← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 75

Sashe 63

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da ya kwashe kimanin Sati Shidda a garin Abuja sannan daga Abujan Ranar al'hamis  ya fara sauka a Gusau, tunda ya fi masa sauki yaje Zariya daga gusau sannan Daga Zariya ya koma Abuja.
Yaje Gusau lokacin Saura Sati Biyu Bikin Salima da Mubarak ya iske gida cike da yan'uwansa mata na kusa Tunda Bikin ya karato nan suke yini.
Daman tunda ya dauki albashinsa na Farko ya yi wani Tunani a ransa.
A wani kanti ya tsaya ya siya ma Abba Agogo mai Tsada da Hula Zanna Bukar sai Bakin Takalmi sahu ciki masu kyau da yarari sai Turaren maza mai kamshi.
Sannan anan yaga wasu lesuka masu kyau guda biyu sai ya siyama Umma D'aya Mama guda d'aya, Innani kuma sai ya siya mata Atamfa mai kyau mai Taushi.
Ya so ya siyama Siya wani abu ammh kuma sai da ya yi wani Tunani sai ya fasa, wani abu dake damunsa shine duk abunda zai gani na kwalliyar mata baya hasaso kowa aciki sai Siya, Sultana bata cika zuwa ransa ba.
In ya yi tunanin kada in ya auri Sultana ya kasa adalci a Tsakaninsu sai wata zuciyar ta fad'a masa cewa Saboda Ita Sultana ta na da gata ne Hasiya kuma ba ta da kowa sai shi.
Da wannan Tunanin na zuciyarsa ya kauda Tunanin bazai iya yi ma Sultana adalci ba.
Duk da ya taso cikin jin dadi sannan bai tab'a neman wani abu ya rasa ba, duk da mahaifinsa na da kudin da yafi karfin komai a gidansa shima a matsayinsa na Namiji tilo kwara daya da iyayensa suka haifa ya na da Buri da Niyar kyautata musu da d'an abunda ya ke samu.
Shiyasa tun ya na aiki da wannan kamfanin na zariya in dai zai je gusau baya zuwa Hannu Rabbana duk abunda ya gani a hanya sai ya siya ya kai gida, Abba ya sha fad'an cewa sunan Magajin gida da Innani ta saka masa ba iya suna ba ne, suna ne da ya ke binsa har jinin jikinsa.
Ko Yan'uwan su na Shinkafi bai manta da su ba in ya samu ya kan Turama Auwalu kudi ta bankinsa yace ya ba ma Baba Sammani ya raba shi da su Goggo Husai.
Ko wannan karon ma 50k ya Tura musu yace su raba a tsakaninsu, haka suka kira sa suna ta yi masa Godiya da Fatan Allah yasa ya gama lafiya sai dai su kira Abba su ce Sadiq ya yi musu kaza kaza da su ba su sani ba.
Shiyasa har abadan Abba baya Nadamar Fifitar kaunar Abubakar acikin ransa domin D'a ne mafi soyuwa acikin duka ya'yan da ya Haifa.
Sanda ya ba ma Abba abunda ya siya masa sai da idanuwansa suka ciko da kwallah cikin Tsananin Farinciki a muryansa yace"Allah ya yi maka albarka Abubakar, Allah ya albarkaci Samun ka Allah ya Tsare ka a duk inda ka ke Allah yasa a fi haka."
Sadiq ya amsa cikin mirmishi Abba ya kara kallon kayan sannan ya jinjina kai ya na yar dariya.
Shi alheri ya na da dadi, sannan kuma koda wanda yafi dangote kudi ne in ka yi masa alheri ya na so kuma zai ji dad'i.
Umma da Mama suma suka yi ta saka albarka Innani ko kuka ta fashe da shi , albarka ko ya sha shi ya fi cikin kwando, Su Surayya ma suka ce sai ya ba su na su shi kuma yace suna da mazajensu.
Sajida ce ta yi tsagal tace"Ko da mu ke da mazaje ai kai kanin mu ne zamu ji dad'i in kanin mu ya yi ma wani abun."
Harara ya sakar mata kafin yace"Da ya ke son kudi ne ai muryanki sai ta fi ta kowa zak'i."
Itama Hararan ta rama shi kuma sai ya saka mata Dariya ganin yadda ta kara zama wata cus da cikin jikinta ya girma.
Maganar Si yan ma Sultana Anko Surayya ta fara yi masa, tace har ta waya ma ta tura masa guda biyu ne material na ranar jumma'a yinin Biki kenan sai Atamfa na ranar Daurin aure.
Nan take yace yana so duka guda Biyu biyu, Cikin mamaki ta kallesa kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa" na sultana d'aya dayan kuma zan siyama wannan abokiyar aikin tawa ta zariya sosai zama na da ita ta yi min kirki."
Surayya ta yi mirmishi kafin tace"ASIYA..."
Cikin mirmishi yace"Ita fa Big sis, ai har yanzu muna zumunci ko da na koma Abuja yanzu."
Cikin gyad'a kai tace"Gaskiya ya kamata ka siya mata ta na da kirki sosai Da fatan zaka gayyaceta ta zo mana Biki"
Da Sauri yace"Anya? Da wuya ta samu zuwa zan dai siyamata ankon in sha Allahu."
Surayya bata damu ba, Tunda duk abunda Hasiya ke ba shi in yace mata zai je garinsu gida ya ke kawowa da sunan abokiyar aikinsa ce ke ba shi ya kawo ya riga ya nuna suna zumunci da ita sosai ita da Mijinta shiyasa kusan duk yayyensa sun san sunan Asiya a baki abunda yasa basu damu ba Sanin ta ba cewa ta na da aure.
Innani ko ta sha saka ma Hasiya albarka domin har Tuwon madara ta sha yi ta aiko mata da shi, daman kuma Innani akwai son Abun Duniya.
Shi ko Sadiq duk ya zurma su ne a Buhu ya Dinke Hasiya ya ke nufi ammh sai ya sauya ma Labarin Suna da Muhalli yadda kafin su Fahimci inda labarin ya dosa za'a Dauki Lokaci.

Bayan ya siya musu nan take ya Turama Surayya kudin Tunda ita ta Daukon ankon, Sannan kuma Sakeena na Saida mayafai da Jaka ta matsa sai ya siyama Sultana, bashi da yarda zai yi yace a kirata ta zaba ita kuma Hasiya a ransa yace in yaje zai bata kudin ta siya hannun Maman Suhailat.
Ba su barsa haka ba sai da ya Turama kowaccen su 2k da sunan za su saka kati har Salima, shi kuma yace tunda hakane harda Umma da Mama da Abba suma sai ya Tura musu Falon Umma ya cika da Ihu suna ta fad'in"Allah ya yi albarka karamin kanin mu."
Umma na ta saka albarka Mama haka har ta na fadin"In sauran suka zo suka ji Labari zaka yi biyan ba shi."
Kai Tsaye yace"Suma zan Tura musu Mama."
Abba ko fad'a ya fara masa da cewa yaushe ya fara aikin da zai zo ya na wannan Hidimar? Cikin yar dariya yace"Abba bakomai ku yi ta saka mana albarka shikenan kawai mu ke bukata."
Abba ya Dafa kansa ya na ta saka masa albarka.
Ya baro Gusau Ranar Lahadi da Safe ne yace zai biya ta zariya yaga Superversor dinsa.
Ya baro su Surayya za su je kaduna Jeren kayan Salima duk da yasan an gama siyamata komai ammh sai da ya kirata shashensa shi da ita ya tambayeta in akwai wani abunda ta ke so ta fad'a masa zai siya mata.
A lokacin sai ta kallesa kafin tace"Yaya Sadiq Abba duk ya gama siyamin komai fa."
Cikin yanayin mganarsa yace"Nasani wannan na Abba Dabam ni a matsayina na yayanki me kike so na Siya miki? Ke kanwatace kuma aure zaki yi na fara aiki ina so nima na yi miki wani abu Salima."
Idanuwanta suka kawo kwallah ko acikin maza an sai antona za'a samu irin Yaya Sadiq, ko acikin yayyen sai an tona Dari kafin a samu kamarsa.
Bata Bukatar komai, ammh Saboda yadda ya Damu yasa tace ya siya mata Frem d'in Ayatul kurusiyu.
Cikin yanayin maganarsa yace"Kin tabbata?
Sai ta gyad'a masa da haka ya sallameta to kafin ya tafi ya kira Surayya suka yi mgana ya Tura mata kudi yace ta siya ma Salima Frem mai kyau da Tsada.

Ko iyayen ba wanda ya sani sai da Surayya ta siyo ta zo da shi.
Kowa yasan waye Sadiq ammh kuma ya na kara girma Hallayarsa na Dattako suna kara bayyana.
Ko da ace su Abba sun gama mata komai shi a matsayinsa na yayanta shima akallah ya yi mata wani abu.

*******
Chapter 63 · 0% Book details