← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 75

Sashe 23

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai nace masa akwai sanyi shi kuma yace kada na damu.
Ammh ban barshi haka ba sai da na Dauko masa zanin gadona nace ya yi Rufa da shi.
Ummi ma ruwa ya taresu ita da Mijinta ni dai har na kwanta banji dawowarsu ba.
Kwana aka yi ana ruwa har asuba ana ta yafyaf na alamun ruwa.
Shiyasa Sallar asuba ma shi ya kara jamana Jam'i.
Samakon wekeend ne yasa bai yi Tunanin zuwa wani waje ba
Bayan mun karya da Safe tunda shinkafar jiya yace na Dumama masa ita zai ci nima ita naci.
Gani na yi ya na ta juya wuyansa kamar yana masa ciwo yasa nace ya shiga ciki ya kwanta ya mike Zuwa anjuma.
Bai yi gaddama ba ammh yace sai ya yi wanka saboda sanyin gari yasa na saka masa ruwan zafi ya yi wanka sannan ya koma ya kwanta.
Ni daman tun safe na yi wankana, abun da ya ke bani mamaki in dai yazo gidan nan to kashe wayarsa ya ke yi baya kunnawa ballatana ma akirasa.
Kuma ya sha barci sai azahar ya tashi ya yi alwala ya tafi masallaci Ummi kuma da na fita har dakinta na kwankwansa naji shuru sai nayi Tunanin a gida ta kwana Saboda Ruwa sannan ga dare.
Na dauka zai ce zai tafi da yammah ammh sai naji malamin ka shuru.
Ina dafama abinci kuma yaci sosai sai da mangariba ne ya fita sallah yace min sai an yi sallar isha'i zai dawo.
To har wajen tara bai Dawo ba sai chan ga shi ya Dawo da wata karamar jaka ashe kayansa ne aciki ya Dauko.
Tunda ba shi da wanda zai sauya na jikinsa sun yi datti ba shi da wasu.
Aiko ya na cire kayan washegari da Safe na wanke masa su tas na shanya.
Bai ma gani ba sai da suka bushe na kwaso ina ninke masa.
Fad'a ya yi min da wai hannuna da ba kwari ne zan iya wanki.
Dariya na yi har sai da na rike ciki ina mamakin in ya na Tunanin Saboda yanayin jikina ya ke min kallon mara karfi.
Wasa wasa tun ina saka ran Assadiq zai ce min zai tafi har na saki jikina.
Daganan ya ke tafiya wajen aikinsa ya kuma dawo, an ce mutum rahma ne sai na fi walwala saboda zamansa tareni da ni shi kanshi kusan hakane baisan ya akayi kawai yaga ya na ta kwaso kayanshi zuwa gidana ba.
Tundaga ranar bai kara komawa Samaru ba sai dai za shi wajen aiki.
Sati daya cur muka kwashe tare kwanaki bakwai masu muhummamci matuka a wajena.
ko da ba Daki daya mu ke kwana ba Assadiq ya na da kirkin sannan ya na da kyakyawan mu'amala.
Ko aiki na ke yi ya na tayani sannan ya na nan ruwa dakina ya kare yaga na fara Dibowa daga waje ya faramin Fad'a wai na Dauki Almajiri mana nace masa ba Almajirai a barayin sosai.
Shi da kanshi ya Tube ya cikamin ko'ina ranar ma ina wanki yace na kawo zai tayani da na hanashi yaki hanuwa sai nace ya yi min Dauraya da Shanya.
Atsakar gida muka yi wannan Diraman da shi Ummi bata nan ta na makaranta, shi kuma ya shanyamin su tas sai nace mu had'a da kayansa mu wanke sannan ya amince.
Ina mamakin yadda kowani aiki ya iya shi sai da na tambayesa ya yi min mirmishi kafin yace"Ni fa Tashin kauye ne sannan goyan kakane ba kuma goyen Sangarta ba."
Har nake ce masa yaushe zai kaini na gaishe da Kaka.?
Kai Tsaye yace ba yanzu ba ammh zamu je watarana.
Ina lura da shi ko waya zai yi sai dai ya kunna wayarsa ya fice daga gidan sai ya gama wayarsa ya ke dawowa.
Ban taba tambayansa ba sannan ban taba saka masa ido kan wasu al'umran da bai sakani aciki ba.
A tunanina ko fita ya ke yi ya na mgana da Uban gidansa kila baya so yasan yana wajena.
Har acikin raina ban kawo tunanin komai ba.
Sadiq bai san Tahir ya Dawo ba sai ranar da ya cika sati a gidan Hasiya da yammah ya na kwance saman kujera ni kuma ina kitchen ina Kokarin yi ma na abincin Dare.
Wayarsa tun safe ta na kashe babban wayar kuma ta na chan samaru ya barota.
yaana kashe wayar ne saboda itace wayarsa da kowa ya san shi da ita akwai matsala in ya na barinta a kunne a kusa da Hasiya.
Ya kunna ne zai kira Tahir saboda Shekaranjiya sun yi mgana ya tambayeshi yaushe zai dawo?
Yace masa bai saka rana ba duk da Jikin Hajjan da Sauki har an sallamo su sun dawo gida.
Tahir da yajisa shuru ya tambayesa sai ya yi masa karyan daga wajen da ya ke bautar kasa ne bai samu Sarari ba.
Ya na kokarin kiran Tahir din sai ga wayar Tahir ya shigo.
Hanyar Kitchen ya kallah kafin da Sauri ya tashi ya shiga ciki ya Daga wayan
Ko sallamansa Tahir bai amsa ba yace"Kai dilla kana ina ne? Na dawo tun dazu ban ganka ba."
Sai Sadiq yaji gabansa ya fad'i da Sauri yace"Arm eh ina wajen aiki ne gani nan zuwa."
Tahir yace"Naga kuma bakwa kaiwa yammah?
Sadiq yace"Ina hanya gani nan zuwa."
Daga haka ya katse kiran.
Sai yaji zufa na ketomasa kamar Abba ne ya kira shi.
Bai tsaya ba ya fito daga Dakin Dole ya tafi yanzu bayaso Tahir ya Fahimci ga inda ya ke duk tsawon kwanakin nan.
Bai ma yi tunanin Tsayawa Dibar kaya ba ballatana takalmansa da ke gidana Jakarsa kawai ya Dauka sai kuma ya yi mantuwa laptop dinsa kan kujera bai sakata aciki ba.
Ina kitchen ya leko ya na cemin zai tafi yanzu.
Cikin mamaki na mike ina fadin"Tafiya kuma? Yanzu?
Ya na duba agogon hannunsa yace"Wannan megidan nawa ne ya kirani tafiyar gaggawace ta same mu. Zan kira ki a waya ki kula da kanki."
Daga haka ya wuce lokaci d'aya yana cemin nazo na kulle kofa.
Sai da ya fita ne na dawo naga Na'urarsa saman kujera kuma ya riga ya tafi, ni kaina duk jikina ya yi sauki Daman ban riga na Dora girkin ba ina gyara kayan miya ne.
Sai na barshi na koma kawai na zauna na yi Tagumi.
Shi ko Sadiq ya na zuwa ya yi ma Tahir karyan sun tsaya wani abu ne.
Shi kuma Tahir bai kawo wani Tunani a ranshi ba.
Hirar Hajja suka dinga yi da ciwonta har suka kwanta sai washegari ne ya Fahimci ya baro Na'uransa a gidan Hasiya.
Kuma sai da Tahir ya lura ba bu ita da ya tambayi Sadiq sai yace a wajen aiki ya barota.
Sannan suna saka takalman junan su Tahir ya Fahimci ba wasu takalman Sadiq.
Cikin mamaki ya tambayesa.
Wannan karon Sadiq sai da ya kusa ba da kanshi kafin karyan ya kai folish ya fad'o masa.
Ammh duk da haka sai da Tahir ya so ya gane wani abu.

*LAME NIG!*

*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*

*Janafty*
*TMWB2K008*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

*LAME NIG!*

*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj

*GUSAU.*
Asabar, 10:50am.
Chapter 23 · 0% Book details