Sashe 53
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya zama Dole ya yi wani abu saboda Dauke musu hankali daga kara munana zargin da suke a kansa.
SULTANA ce ta fad'o masa a rai sai kuma yaga tabbas itace makaminsa a daidai wannan Lokacin.
Da ita zai yi amfani ya nuna musu cewa bai sauya ba, bayan Rayuwar da suka san shi da ita bai yin wata Rayuwar da suke zarginsa a kai.
Ya tuna tunda ya bar garin sau daya ya Kirata a waya, shima zai yi mgana da Umma me ya kira wayarta a kashe sai ya kira Sultanan yace ta kai mata.
Tun daga kuma ranar bai kara Kiranta ba ammh yana ganin sakonta a kai akai duk da yasan duk sakata aka yi ta rika yi masa wad'anan sakunan iskancin.
Sannan yaga maganarta a WhatsApp duk da shi sai ya yi sati bai bude data ba, shi kafafen sada zumunta ba su cika Damunsa ba Tahir ya yi har ya gaji da ya Fahimci baya Ra'ayi.
Da wannan Tunanin ya ta shi, yau wajen aiki zai je tunda bai da shiga makaranta.
Shiyasa da wuri ya fita Tea kawai ya sha ya fita ya bar Flat din da ya Rage agidan ana tarewa aciki.
Sai da yaje wajen aikinsa ya natsu sannan ya kira Sultana bayan ya Duba Lokaci yaga sun isa dawowa daga makaranta.
Sai ga shi Sadiq ya Daddage ya na yi ma Sultana Hira wanda ya ke da yakinin yan saka ido duk za su ji Labari kamar ya sani kowacce na yawan kiranta suna tambayanta kuna waya da Sadiq? Ranar sun samu Labari mai dadi ta sanar da su ya kirata sun sha fira.
Daga ranar kullum sai ya kirata in ya na wajen aiki duk da dai hiran ta su ta karatu da Tambayan gida ne ammah tabbas Hasashensa ya yi tasiri.
Surayya da kanta ta kirashi ta na yi mishi Tsiyan wai ya shiga hannu sai yadda suka ga Dama da shi.
Dariya ya rika yi a ransa ya na fad'in na shiga hannu ko kun shiga Hannu.
Har su Umma suna samun Labari kowa sai yaji dadi jin Sadiq yanzu ya nuna da Gaske ya na son Sultana.
Sai kuma mganar komawarsa Zariya ta bar Tunanin kowa.
Suka koma Binsu da Fatan alheri tare da kara koyama Sultana wasu Dubarun zamantakewar.
Sadiq ya na waya da Abba sosai tare da Mutanen shinkafi ammh sai in baya tare da Hasiya saboda gudun Tautsayi ma kashe wayarsa ya ke da Zarar ya dawo gidan nan.
Ana cikin Hakane Abba ya kirasa da Mganar Salima da d'an abokin kasuwancinsa Alhaji Jibril.
Tunda Had'in da yaso na Sadiq bai samu ba ya ba ma Mubarak izini ya zo ya nemi d'aya daga cikin ya'yansa.
Sadiq ya yi supporting mganar Sosai.
Acikin kuma Satin Mubarak yazo ganin Salima bayan Abba ya Kira Umma da Mama ya sanar da su komai.
Ba'a samu matsala ta bangaren kowa ba sai Salima ta fara compain din cewa ita karatu zata cigaba Tunda suna Zana jarabawar Fita ne daga Secondary, mama ta kira sauran ya'yan yan Dakin su, su Sa'ima suka shige da ita suna mata fad'an ta shiga Hankalinta ga Sultana nan kanwar bayanta zata yi aure ammh ita ta Samu tana wani iskanci.
Duk yadda ta nuna bata so sai da suka Tursasata ta amshi mganar Mubarak.
Har sakeena na fadin bata da Tunani ne? Ba gwara ta yi ta Riga sultanan aure ba ta na dai ji ta na kuma gani Sadiq din baya son auran Sultana ammh Uwarsa da yan'uwansa sun kafe sai an yi saboda sun san amfanin su kuma da ba sa son Sadiq din ya auri wata Daga waje.
Kananun manganganu suna ta tashi, Duk da ga junansu ba sa nuna yan Ubanci ammh akwai wannan kishin Tsakanin ya'yan da suka Had'a Uba d'aya a tsakaninsu.
Salima ba ta da mafita illah na Amince ma Mubarak sannan da yazo suka samu Lokaci suka gana sai taga zata yi auransa domin shima 80% ya yi daidai da Ra'ayinta kamar yadda shima ta yi masa daidai Dari bisa Dari.
Hajiya Murjanatu ba ta so wannan had'in ba saboda a cewarta ba Tsaran juna ba ne shi da Alhaji Sulaimanu kuma ta na da Tabbacin ba domin Allah zai had'a wannan auran ba
Da nuna raahin amincewarta Har ikirarin sakinta ya yi, kuma shima Mubarak din ya nuna mata ya na so, sannan da shawaran yaranta da na yan'uwanta sai ta koma ta yi shuru kawai Tunda ba ta da ta cewa.
Da kansa ya shirya yaje zariya wajen yan'uwansa ya fad'a musu cewa zai kira su in Lokacin neman auran ya taso.
Hajiya Murjanatu ta na mamakin irin zumunci na gidan mijinta da babu ruwansa kowa da kowa, ita kanta ta jima Rabonta da garin zariya da sunan wani sha'ani.
Suma ba sa zuwa ballatana matansu da ya'yansu hana rantsuwa ta san iyalan Alhaji Tanko da iyalansa, sai Goggo Saratu ita gwara ita ta na biyo dan'uwan nata.
Hajiya Halima ta garin ikko kuwa ba su had'u ya kai sau biyar ba.
Ita fa tun wani rasuwar kanin Babansu Zahra da akayi ta yawo da Cewar Dalilin yar da ya Haifa mai Farar kafa ce ta yi sanadiyar karayan arzikinsa da Mutuwarsa bata kara ganin Hajiya Halimar ba.
Su kansu yaran na su ba su san kowa ba domin da wayan su bai wuce sau d'aya suka taba zuwa garin da wayaun su ba.
In ta yi masa magana sai yace shi ya ji da aiki yara kuma suna karatu in tace ita ya barta ta rika zuwa sai yace a'a, rabonta da Zariya tun auran Diyar Kaninsa Saminu wajen Shekaru hud'u kenan.
Ita ta na ma so ta yi masa mganar ya'yan dan'uwansu da ya rasu da yarinyar da akace ta na da Farar kafa sai ta manta Tunda dai ita bata kara jin Labarin su ba.
Abun na ranta ya na dawowa da Daddare bayan ta Shiga masa sannu da zuwa ta kai masa ruwa.
Ta na zaune gefensa ta ce"Maganar auran Murabak din yanzu ne?
Ya na gyad'a kai yace"In dai suka Fahinci juna me zamu jira?
Hajiya Murjanatu tace"Hakane to Allah ya tabbatar mana da alheri su waye zasu nemam auran?
Kai Tsaye yace"Alhaji Tanko da Saminu mana ina da wasu yan'uwan da suka fi su ne?
Mirmiahi ta yi kafin tace"Baka da shi kam tunda duk sun rasu, ya ma sunan wannan wanda ya taba rasuwa kace min Ya haifi wata yarinya mai Farar kafa sai da ta talauta shi kuma sannan ta yi Sanadiyar Mutuwarsa?
Sai da ya sha ruwa Sosai sannan ya mikamata kofin ya na fadin"Mamman kenan ki ke mgana."
Da Sauri tace"Yauwa shi, wai ina Labarin iyalansa da matarsa?
Alhaji Jibril ya tabe baki kafin yace"Ina zan sani? ni dai chan kwanaki naji Alhaji Tanko na mganar yarinyar ta sake wani aure kuma wai ko uwar tasu ta koma garin su."
Hajiya Murjanatu tace"Ina ne garin na su?
Cikin karamin tsaki yace"Bafullatanan Ruga ce na manta sunan garin, yaran kamar su hudu ne ina ji sauran biyun sun yi aure ita mai Farar kafar ce akace auranta uku duk wanda ta aura sai ta talauta shi wani ma an ce dakyar ya rayu."
Cikin Tsausayi tace"Allah Sarki ku ma da laifin ku ai hakkin ku ne ku Kula da su bayan kasa ta Rufe idanuwansa."
Cikin zaro ido ya kalleta kafin yace"Uban waye zai Daukan ma kansa masifa ? Ko Tanko da suke uwa da Ubansu bai Daukan ma kansa ba ballatana wani, ke ana gayamiki yarinyar sai a Hankali kina wata mganar ta Dabam"
Hajiya Murjanatu tace"ammh ai babu wata Farar kafa a addini Abban zahra Canfi ne da rashin Tauhidi."
Kallonta ya yi daga sama har kasa kafin ya tabe baki.
Zata kara mgana ya Daga mata hannu Lokaci d'aya ya na mikewa ya shige ciki ya barta nan zaune.
Da kallo ta bisa kafin ta Sauke Numfaahi.
A cikin ranta sai taji Tausayin wannan Yarinyar Allah kad'ai yasan Halin Tsaka mai wuyar da ta ke Fuskanta a wajen Mutane.
Abu kamar wasa sai ga shi ya Tabbata acikin watan waliyan Mubarak suka je har Gusau gidan Alhaji Sulaiman suka yi ma Mubarak Tambayan aure.
Su Baba Sammani suka ba su Salima a matsayim mata.
Sai dai ba'a tsaida Lokaci ba tunda Mubarak na gini sai aka saka nan da Shekara daya da Rabi kafin na Sultana da Sadiq kenan.
Alhaji Jibril ya fi kowa jin dadin wannan Labarin bakinsa har kunne ko Mubarak albarka.
Alhaji Tanko da suka Dawo nan kaduna gidan Alhaji Jibril fadi ya ke yi"Jibo ina ka had'u da wannan Ahalin ma su kudi haka?
Alhaji jibril ya yi dariya kawai bai ce komai ba. shi ko Saminu fad'i ya ke yi" ni dai ko akwai kanwarta sai Nasiru Shima ya nema."
Alhaji Jibril ya yi dariya kafin yace"Shege saminu har yanzu baka Daina son abun duniya ba ko?
Shima ya na dariya yace"Yaya kaima fa na sanka baka kwai sai da Zakara."
Dariya ya Bushe da shi kafin yace"Ka sanni sosai Saminu."
Suna wannan Hiran ne a falon Alhaji Jibril bayan sun dawo daga Gusai da labarin irin sha tara na arzikin da aka yi musu a chan.
Su ko sauran yan'uwan Salima mata yan Dakin Umma da suka ji Labari sai sukace meyasa ba'a hade da na Sadiq da Sultana ba? Umma tace itama sai da ta yi wannan tunanin ammh ganin kamar Mama ta fi son a fara yin na Salimar Shiyasa bata ce komai ba.
Suma tace su bi mganar da Fatan alheri kada su furta komai.
Innani ko sai shiri ta ke ta na Murna zata aurar da jikoki uku alokaci d'aya ba ta ga ta zama ba.
Duk abunda ta samu sai ta boye tace na Hidimar Bikin Magajin gida da Sultana ne, Sai kuma Salima tace masu kid'an kwarya har bakin get sai sun cika gida. su san ranta ya kai na ganin auran jikokinta.
Ba ma wanda ya zauna da ita ballatana ya sanar da ita ba Rana daya za'ayi auran ba.
*******
*Bayan wata biyu.*