Sashe 8
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Lokacin Da kiran Adda Fati ya shigo wayae Tahir ya na kishingid'e ya na chart ne Sadiq na kwance gefensa barci ya kwashe shi yau yini ya yi a wajen aiki ya dawo a gajiye da yasa barci ya kwashe da wuri suna Hira ne ma shi da Tahir.
Har ga Allah sun ma sha'afa da mganar Tariyan Hasiya Basu san kan al'amarin ba sun zata ma basai ma an kira su ba Shiyasa ba su yi tunanin wani abu ba.
Tahir ba shi da lambar Adda domin ba shi da alaqa da ita ballatana ya adanata shiyasa har ya daga wayarsa suka gaisa bai gane wacce ke mgana ba.
Cikin Muryansa yace"Bangane wa ke magana ba?
Adda Fati tace"Fati ce yayar Hasiya."
Har ga Allah kwana biyu nan Tahir ya fara dawowa cikin Hayyacinsa da Halin Tsaka mai wuyar da Sadiq ya saka su ya fara mantawa da wata Hasiya tunda Sadiq baya masa mganarta shima ba ya yi masa.
Kai tsaye yace"Na'am bangane ba wata Hasiya?
Ya fad'a kai tsaye sai Adda ta kasa mgana su kuma su Ramatu sun Tsorata sun zata wani abu ne ya faru suka fara tambayanta ko lafiya Hankali ta she.
Ba su kadai ba ni kaina ina makale a jikin kofar dakin gabana na fad'uwa.
Bana son wani abu ya samu Assadiq in hakan ta faru ta sanadina bazan tab'a yafe ma kaina ba.
Adda Fati ta hadiye miyau kafin tace"Sadiq na lafiya kuwa? Na yi kiran wayarsa a kashe ko ya manta yau ne nace masa Hasiya zata tare."
Sai da ta fad'i haka ya tuna da gagurumin tarnakin Bala'in da Sadiq ya jefa rayuwarsu a ciki.
Cikin mamaki yace"Ta na chan gidan ne yanzu?
Adda Fati tace"A'a ina dai tambayan Sadiq ya na lafiya?
Tahir yace"lafiyansa kalau ya kwanta ne bari na yi masa mgana."
Daga haka ya yanke kiran Lokaci daya ya na shurun Sadiq da kafa.
Fad'i ya ke yi"Mallam ai sai ka tashi Shigen Tausayi ya sa ka jefamu a masifa ba ka ga ta barci ba Sadiq."
Sadiq ya motsa lokaci daya ya Bude idanuwansa ya na kallon Tahir kafin yace"A gajiye na ke Tahir ka bar ni na Huta don Allah.".
Tahir ya kwashe da dariya kafin yace"Ina kaga ta wani Hutu? Amaryan ka Hasiya na chan na jiran ka."
Kamar bai jisa ba sai kuma ya mike Zumbur ya na fad'in"Me ka ce?
Tahir yace"Yanzu wannan yayar nata ta min waya suna tambayan ka ko lafiya ka ke kuma da sakon Amarya na chan na jiranka"
Sadiq ya dafe kansa kafin yace"Na manta daman yau jumma'a ne?.
Tahir baka tuna min ba."
Tahir ya balla masa Harara kafin yace"Ni kuma a suwa da zan tuna maka? Kai da abun ya shafa ka manta sai ni karan kad'a miya."
Mikewa zaune Sadiq ya yi cikin kasala ya na fad'in"Duk dai ba wannan ba yanzu ta na ina?
Tahir yace"Oho ina na sani sai dai ka kirata kaji."
Sai alokacin ya duba karamar wayarsa yaga ta mutu daman ya kwana Biyu bai sakata a chaji ba.
Wayar Tahir ya amsa ya kira Adda Fati daidai Lokacin da zukata suka samu natsuwa jin Babu abunda ya faru da Sadiq.
Ta zata ma Tahir ne sai taji muryan Sadiq tambayanta ya yi sun kai Hasiyan chan gidan ne? Adda Fati tace a'a ai ba su yi da shi zasu kaita ba.
Kansa ya dafe kafin yace"Ku yi hakuri na Shafa'a ne sannan wayata ta mutu ba chaji. ina ne in da ku ke sai mu zo mu dauketa?
Nan Adda ta rarrataba masa kwatance tace in ba su gane ba su kirata.
Suna yin sallama ta kalli su Ramatu ta na fadin"Alhamdulillah ba abunda ya same shi yace mu yi hakuri ya sha'afa ne wayarsa ce ta mace ba chaji ammh yace gasu nan zuwa."
Gabadaya suka sauke ajiyar zuciya ni kaina da na ke labe sai da na sauke Numfaashi ina jin gudun zuciyata na Daidaita.
Sad'af Sad'af na koma daki na zauna ina maida numfashi.
Sadiq ya sha fama da Tahir domin da Farko yace shi ba mai sake fitar da shi da Daddaran nan ya gaji.
Sai da Sadiq ya yi ta rokonsa sannan ya tashi ya Shirya suka Rufe daki suka tafi.
Ba yan gari ba ne kuma basa yawo shiyasa suka sha wahala kafin su gane gidan Adda Fati sai da Mijinta ya fita bakin hanya ya tarosu.
Saboda Sauri kananun kaya ne dukkansu a jikinsu gwarama Sadiq ya Dora Jaket a saman riga da wandon jikinsa.
Har Falon Adda Fati Habibu ya yi nusu Jagora in da su Adda ke zaune suna jiransu.
Dukawa suka yi suna gaishesu Sadiq yafi nuna jin kunya Tahir ko aransa cewa ya yi kunyar me tunda ba surukansa ba ne.
Adda ta jima ta na nazarinsu kafin ta yi mirmishi tace"Duk da bansan surukin namu ba ina da tabbacin mai kunyar nan ne"
Adda Fati na mirmishi tace'Shine Addan mu"
Sadiq ta kallah kafin tace"Abubakar ga Addammu yaya ta ke a wajen Amma."
Sai a lokacin ya dago ya kara kallonta sai kuma ya ga tsantsan kamarsu da Amma cikin sanyin murya yace"Sannu da zuwa. Amma na lafiya?
Adda tace"Ta na lafiya bata zo ba ammh tace sakon fatan alherinta na tare da ku a koda yaushe in sha Allahu."
Da kai ya amsa mata Tahir kan kiris ya rage bai tashi ya zauna ba tunda yaji kafafunsa sun gaji da Tsayawa.
Adda ce ta fara yi ma Sadiq tambayoyin sana'ar da ya ke yi.
Su ka kalli juna shi da Tahir kafin yace"Ina bautar kasa ne da d'an alawun da suke bamu na ke buga bugata namu dai irin na talakawa."
Adda ta jinjina kai kafin tace"Allah ya tallafa Naji suna fad'in kai d'an shinkafi ne nan ta zamfara ko?
Sadiq ya gyada mata kai alamun hakane ya Dauka nan Adda zata tsaya ammh sai ta cigaba da fadin"To bayan iyayenka sun rasu a hannun wa ka ke a chan shinkafin?
Sadiq ya kalli Tahir karo na biyu shima ya kallesa.
Adda na ganin haka tace"Ina fatan ba damuwa ko? Kasan aure na bukatar haka an yi abun cikin gaggawa akwai bukatar ka gabatar ma da Ahalinka Hasiya."
Sadiq ya had'iye wani miyau kafin yace"Eh eh zan kaita in sha Allahu."
Adda tace"Baka amsa min tambayata ba? Wajen wa ye ka girma bayan ka rasa iyayen ka?
Kamar Subutan baki Sadiq yace"Hannun kakata. Eh hannun kakata na girma."
Adda ta murmusa kafin tace"Dakyau. allah ya baku zaman lafiya bayan an kwana biyu sai ka kaita taga Dangin ka. Allah ya baku zuru'a masu albarka nasihata itace ka rike Hasiya da Amana don girman Allah kada ka bari rayuwar Hasiya ta shafi zaman Lafiyan ku. Canfi ba gaskiya ba ne komai kaga ya faru daga Allah ne."
Sadiq ya dago ya na fad'in"Wannan bazai taba zama matsala ba in sha Allahu. Kowa yasan ba bu mai yi sai Allah.".
Adda taji dadin jin haka sai ta yi hamdala itama ta aminta da zabin jari yaron akwai hankali.
Ramatu ta kallah kafin tace"Ki je ki taho da Hasiya. Dare na yi"
Da Sauri ta mike zuwa Dakin Habiba na ciki da tashigo daga baya.
Ban jira tamin magana ba na mike Ramatu ta saka Habiba ta Dauki karamin akwatina ita kuma ta rike Babban.
Ina gaba suna bi na a baya muka fito falon ban kalli kowa ba gaban Adda na Durkusa.
Ta Dafa kaina ta na sakamin albarka kafin ta mike ta na fad'in su tashi su rakani.
Allah yasa ba su sallami mai adaidaitan da ya kawo su ba, har kofar gida suka rakani Adda da Inna Talattu suka sanya cikin adaidaita Sadiq na gefe Tahir kuma ya shiga gidan gaba.