← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 75

Sashe 62

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaune ya ke acikin Office sabon office d'insa tunda yau litini aiki garesa kaca kaca, hankalinsa ya kasu kashi biyu ne daya na kan na'urar da ke gabansa d'aya kuma na kan wata Takardan dake gabansa.
Sanye ya ke da Suit baki da Fari ya sasauta tektie dinsa saboda ya samu Saukin ayyuka.
Ya na aikin ya na sakin mirmishi shi kad'ai da ya tuna wayarsu da Siya yau da Safe. Shagwaba ta ke masa ko yace kukan banza saboda ya sakamata rai zai zo mata weekend sai bai samu zuwa ba.
Saboda akwai wasu ayyukan da ya tsaya yi, yasan kuma in yaje zariya bazai taba iya aikin nan ba in dai ya na ganin Hasiya.
Kuma a yadda bai jima da fara aiki ba, bazai yi wasa ba ballatana aga kamar ya fara wasa da aikinsa.
Kamar zariya gidan haya ya nema anan kusa da inda kamfanin su ya ke zaune.
Tunda aikin ya zo masa ne bagatatan, ya jima da Tura CV Dinsa bai kuma taba saka ransa ba shi mutum ne mai amfani da duk abunda ke Hannunsa.
Ya yi mamaki sanda yaga Sakon Email dinsu suna nemansa, kuma har yazo Abuja interviuw bai gama sakankancewa da zai samu aikin nan ba sai ga shi kafin ya Dawo ma sun bashi accpeted letter.
Kamar kuma Sun san ya siya mota da kud'in da ya tara zai siya, da ya gayama Abba sai ya cika masa ya siya toyota kirar 406 da ita ya zo Abuja nan sannan achan Zariya da ita ya fara zirga zirgan zuwa wajen aiki da Shiga makaranta duk da yanzu Project ya ke yi ya ma kusa gamawa.
A shekara daya da Rabin nan ya yi ta kokarin boye sirrin auransa da Hasiya, ya kuma tare duk wani hanya da wani zai Fahimci wani abu ciki harda yan'uwansa da Tahir shi kan shi.
Yana cikin wannan Tunanin yana aiki Wayar Big sis ta katse shi.
Dole ya ijiye komai ya Dauki wayarta suka gaisa.
Mganar kayan auran Sultana ta yi masa Abba ya ba da miliyan Biyu a had'a mata kayan aure.
Bai yi mamaki ba sanim Daman auren Sultana na gata ne a wajensa.
Auran Hasiya ne ya yi shi da Guminsa.
Kamar yace ta siya komai guda Biyu sai kuma ya fasa sanin abunda zai jawo sanadin subutar bakinsa.
Cewa kawai ya yi su yi mgana da Sultana sai Surayya tace shima Abba yace a yi masa a kwatinsa.
Dariya kawai ya yi yana kara jin Kaunar Abba a ransa.
Shi yasa bai yarda ya kwanta Saboda mahaifinshi na da kudi ba.
Abunda ya sani shine Abba ya tara musu kudi shima zai tarama ya'yansa Saboda yau in Abba ya fadi ya Mutu ba shi kadai zai gaji wannan dukiyar ba, ya na da Sauran yan'uwan da suma suna da Hakki a kan Abba.
Dakyar ya aminta da karb'an gidan da Abba ya ba shi hakal malak a Million Quaters dake garin Gusai.
Anan za'a saka Sultana kafin ya samu inda zai ijiyeta anan garin Abujan
Ammh har acikin ransa a zariya ya ke da Niyar barin Hasiya saboda wasu Dalilansa.
Itama ya na so ya had'a mata lefe duk da ya siya mata wasu kayan, ammh zai bari sai bayan auransa da Sultana tukunmah sai ya had'a mata da Jarin da zata fara sana'a da shi.
Sannan rayuwar da ya ke yi ta Sirri duk ta fara isansa sai dai ba shi da mafita ne.
Hasiya ta zama wani bangare na Rayuwarsa da har Abada bazai iya rabuwa da ita ba.
Shiyasa duk mafitan da ya hango sai yaga gwara ya cigaba da yin Rayuwa guda Biyu a lokaci daya domin tsira da abunda ya ke so da Muradi.
Tunda yanzu ya Fahimci ba wai mganar Tausayi ba ya na son Hasiya.
Yana son Siya irin kauna mai zafin da zai iya aikata komai domin yaga ta na Kusa da shi har gaban Abada.
Dalilinta ya samu natsuwa ta magidanta maza ma su aure, ko gida yaje haka su surayya zasu rika mganar ya kara kiba ya yi haske kamar ba shi ba.
Shi kanshi yasan natsuwar aure na Dabam ne.
Kuma Hasiya ce sanadiyar zamowarsa cikin wanman natsuwar da a koda yaushe bata gajiya da shi in yazo da bukatunsa zata killacesa har sai yaji ta ishesa.
Ba zai ce baya son Sultana ba, ammh Siya ta mamaye kaso mafi rinjaye acikin zuciyarsa.
Ya tuna kwanaki kad'an ya rage asirinsa ya Tonu kafin samun aikinsa na garin Abujan nan ne.
Suka fita cin abincin daren da suka saba da Siya duk karshen mako.
A wani  restaurant  dake zariya wani abokin karatunsa anan Abu ya gansu shi har ga Allah bai gansa ba.
To da yake gayen suna mgana da Tahir ta facebook kuma yana da lambarsa nan da nan ya kirasa ya na Tambayarsa Sadiq ya yi aure ne?
Tahir yace"A'a."
Sai yace ai ya gansa da wata mace anan zariya kuma a yanayin da ya gansu kamar dai in ba mata da miji ba to ba'a fad'in d'ayan.

Tahir ya yi mamaki sosai nan da nan ya kira Sadiq ya na tambayansa.
Shi kuma sai ya tuna Fitansu, ammh sai ya nuna ma Tahir ba shi aka gani ba Domin shi bai ma fita ko'ina ba.
Tahir kamar yaso ya Fahimci wani abu Tunda har alokacin Sadiq bai bari ya Fahimci inda ya ke zaune a zariya ba in yace zai zo sai yace ya na Gusau
To da yake Yanzu Tahir ya yi karfi a siyasa Dan majalisan garinsu ya bashi Shugaban matasan garin Daura na kafafen Sada Zumunta.
Sannan kuma ya Dauki nauyin Cigaban karatunsa a jami'ar  Alkalam da ke katsina. Kuma ya na koyarwa a wata makaranta Sakandirin gwammatin garin.
Gabadaya dai baya samun zama Shiyasa bayan komawarsu gida bai fi sau biyu suka had'u ba sai dai ta waya suna mgana sosai tunda yawancin Tsarin Bikin Sultana Tahir ne Jagora.
Ammh duk da haka sai da Tahir ya Tsaresa da tambayan ko dai bai rabu da Hasiya ba ne?

A lokacin sai da gabansa ya fad'i cikin Basarwa yace"Wata Hasiya? Ni har na manta da ita ma, inaga kamar ta koma wajen mahaifiyarta ma."
Tahir ya ce"Sadiq ka kula. ka sani in har kana wani abun ne ka Boyemin wlh Ramar da ta kwabe maka ba Ruwana Sadiq."
Maganar tahir ta jima na mai yawo acikin kansa ya sani watan watarana bai isa ya Boye wannan abun ba.
Watarana kowa zai sani.
Sai dai ranar ce ya ke jin Tsoron zuwansa, tunda dai abu d'aya ya sani Ruwa da iska ba su isa su Raba  shi da Hasiya ba.
Itama Matarsace da Aure ya ba shi ita.
Ga auran salima ya na Tunanin yadda zai yi da Siya, wannan karon karyan Wajen aiki zai yi mata in yana so su Rabu lafiya saboda yaga ta fara Fahimtar ya na Boye mata wani abu.
Ajiyar zuciya kawai ya ke saukewa a Jejjere kamar na wanda ya tashi jinya.
Sai kuma ya koma kawai ya jingina da Kujerar da ya ke kai.
Fuskar Siya ya ke gani ta na gilmasa, kirjinsa ya ke shafawa a fili ya Furta.
"I MISS U SIYAAASSADIQ..."

*Janafty*
*TMWB2K018*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.
Chapter 62 · 0% Book details