← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 75

Sashe 20

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Danwake na yi da yaji mai manja, Ummi ba ta nan ta na makaranta karfe biyu ake tashi na rana kafin ta kariso gida uku ta yi wani lokacin kuma gida ta kan biya sai bayan la'asar ta ke dawowa. Yaji na cika ma danwaken nawa da yasa bayan na ci na kasa ta shi sai faman shi! Shi! Na ke yi saboda harshena da bakina ya nad'e da yaji har cikin kaina. Ta ko'ina zufa ke ketomin gabadaya rigar material d'in da ke jikina ya jike da zufa idanuwana sun yi jajir harta Fuskata ta nuna alamun na sha wuya. Zaune na ke kasan tayels din falona filet din da naci danwaken na gabana na kasa Daukewa harta ledan da na sha ruwa nan na watsar da shi ga Roban yaji da yar roban da na zubo manjan bayan na soya. Saboda kwazzaba danwake bai wuce guda ashirin na jefa ba, sha'awansa naji ina yi shiyasa na yi kad'an saboda ba na so ya kai min dare. Kamar daga sama naji ana kwankwasamin kofa agogon wayata na Duba dake gefe na, naga biyu da wani abu na rana sai a raina nace kila Umma ce ta dawo tunda in dai ta dawo sai ta fara bugamin kofa na leko mun gaisa kafin ta bude dakinta ta shiga. Shiyasa batare da tunanin komai ba na mike ina faman shan yaji Saboda Rud'ewa ko dankwali ban saka ba Kitson Shukun da ke kaina tun wanda Adda Fati ta min ne ranar da suka zo da na saka Habiba ta tsifemin na biki. Shi ma wannan din ya tsufa ballatana Sumana na da Santsi kitso ba ya Dadewa sai ya fara warware kanshi. Kai tsaye batare da tunanin komai ba na bude kofar lokaci daya ina fad'in"Ummi yau kin..." Sauran kalamai na sun makale ne samakon ganin abunda ban taba zata ba. Yana tsaye a kofar dakin sanye da riga da wando baki da fari da jaket a saman kayansa sai kafarsa sanye da Rufaffen takalmi na bakin fata mai kyau Sannan bayansa goye da jaka kamar ta yan makaranta. Hannayensa sanye acikin Aljihunsa kyam ya na kallona, sai naji na tsargu na kasa magana sai na fara sosa kai da Hannu guda d'aya mai kyau. Wanda ya yi dama dama da manjan sai na maida shi baya. Kunyar duniya duk tabi ta lullubeni cikin sanyin jiki da na murya nace"Sannu da zuwa." Daga sama har kasa ya karemin kallo kafin ya dan saki fuska kad'an Cikin maganarsa yace"Yauwa in shigo? Sai na gyad'a masa kai ammh bansan cewa na tsaya kyam na bake kofar shigowa ba. Sai da ya kara kallona sannan yace"To ba ni hanya ko Hasiya? Sai da ya fad'i haka sannan na yi gefe da Sauri ina kif kifta ido kamar mara gaskiya Sai da ya shigo sannan na kulle kofar na bi bayansa Lokaci d'aya ya na fad'in"ke haka ki ke bude kofa batare da kinsan wa ke miki knooking ba? Ya fad'a daidai muna karisowa Tsakiyar falon. Na kasa mgana ganin ya na bin inda na tashi da kallo cikin mamaki ya juyo ya na kallona bai yi mgana ba sai ma ya samu d'aya daga cikin kujerun falon ya zauna lokaci d'aya ya na sauke Jakar hannunsa. Ajiyar zuciya ya sauke na alamun gajiya ni kuma ganinsa da jaka sai na yi tunanin kila daga tafiyar da suka yi yake. A gaggauce na duka ina kwashe kayan gabansa cikin jin kunya da nauyi. Da akwai sauran danwake a Filet din yaji ya yi min yawa yasa ban karisa cinyewa ba. Filet din yabi da kallo sanda na ke mikewa cikin yanayin mganarsa yace"Danwake ki ka yi? Kai na gyad'a masa ban yi mgana ba kai tsaye yace"Zan ci. Ammh bari na dan watsa ruwa tukunna." Ina so nace masa babu ya kare ammh na kasa mgana. Ya mike ya na fad'in"Akwai ruwa a cikin Tiolet din? Da rawan baki nace"Eh ammh ba ruwan zafi bari na saka maka." Bai jiyo ba ya na nufar hanyar Bedroom din yace"Zafi na ke ji ruwan sanyi is ok a wajena." Daga haka ya wuce ciki sai a lokacin na samu damar Sauke numfashi. Kitchen na Rumtuma kwanukan wanke wanke tun jiya ban wanke su ba su na fara wankewa sannan na Sake dora masa ruwan danwaken. Sai alokacin na taba kaina naji ashe ban da dankwali a kaina da gudu na sake dawowa falon na Dauki Dankwali na Daura, sai alokacin naga ashe manja duk ya zuba a saman tayels din ga shi da haske ya bayyana. Da gudu na koma kitchen na jika Tsumma da ruwa na dan barbard'a omo na goge wajen. Sannan na dawo na kwaba garin Danwaken na jefa masa cikin mintina sai ga shi na gama komai har na kara gyara kitchen d'in. Nasan ya na san manja ammh ban yi gaban kaina ba nace bari naji Ra'ayinsa. Ammh har alokacin yaji bai bar auna min Rad'adi a saman harshena ba. Sai ga shi mura ta kamani ina ta faman jan majina saboda azaban yaji. Ina fitowa na gansa a falo zaune da waata na'ura akan cinyarsa ya na Dubawa. Daga nesa da shi na Tsaya ina fad'in"Manja zan saka maka ko Mangyad'a? Kansa ya dago ya na kallona kafin yace"Kinsan Ra'ayina ko? Sakamin manja" Sai na juya na koma a karamar kula na saka masa Danwaken sai na dauko masa Filet da cokali da ruwa. Manjan ma dabam na sako masa sai Roban yajin duk na jera a gabansa. Ina durkushen nace"yaji kada ka cika ya na da fad'a" Batare da ya kalleni ba yace"I see. Ko daga yadda kika jigata nasan ya na da fad'a." Sai da ya fad'an na kara bin kaina da kallo sai na kara yarda ma kaina a jigace nake. Sad'af Sad'af kamar barauniya na mike na shige bedroom da sauri. Ba Kasafai na ke kara yin wanka bayan na yi da Safe ba ammh yau ta kamani dole sai na kara. Nima kamar shi da ruwan sanyi na yi wanka naji dadi har raina da naga da Soson wanka na ya yi amfani. Da na fito daga wankan ban ko shafa mai ba na bude wardrope na Dauko Atamfa riga da zani na saka na Daura Dankwali. Sai na kasa fita falo Saboda kunya na yi zamana aciki. Zanina da na ke wanka da shi na gani an shayamin saman kofar Tiolet na tashi na taba sai naji da Danshin Ruwa. Sai nasan da shi ya yi amfani kila ya goge jikinsa tunda nikam ban tsaya Daura wani zani ba na fad'a wanka. Gajiya na yi da zaman cikin na fito salau salau kamar kazar da kwai ya fashe mata acikin cikinta. Hankalinsa na kan Na'urar gabansa da ya ke ta dannata sai nima yaja Hankalina. Kasa na zauna a kujeran da ke fuskartsa ina kallonsa hannunsa baya gajiya Tab! Tab! Kana jin karan abunda ya ke dannawa. Sai naji ya Burgeni abu kamar aljani bansan ya juyo ya na kallona ba, saboda shagala da kallonsa ina mirmishi sai ji na yi kamar daga sama yace"Kwashe kaya nan na gama tun daz'u." Sai na yi kamar na Firgita kafin na shiga Raba ido ina Fad'in"Eh." Bai kara kallona ba yana cigaba da abunda ya ke yi yace"Eh nace ki kwashe su ki kai kitchen.". Da sauri na mike na fara Tattarawa na mike na zuwa kitchen sai da nashiga sannan na duba naga yaci Danwaken da yawa kadan ya rage. Sai na ijiye masa sauran ina Tunanin kila anjuma zai bukace shi. Abunda ya bata na ke wankewa naji bude get da Shigowar mutum. Sai chan naji muryan Ummi kamar ta na mgana a waya ne. Ban jira ta bugamin kofa ba ina gama wanke abunda ya bata na kifesu a kwando na fito zuwa kofar dakina. Sai alokacin ya bi ni da kallo tun ba ma Siraran kafafuna ba. Ya na mamakin yadda na ke da karfi da Kuzari ashe abun ba daganan take ba. Ina bude kofar na ci karo da Ummi ta na saka wayarta a jaka. Cikin washe baki muka tarbi juna na yi mata sannu da hanya muka gaisa sannan ta karisa dakinta ta bude ta shiga ni kuma na maida kofata na kulle na dawo cikin Falon. Diri diri na yi tunda ni dai ban saba da shi ba, sai na yi tunanin na koma ciki na kwanta zuwa la'asar kafin ya tafi. Na kama hanya kenan naji ya na fad'in"Kin yi kawa ne? Sai na juyo ina kallonsa kafin nace'"Amaryan da ta tare ni kwanakin baya Sunanta Ummi." Jinjina min kai kawai ya yi batare da ya kara mgana ba ni kuma sai na yi wuf na fad'a ciki. Ban cika barcin rana ba saboda ban saba ba. Gwara ma kwanaki kafin na samu waya na kan kwanta na rasa na yi na yi ta tunanin rayuwa har barci ya kwasheni bansani ba. To yau ma hakane ya faru kwanciyata ba Dadewa barci mai nauyi ya kwasheni. Barcin da har akayi la'asar bansani ba shi kuma ba ma'abocin yin salla agida ba ne fita ya yi ya nemi masallaci ya yi sallansa ya dawo ya cigaba da aikin da ya ke wani aiki ne aka ba su daga wajen aikin su. Baisan barci na ke yi ba ya dauka na yi salla ban fito ba ne saboda zamansa a falon shi kuma sai ya samu kansa da Sakewa sanin ina cikin Dakin. In da yana chan dakin ne bazai iya wannan aikin ba kadaici da kewa duk zata addabeshi ya kasa yin komai. Sai da yaji ana ta bugamin kofa ne kuma yaga ban fito ba sannan ya tashi ya leka cikin Bedroom din yaga ina ta barci hankalina kwance. Bai tasheni a lokacin ba jin ana ta buga kofar yasa ya juya ya fita yaje da kansa ya Bude. Ummi ce ta kawo min abinci ta na ganinsa duk da bata taba ganin mijina ba amnh tasan ba wanda zai shigar min daki a wannan Lokacin in ba Mijina ba. Da sauri ta gaisheshi ya amsa da Lafiya lau bai kuma saki fuska ba. Cikin sauri Ummi tace"Hasiya fa? Kai tsaye yace"Ta na barci." Ummi sai ta
Chapter 20 · 0% Book details