Sashe 70
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabbas hakane domin ko wanda baisan kama ta jini ba yaga Assadiq da wad'anan matan yasan suna da alaqaan jini mai karfi a tsskanin su.
Na yi ta kallon Hoton nan ina sake Zooming ina kokarin gasgasta zargina zuciyata na Tunanin Assadiq bazai min karya ba? Wata zuciyar na gayamin ya yi min karya tunda har yau bai taba kaini ga wani nasa ba hatta ko kakar tasa da yace ita kad'ai ta rage masa.
Lokacin da nake zaune ina wannan Tunanin, ashe ban sani ba na yi sharkaf da jini, sai da naji abu na bin kafata sannan na farga ko da na mike sai da naji tsoron ganin jini ya bata siket din jikina yar ya bata kujeran da na ke zaune sannan ya bata har kasan Tayels wanda ya gangaro ta kafafuna.
Wannan tashin hankalin ya mantar dani Hoton da na gani na shiga cikin tashin hankali na shiga Tiolet na gyara jikina sannan na kwabe kayan Jikina na wanke su tas sannan na fita waje na shanya.
Muka had'u da Maman suhailat itama ta na shanya ta yi wanki sai muka gaisa sama sama domin ba na cikin yanayin nishad'i, na koma daki da Sauri na goge kujera in da na bata da kuma Tayels din na wurgar da Tsumman da na goge da shi.
Abun kamar wasa sai ga karaman mgana ta zama babba kwana nayi ina Zubar da jini, pad ya daina amsata na koma yaga zanina ina kunzugu da shi ammh duk a banza kafin safe sai da na cika baho da kayan da na bata har da zannuwan gado har katifan ma sai da ta baci.
Hankalina ya tashi saboda Ina Tunanin jinana ya kusa karewa, ni ba Ciki gareni ballatana nace ko bari zan yi tuni har karfina ya kare ma fara ganin jiri jiri dakyar na iya wanke kayan da na bata na fita na shanya, daga baya da naga zanin ya daina Tarenin jinin duk inda na zauna sai na bata ina tafe ina yoyo da sauri na Daga waya na Kira Adda Fati a Lokacin ban yi Tunanin kiran Assadiq ba Sanin da na yi baya kusa kafin ya kawomin agaji na mutu.
Cikin tashin hankali nace mata tazo gida yanzu, jin yanayina yasa tasan ba lafiya, ko da ta zo ta iskeni zaune ina kuka ga jini na ta bin kafafuna.
Cikin tashin hankali ta rikeni ta na Fadin"Innalillahi Hasiya? Me ya sake ki? Ko bari kikayi?
Cikin kuka nace"Bansani ba, daga al'ada ne jini ya tsinke min adda Tainakemi ki kaini asibiti kafin na mutu jini na ya kare."
Adda Fati ta rakani Bayi na gyara jikina ta ninka wani Dankwali na yi Kunzugu da shi sannan na sauya kayan Jikina, ita ta Rufe dakin muka ta fi asibiti abun da ya kara ba ma Adda Fati tsoro tun muna adaidaita jini ya fara bin kafata kuma duk ya bata kayan jikina da Hijabina
Asibitin musulmi ta kaini mun jima kafin mu ga likita don ma wai jama'a sun Tausaya ganin ina ta zubar da jini ga shi nan inda na zauna har ya na gangara.
Ni dai nasan Adda Fati ta rikeni zuwa ofishin Likita, daganan bazan iya tuna komai ba, sai da na farka da misalin hudu na yammaci na gani kan gadon asibiti a wani daki ni kad'ai sai Adda Fati a Tsaye a kaina sai kuma Ramatu na zaune gefena ta na rike da Hannuna.
Cikin Nauyin jiki da na ido na farka ina bin su da kallo suma kallona su ke yi ganin na Bude ido yasa Ramatu tace da Sauri"Adda Ina ga ta farka."
Jin haka yasa ta kariso gabana ta na fadin"Hasiya."
Amsawa na yi cikin dakushewar murya ina kokarin tashi ta kamani na tashi lokaci d'aya ta na fadin"Ki bi a sannu kada ki fama Hannun ki."
Sai na bi hannun da kallo cikin mamakin ganin bandage a hannuna, sannan kuma na duba kafata ban ga jini na bi na ba, ammh daga kasa naji kamar an sayamin Audugan mata.
Cikin neman karin bayani na kallesu kafin na yi mgana Adda Fati ta Bude kofa ta Fice ta na fadin"Bari na Fad'a ma Likita ta farka."
Ramatu na rika tambayan me ya sameni? Ko jinina ne ya kare? Sannan miye ya sameni a hannu.?
Ramatu bata amsamin Tambayata ko Daya ba sai ma wani kallo da naga ta na yi min kafin kawai tace"Uhm Hasiya kenan."
Daga haka ta tsuke bakinta sai abun ya bani mamaki, Adda Fati ta dawo tare da likita ya duba ni sannan ya yi min Tambayoyin ya na ke ji nace ba komai ina jin jiri nace a'a? Ina jin zubar jinin yanzu? Nace ba na ji.
Sai ya kalli Adda Kafin yace"Kada ku damu zubar jinin ya tsaya, daman kuma shi Inplant da zarar an ciresa ya na tafiya tare da matsalansa ne, Saboda ta samu karfin jikinta sai ku kwana anan da Safe sai ku tafi gida."
Bayan fitan liktan ina so na yi tambaya ammh Daga Adda Fati har Ramatu ba su bani Fuska ba.
Haka suka yi Fuska kamar ba su sanni ba, kudi kawai Adda Fati tace ko akwai a Hannuna nace suna banki.
Sai na gayamata in da na ke ijiye Atm dina Ramatu tace zataje gida ta dauko sannan tazo min da wasu kayan.
Sai lokacin na lura da na jikina ba nawa ba me na Ramatu ne wad'anchan kenan sun lalace komawa na yi na kwanta ina Tunanin abunda ya sameni da bansani ba.
Adda sam taki sakarmin Fuska, Ramatu ta je gidana sai ta wanke kayan da na bata sannan ta Dauko min zani da riga, sai pant guda Biyu sai ta dabo Ruwan zafi a fulas ita ta gayama Maman Suhailat ina asibiti ba ni da lafiya ammh gobe zan dawo gida.
A hanya ta tsaya ta cire kudi ta siyo kayan marmari da Buredi, sanda ta dawo ina barci sai daga baya na Farka Adda Fati ta rakani bayi na yi fitsari sai naga jinin ya tsaya sai dai dis dis ya ke diga a saman Audugan.
Tea Ramatu ta hadamin na sha Daman yunwa nake ji, sai kuma Kayan marmarin da na sha, yadda suka min gim nima sai ban kara mgana ba ina so nace ina wayata ammh na kasa tambayar su.
Adda Fati ce ta kwana dani Ramatu ta koma gida Tundaga Noor.
Da Safe ma sai dai ta same mu a gida Tunda da wuri aka sallame mu.
Sai ga shi da kafata na shiga Daki na tare da Adda Fati, Maman Suhailt da Ummi sun shigo sun gaisheni.
Adda Fati ta had'amin Ruwan wanka na shiga na yi sai dai tace na kula kada na Fama Hannuna.
Bayan na fito na sauya kayan jikina , na saka pant da pad duk jinin kad'an Ya ke zuba ita kuma har ta had'amin Tea ta soyamin kwai.
Kadan naci kwan Tunda bakina baya min dadi, sai ta bani mganguna guda biyu na sha wanda inaga aka Rubuta daga asibiti ne.
Adda Fati ta share dakin ta goge ni kuma ina zaune saman kujera ina Tunanin karo na Biyu kenan a sakamin Bangade a hannuna kuma duka ba acikin yanayin Hankalina ba to me ke faruwa ne?
Wajejen sha Biyu sai ga Ramatu, ta zo suka had'u da Adda fati suka zauna waje daya suna ta magana kasa kasa bana jin me suke fad'a.
Wayata ce a hannuna ina duba kiran da na rasa Assadiq sau biyu ya kira jiya da Daddare, sai bai kara kirana ba Kila ya na Tunanin na yi barci ne.
Gabadaya sai na Tsargu, na fahimci kamar da ni suke.
Sai na tashi Zaune dakyau ina kallonsu cikin mamaki kafin nace"Adda, ramatu wai don Allah me ya ke faruwa ne ? Tun a asibiti na ke tambayar ku shuru baku ce min komai ba ?
Adda Fati ta Kalleni kafin ta harareni tace"Gani mu ka yi tambayar taki ba ta da amsa, Tunda kinsan abunda kika aikata."
Cikin mamaki nace"Bangane ba? me na aikata?
Ramatu ta ce ka tsaye"Ki na so ki gayamana baki san abunda kika saka a jikin ba ne da ya sakar miki jini ba?
Cikin wani karin mamaki nace"Wani abu kenan? Don Allah ku fad'amin bansani ba."
Adda Fati cikin bacin rai tace"Hasiya da wayau ki da komai me ya kai ki? Baki taba Haihuwa ba me ya ja miki saka Tsarin iyali? Abun takaicin ma in za ki saka Tunda baki son Haihuwar yanzu sai ki saka na shekara d'aya ko Biyu ammh Saboda Rashin Lissafi har na Shekara biyar kikaje aka saka miki to Allah ne ya cece ki, sai da aka yi miki karamin Tiyata a hannun nan naki aka Cire abunda kika kai kan ki aka saka miki"
Har alokacin Cikin Duhu nake cikin Sigar tambaya nace"naje aka sakamin mene? Kuma a yaushe?
Adda Fati tace"Bana son Renin wayau Hasiya, inplant din da kika saka na Tsarin iyali na shekaru Biyar."
Na bud'e baki ya fi sau biyar ina Rufewa Lokaci d'aya ina kallon Adda Fati cikin mamakin kalamanta.
Cikin fitar hayyaci da Sigar tambaya na maimaita"Inplanta kuma? Menene shi?
Ban gama Rufe baki ba Ramatu ta ballamin harara kafin tace"kin fi mu sanin koma menene shi tunda kika iya aminta kika kuma saka shi a jikin ki Hasiya, kin bani mamaki ban zaci haka daga gareki ba."
A zahirance ne na ke kallon Ramatu, ammh a badini ba ita na ke kallo ba na lula wani Tunani na dabam
Ina jin acikin fad'an Adda Fati sai na gano ma'anar abunda aka gani ajikina.
Inplanta wani abu ne na tsarin iyali, to yaushe na saka bansani ba?
Kwakwalwata ta shiga Tunanin a watarana, sannan da wani Lokacin har haka ta faru bansani ba?