Sashe 16
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan ya b'ace ma ganin mu ne har ma ya bude get ya fita daga gidan. Budurwan da ke kusa da ni ta kalle ni ta na fad'in"Ba shi ne mijin ki ba?
Cikin mamaki na kalleta sannan na gyad'a mata kai na alamun eh.
Sai naga sun kalli juna da ta kusa da ita kafin ta kara kallona ta na fad'in"Oh na gane kina da abokiyar zama ne ko?
Kura mata ido nayi cikin mamaki ina so na fahimci dalilin tambayan nata sai da ta ambaci abokiyar zama na Fahimci bakin zaren.
Dan daure fuska na yi kafin nace"A'a me ki ka gani?
Yanayin yadda nayi maganar ne yasa tace min bakomai.
Ina gaba suna bayana har cikin Dakin Ummi sai da muka kwankwansa wata yarinya ta zo ta bud'e mana.
Nasan kawai sun yi shuru ne ammh suna da tambayoyi fal acikin su.
Ni kuma na datse su ne saboda nima bani da amsar tambayan na su in kuma suka matsa zasu san abunda bai kamata su sani ba.
Sai a lokacin naga Ummi Amarya tunda har cikin bedroom din ta na shiga yan'uwanta da kawayenta suna ta min godiyan abinci da Dawaniya.
Hakane din ne baza mu wuce sa'annin ba sai dai ganin farko da na yi mata na Fahimci ba kamar ni ta ke ba.
Ita ta na da wayewa sosai da Bud'ewar ido sannan rayuwarmu da muka taso ba daya ba ne da ni da ita.
Ban wani jima a dakinta ba na musu sallama na koma dakina saboda ina zumudin na koma daki na kira Ramatu da Sabuwar wayata tunda itama na Haddace lambarta.
Ina ko komawa daki na dauko Sabuwar wayata raina fes na saka lambar Ramatu na kirata.
Nayi murnan jin muryata sannan taji dad'in jin na samu wayar da za su rika samuna.
Mun jima muna ta hira da ni da ita har gwarancin Noor nace ta sakamin ina so naji.
Gajiya inaga tayi dare ya yi yasa ta fara Hamma ta na fadin"Ke wai mijin ki baya nan ne hala?
Bansan me nace ba sai ji nayi bakina yace"Eh."
Da mamaki Ramatu tace"Eh kuma? Ke kad'ai ne yanzu a wannan gidan Hasiya?
Da sauri nagyara mgana ta da cewa"Ya na nan abokinsa ne yazo suka fita tare. Yanzu zai shigo."
Sai Ramatu ta sauke Numfashi kafin tace"Oh na zata baya nan nace ko yaje kauyen su ne?
Ni dai daganan ban kara mgana ba na samu muka yi sallama da ita.
Ban hakura ba na kara kiran Addan Fati nace ta turomin Lambar Adda
Rukayya da Adda ina so na yi mgana da Amma.
Karamin Tsaki Adda Fati taja kafin tace"Baki da Hankali ko Hasiya? Kinsan karfe nawa ne yanzu?
Sai da ta fad'a na duba agogon wayarta naga goma ta wuce.
Jiki a sanyaye nace"Sai da Safe."
Bata amsamin ba ta kwashe wayarta, sai na koma na lafe kan kujera ina cigaba da danna wayar tawa yau ban ji na wani damu ba.
Sabuwar wayar ta Daukemin Hankali na sosai.
Ina cikin Saving din lambar su Adda Fati na shiga cantact sai kawai naga Lamba da sunan ASSADIQ.!
nayi jim ina kallon Lambar sai na samu kaina da murmusawa.
Ranar na jima ban yi barci ba game na rika yi a wayar sai da idanuwana suka fara yaji na ijiye wayar na yi shirin kwanciya
Washegari ma Ummi ni ta roka na saka musu ruwan zafi sannan na ara musu kofinan da suka sha tea nima ba kayan kitchen din gareni sosai ba abunda na ke da shi na ba su.
Ranar kamar a gidan mu ne bikin Saboda duka Danginta nan suka zo da rana aka kara gyara daki.
Nima ba laifi ban wani zauna adaki ba ina dakin Ummi ina ganin abunda suke yi da rana ma Hajiya zainab tace kada na Dafa abinci daga gidan su Ummi za'a kawo abinci.
Lafiyayyar Jalop harda Nama suka Diba'rmin a kula mai yawa shi naci da rana har na ijiye na dare.
Da yamma kafin kawayenta da sauran yan'uwa duk sun watse sauran ne da suka Rage ango ya kawo mota har da Ummi suka dauketa zuwa gidan Surukanta, ammh kafin su tafi sai da Hajiya zainab tace ga Ummi ne mu zauna lafiya da juna nace mata in sha Allahu.
Ni dai ina ganin haka na shige daki na kulle na dauro alwala na yi sallar mangariba sannan na dauko wayata na kara kiran Adda Fati na kara mata Tuni lambobin da nace ta Turomin.
Sai tace bari ta bama Habiba ta Turomin ba jimawa Sai ga lambar Adda da ta Adda Rukayya.
Jikina na rawa na kwashe Lambar Adda na saka a cikin wayar ita na fara kira har sai da ta kusa katsewa sannan Adda ta dauka da sallamanta cikin Hausanta da ta had'e da Harshen Fullanci.
Cikin Zumudi na kira sunanta da Adda.
Bata gane ni ba sai da nace mata Hasiya ce sannan ta gane muryata.
Cikin shakiyanci tace"Au Hasiya ce? Kin gama Fushi da uwar taki kenan kin kira? Sai na kasa mgana kunya ta kamani cikin sanyin murya nace"Ku yi hakuri Adda."
Bata damu ba tace"Yar nema. Ga uwar taki tunda yanzu kin gane muhimmancinta."
Nasan tana mikama Amma wayar ta fice daga d'akin ina jin muryan Amma ta na kiran sunana.
"Hasiya."
Sai kawai na sakar mata kuka ina Fad'in"Amma ki yafe min don Allah."
Mirmishin nan nata ta yi min kafin tace"Baki yi min laifin komai ba Hasiya. Ban kuma rike ki a raina ba nasan komai daren dad'ewa watarana zaki kirani ki godemin."
Ina sharen hawaye nace"Ki yi hakuri Amma."
Amma tace"Nace kada ki damu bakomai yanzu dai ki fad'amin kina Lafiya? Ina Abubakar ina Fatan ba wata matsala ko?
Cikin Sanyin jiki da na Murya nace"Lafiya kalau mu ke Amma."
Ina jin Ajiyar zuciyar Amma kafin tace"Alhamdulillah daman ni na sani akwai wani lokaci da zai zo mutane su gane babu mai yi sai Allah."
Ina gyad'a kaina kamar ta na ganina nace"Amma ki ga fa babu abunda ya samu Assadiq wannan wayar ma shi ya siyamin ita jiya."
Amma na dariyan jin dadi tace"Daman ai ke baki isa ki yi ma wani mutum arziki ba, balle ki yi masa Talauci kuma ke baki isa ki sauya rayuwar wani ba Allah kad'ai ke da wannan ikon Hasiya."
Da sauri nace"Hakane Amma."
Amma Nasiha ta cigaba da yi min ta na kokarin nuna min komai ma da ya faru a baya ba ni bace daga Ubangiji ne kamar yadda ta ke kara gayamin yanzu.
Na kasa bude baki na gayamata kalubalen wannan auran sai naji bazan iya wargaza mata wannan Farincikin nata ba sai na yi shuru da bakina na saki jikina muna ta Hira.
Cikin Shagwaba nace"Amma na yi kewar ki yaushe zaki zo na gan ki?
Amma ta yi dariya kafin tace"Hasiya ki zauna lafiya a gidan auran ki. Ina nan watarana ke da Abubakar zaku zo ku gaisheni in sha Allahu."
Sai na kasa ce mata komai sai na basar da wannan mganar da fadin"Amma kina jin dad'in zaman chan?
Amma tace"Alhamdulillah hankalina a kwance nasan ya'yana suna cikin Tabattaciyar rayuwar da na yi musu fata."
Jin Amma na lafiya yasa sai naji na samu natsuwa mun jima muna Hira ina ta bata labarin gidan da na ke ciki jiya an kawo wata amarya zamu zauna mu biyu yanzu kafin sauran su tare.
Amma ta ta yi min fad'an na kama kaina nasan dai kalubalen zama a gidan Haya ji na yi kamar ban ji ba na gani nayi kamar ban gani ba sai na zauna lafiya nace mata in sha Allahu.
Sai da aka kira sallar isha'i sannan Amma tace zata yi sallah nima naje na yi sallah sai alokacin muka yi sallama.
Ban samu na kira Adda Rukayya ba sai da Safe kuma bata Dauka ba.
Sai chan da rana ta kira muka gaisa tamin murna jin nayi waya tace daman rashin wayar nan ba dadi gwara dai a rika jin mutum ya zauna Shuru ba waya a hannunsa.
Ba mu cika had'uwa da Ummi ba tunda ta na ta cin Amarci sai dai ranar litini mun had'u da Safe ta fito Diban ruwa nima haka.
Muka gaisa cikin sakewa sannan da Rana ta kawo min Cincin da su Dublan da yawa harda Alkaki.
Ban taba ganin mijinta ba sanda ya ke fita ina dakina kuma sanda ya ke shigowa ma ba na waje ina cikin Dakina.
Sai dai ina jinsu suna ta baki maza da mata mazan ina tunanin abokansa ne suka zo ganin Amarya da yammah haka ko da Daddare.
Matan kuma kawayen Ummi ne da yan'uwanta masu zuwa ganin daki da Rana.