← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 75

Sashe 15

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar asabar da daddare ya je ya kaimata da tare da Tahir za su zo sai kuma yace ya fasa sai in zai koma da Rana ido na ganin ido sai su tafi dare.
Har Sadiq na zolayansa da cewa ya gane wayonsa girkin Amarya ya ke so yaje ya ci.
Tahir ya sheke da Dariya kafin yace"girkin wata Amaryan?  Su Amarya sun ji jiki. Wannan yarinyar bazata dafa abinci na ci ba."
Sadiq ya kallesa kai tsaye kafin yace"Tahir ba sunanta yarinya ba. Hasiya sunanta."
Ya fad'a ya na hade rai Tahir ya kara sakin Dariya kafin yace"Angon karya na Hasiya. Angon gaskiya na Sultana."
Ya na yi masa wannan shakiyancin ya fita ya barsa.
Sai da ya tsaya a hanya ya samu jam'in sallar isha'i sannan ya karisa koda yaje ya iske gidan cike da yammata ga shi akwai wuta.
Ya na ganin haka yace an kawo amaryan kusa da Dakin Hasiya kenan.
Lokacin da yazo dakina ya na bude tunda wasu daga cikin yanmatan Amarya sun shisshigo dakina wasu nan ma suka yi sallah iyayen ana kawo Amaryan ba jimawa suka tafi.
Hajiya zainab ce tace ma yan matan in suna Bukatar wani abu su yi min mgana.
In ka ganni sai kace nima ina cikin yan bikin ne sabon materil dina na saka Doguwar riga bakina a washe saboda ganin mutane, Allah ya gani na saba zama cikin jama'a shiyasa na ke murna da wannan sha'anin.
Bansan zai zo ba har wata na tambayana miji na ya na gari? Sai nace a'a ya yi tafiya ban jima da bata amsa ba suna kuma zaune afalo in da suka yi sallah ni kuma ina kitchen na Dora Taliya jalop ganin baki kada su ce ba na girki ina da Rowa.
Ban ji sallamansa ba ballatana shigowarsa dakin ni dai fitowa falo na yi naga ba yanmatan nan sai shi ya na zaune ya na latsa wayarsa.
Cikin mamakin ganinsa na yi masa sannu da zuwa ya amsa.
Ruwa a jug naje na debo masa sai da na kawo sannan ya kalleni ya na fadin"wannan wani ruwa ne? Kai tsaye nace na nan gidan nan ne.
Bude baki ya yi kamar zai yi mgana sai ya fasa ya tashi ya fita.
Ba jimawa sai ga shi ya dawo da ledojin pure water wajen guda Biyar nazo zan karbesa ya matsa gefe ya na Fadin"Kaji min yarinya ke yaushe zaki iya?
Jin haka yasa na matsa baya ya shiga kitchen ya sauke ruwan.
Sai yaga ina girki ya fito ya na kallona Lokaci daya ya na fad'in"Girki ki ke yi?
Da kai na amsa ban yi magana ba Mirmishi ya yi kafin yace"Ki ce yau zan ci girkin Amarya."
Dariya na yi ina Rufe fuskata da Tafukan hannuna.
Wuceni ya yi ya na fadin"Rufe kofa ki zo ki gani."
Ban kawo Tunanin komai ba naje na Rufe kofa na dawo.
Na gansa da kwalin waya kirana ya yi nazo gabansa na zauna ya mikamin kwalin ya na fad"in"Ga wayarki nan"
Ido na zaro kafin nace"Eh..'"
Dariya na bashi sai da Fararen Hakoransa suka bayyana
Cikin kwarin gwiwa yace"Taki ce ni na siya miki."
Sai gani kan kafafuna bakina kamar zai yage.
Na warce kwalin wayan ina dubawa cikin murna nace"Ka siya min waya? Ni?
Da kai ya amsamin kafin yace"Bud'e ki gani."
Rawan jiki yasa na kasa budewa sai da ya karb'a ya bude min ya fiddomin wayar ya kunna min ita ya mikamin
Bakina a washe na karb'a ina dubawa dai na kalleshi na koma kuma ina kallon wayar bakina ya kasa Rufuwa.
Ya yi min abunda na ke so alokacin da nake tsananin bukatar waya.
Na kallesa ya na min dariya ganin yadda na kasa Rufe bakina.
Gira ya dagamin kafin yace"Kin samu ta kiran Amma da su Adda Fati. Zaman kadaicin ya kare ko?
Idanuwana suka ciko da kwallah kawai sai na duka ina fadin"Nagode sosai Allah ya saka da alheri ya kuma kara budi."
Ya amsa da Ameen lokaci daya ya na saka Hannu ya dagoni Tsaye ya na fadin"To baki latsa wayar ba."
Ai ya na cewa haka na koma na zauna na fara latsa wayar ina shige shige.
Gefena ya zauna ya na fadin"Kin iya sarrafa wayar ko?
Cikin murna nace"Eh mana Abubakar ya taba siyamin irin ta kafin auran mu."
Sai da na yi mgana na Tuna a gaban wa na ke.
Idanuwana a sanyaye na dago ina kallonsa shima ni ya ke kallo.
Ammh sai naga ya basar da mgana da fadin"Na saka miki lambata in kina bukatar wani abu ki kirani na saka miki kudi a wayar."
Ya dakata kafin ya cigaba da fad'in"Sannan sai ki kira sauran yan'uwan ki ko?
Da kai ma amsa masa na kasa Rufe bakina.
Ya rasa ta inda zai faramin mganar ne yasa ya yi shuru ni kuma ta duba wayata ina murna kamar an sani a Aljannah.
Kamar daga sama naji ya na fadin"Hasiya kin taba fad'a ma wani ba anan na ke kwana ba ne?
Na girgiza masa kai Lokaci daya ina fadin"A'a."
Ina ji ya sauke ajiyar rai kafin yace"Yauwa. Kada to ki sanar da kowa kin ji ko? Ko Amma ko sauran yan'uwan kin ji ko? Wannan sirrin auran mu ne"
Sai da na yi masa mirmishi kafin nace"In sha Allahu ba wanda zai ji."
Numfashi ya saki mai karfi na samun salama.
Ina kallonsa nace"Na kira Adda Fati?
Kai tsaye yace"Kira ta mana ki na da lambarta ne?
Sai na gyada masa kai jiki na rawa da Hannuna na saka lambarta na kirata ta na dauka taji murya na tace su Asee asee an yi waya kenan nace mata eh.
Hira muka sha na manta da shima afalon ballatana girkin da na dora sai da ya fara kauri ni ban ma ji ba shine yaji ya yi min mgana ina chan muna hira da Adda Saboda murna har Mijinta sai da nace ta bashi mu gaisa.
Shi ya rigani isa kitchen din ya kashe gas din ya na fadin"girkin Amarya ya yi kauri"

Kunya naji da yasa na kasa mgana.
Sai da na sauke tukunyar na bude yaga uban abincin da na Dafa ya kama baki ya na fadin"Hasiya ina zaki kai wannan abincin?
Kai tsaye na kallesa ina fadin"Bazaka ci ba? Kuma zan zuba ma yan kawo amarya har yanzu ba'a kawo musu abinci ba."
Sai ya kasa musamin cikin yanayin mganarsa yace"To zubamin kad'an tafiya zan yi."
Yau sai naji ban damu da tafiyarsa ba.
A filet na saka masa da ruwa na kai masa falo.
Kuma abun mamaki ya ci kadan ya rage ya sha ruwa ya mike yace min zai tafi sai ya kara zuwa.
Ni kuma sai nace ya tsaya mu fita tare na mika musu abincin
Shi ya Daukamin kulan abinci ni kuma na Dauki karamin baho inda na saka musu ruwa da filet da cokullaya.
Har bakin kofar dakina.
Shi ya karbi key din ya Rufemin dakin ya na fad'in"Kada fa ki zauna achan da kin kai musu ki dawo dakin ki "
Da Toh na amsa masa.
Naso ya bani kulan ammh yaki har sai da ya rakani har kofar dakin Ummi sannan ya mikamin na tare hannuna guda d'aya na karb'a da mukullin dakin nawa saura kadan robar hannuna ta fad'i ya yi saurin tallafewa ya na fadin"Kin gani ko? Daman nace bazaki iya ba."
Wasu yan matan Amarya ya gani su biyu a kofar dakin suna kallon mu suna zaune.
Cewa ya yi su zo su taimakamin bazan iya ba ni ko fadi na ke yi wlh zan iya.
Cikin ido ya kalleni kafin yace"Bazaki iya ba SIYA.."
Sai na kasa yi masa gardama dukkansu suka taso d'aya ta karbi kulan d'aya ta karbi Roban sai alokacin nagane wad'anda suka shigo dakina ne.
Bai tsaya ba ya juya ya na fadin Sai da Safe.
Nima na amsa masa da Sai da Safe.

Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086

*Janafty*
*TMWB2K006*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj

*BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*!

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Gaban ayu*.
*Hakkin daka gangariya*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*.
Chapter 15 · 0% Book details