike akan Sadiq kada yazo wata ya samu achan ta na so ta sauyasa daga yadda ya ke tun farko.

*Janafty*
*TMWBK2015*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488.*

Haba Babyn Habiby ya zaki zauna kina ta fama cutar infection, ke ce rashin sha’awa, ke ce jin zafi yayin tarayya, ke xche d’aukewar ni’ima, ke ce kai’kayi ki fitar farin ruwa da sauransu, an yi maganin asibiti da na gargajiya amma duka dai, tau share hawayenki ‘karshen matsalarki ta zo, da Honeydrops infection flusher ko cleanser pro sai kin yi dariya da godiya don zai wanke miki duk wata cutar sanyi. Akwai original sabaya ta gyaran breast su cicciko kamar baki shayar ba, akwai ta hips da mazaunai ki yi ma sha Allah ki samu kaya kema su miki d’as ki bar yawo da doguwar riga.

Na ce ba a nan muka tsaya ba muna da hadaddun kaya irinsu sweeteners, tighteners and wetners na tashin kan oga, wanda zai miki tukwicin dole, ke ko kurma ne sai ya yi magana ranar, don sumbatu ki dai samu abun rufe mai baki gudun ma’kota. Muna nan a garin Sokoto muna aike kowani gari kowacce kasa cikin aminci da rahusa. Kuna iya danna link din nan domin yi mana magana Kai tsaye https://Wa.me/2348167888934 ko kuma a kira 08167888934. Sai mun ji daga gareku isassun mata.

Tahir ya sha matukar mamaki lokacin da Anty Surayya ta kira shi ta na tambayanshi game da Sadiq.
sai dai mamakin na shi yafi karkatane inda ta tabbatarmai da cewa yanzu haka Sadiq na zariya.
Abun sai ya ba shi mamaki a iya Zaman da suka yi tare da Sadiq yasan ya na da Burin cigaba da karatunsa ammh bai taba ce masa ABU zariya zai dawo ba.
yadai san sun taba maganar BUK kano ya ke da Ra'ayin zuwa ya yi masters dinsa.
Tahir ya kara shan jinin jikinsa da yaji dalilin kiran da Anty surayya ta yi masa shine ta na tambayansa a zamansu a zariya bai fahimci wani Sauyi Daga Sadiq ba? Ta na tambayan yana da wasu abokai ne bayan shi? Ko kuma bai Lura ya fara soyayya da wata ba? Ko kuma dai wani abu da ya Fara Dauke masa Hankali?
Tahir ya yi shuru ya kasa magana a zahirin gaskiya yasan Sadiq ba shi da wani aboki Amini kamarsa, sannan Labarin Hasiya ne boyayye ga Ahalinsa kuma yanzu ba bu ita acikin Rayuwarsa.
Shiyasa kawai ya fad'a mata iya abunda ya sani game da Sadiq sannan ya tabbatar mata da cewa ko shi bai gayamasa ya koma karatu zariya ba.
Tahir ya Boye maganar Hasiya saboda akwai Amana Tsakaninsa da Sadiq bazai iya fallasa sirrinsaba, in dai ba shi ya nemi hakan ba.
Sun rabu akan zai bincika mata achan Zariya in da Sadiq ya ke zaune yanzu da kuma Halin da ya ke ciki domin tace ita fa bata yarda ba akwai abunda ya ke d'aukan Hankalin Sadiq a zariyan nan, sannan ta fad'a ta kara Fad'a Hallayar sadiq ta fara sauyawa.
Tahir suna gama waya da Anty Surayya ya kira Sadiq bai Dauka ba sai da ya kara kira ne sannan ya Dauka yana fad'a masa yana aji ne in ya fito zai kirasa.
Sai Tahir ya kara Tabbatarea duk da yasan Daman Anty Surayya bazata gayamasa karya ba
Haka ya yi ta dakon kiran Sadiq ammh har Dare bai kirasa ba, sannan shi din daya damu su yi mgana ya kirasa sai sharrin Network yasa bai same shi ba, Tahir yaji kamar ya zama Tsutsu ya gansa a Zariya.
Har wani Shamsu ya kira cikin yan makaranta da suka zauna tare da su yana Tambayansa ko Sadiq ya Dawo nan dakin ne again? Nan take shamsu ya tabbatar masa da cewa tafiyarsu ba Dadewa wasu yan makarantar suka kama Dakin nasu sai anan ya kara Tabbatarma da kansa cewa Sadiq ya Sauya Muhalli wannan karon.
Shi ko Sadiq sam ya manta da Tahir suna gama Lectures ya tafi wajen aikinsa sai Gabda mangariba ya koma gida.
Ya iske Hasiya ta gama girki ta share daki ya na tashin kamshi sannan itama ta ci gayunta kamar yadda ta fara sabama kanta acikin yan kwanakin da suke tare.
Babban abun da ke sakashi cikin Farinciki ya fita da Safe ya dawo ya iske Hasiya na jiransa cikin Farinciki nan take sai yaji komai na Duniya ya gama samu in dai ga shi ga Hasiya ne.
Baisan wani iri abu ne mai karfi haka yake ji a kanta ba abu d'aya ya sani Allah ya had'a zuciyarsa da ta Hasiya waje d'aya.
Tun dawowarsa ya zaunar da ita ya fad'amata cewa yanzu tare zasu zauna Ya samu gurbin cigaba da karatu sannan kamfanin da ya yi musu hidimar kasa sun Daukesa a aiki a matsayin ma'aikacin su cikakke, Hasiya ta yi murna da Farincikin jin wannan Labarin barin ma da ya ce tare zasu zauna tare yanzu.
Sai ya kasance sun fara shimfid'a wata Sabuwar Rayuwar da dukkansu ba su Shiryamata ba.
In ya na da Shiga cikin makaranta da Safe ya kan fara shiga kafin ya wuce wajen aiki daman kuma sun riga sun san ya na masters dinsa kuma sun amince da hakan.
In bazai shiga makarantar ba sai ya wuce wajen aikinsa in kuma ya Dawo gida suna manne da juna shi da Hasiya.
Girki ma tare suke yi ya na taimakamata da Dauko wannan suna yi suna Hira, Dibar ruwa shi ya ke mata wanki ma damam ya saba tare suke yi, abinci ma yanzu a kwano daya suke ci, in kuma baya Bukata sai su fita waje su ci abinci, da Daddare kafin su kwanta za su yi kallo ko kuma ya kunna musu game a babbar wayarsa su yi, ko kuma ya yi ta mata Hira kala kala na Duniya duk domin ya sakata Farinciki.
Yana waya da duka yan'uwanta da shi har da Amma, hankalinsu ya kwanta a zaton su da kyakyawan yakininsu Hasiya ta samu sukuni da zaman lafiya a gidan auranta.
Amma ta fi kowa jin dadin haka In Sadiq yace za su zo su gaisheta sai tace ba yanzu ba, tafi bukatar su natsu su samu kwanciyar Hankali da zaman lafiya.
Har gidan Adda Rukayya sun je tare ba dai su jima ba ne a gidan duk da ya Fahimci kamar ba su cika shakuwa kamar Adda Fati ba, bai matsa sai yaji wani abun ba, gidan ramatu kuwa sun je bai san iyaka ba har gidan Inna Talatu ta kaisa ya gaisheta ya yi mata alheri.
Kwata kwata Sadiq ya sauya Rayuwarsa gabadaya kamar ba shi ba, abu daya me bai sauya ba kwanan da suke yi Dabam Dabam, har gobe ita ta na cikin Daki shi kuma ya na Falo ne.
Wannan matakin kam Sadiq ya kasa Jarumtar ketare sa tukunnah.

*****
Chapter 51 · 0% Book details