← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 75

Sashe 72

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai duk yadda na so na saki Jiki da shi na kasa kamar baya, da nake jin Matukar kosawa kasancewa da shi a lokacin naji komai ya fita kaina.
Shi kanshi ya Fahimci wannan karon ban yi zumudin zuwan shi ba sannan ban yi masa rawan jikin da na saba yi masa a shimfid'a ba, ban kuma nuna na yi kewar kasancewa da shi ba kamar yadda ya rika gayamin lokacin daga ni har shi muka samu natsuwa.
Da ya neme ni ban hanashi kaina ba, Saboda in na hanashi zai zargi wani abu Tunda ban taba yi masa gaddama ba ni mai tallafinshi ne in dai ya zo da Bukatarsa.
Shiyasa na ba shi had'in kai ammh ba Dari bisa dari ba, abunda bai sani ba yana kasancewa da ni ina Sharan hawaye tunda nasan daman ya ijiyeni ne saboda na zama abar Deb'e masa kewa sannan ina Tunanin wata kila nan da Lokaci kad'an zama na da Assadiq zai zama shud'adden Tarihi kamar yadda na Abubakar da Salisu ya kasance a Rayuwata.
Sai da muka Tsarkake jikin mu sannan muka sake komawa muka kwanta duk yadda na so na makale masa a jiki kamar yadda saba a baya na kasa sai na koma gefen gado na lafe ina maida Numfashi.
Sai jinsa na yi ta bayana ya kwantar da kansa a saman wuyana ya na leken Fuskata sai na yi Saurin Runtse ido alamun na fara barci.
Yar dariya ya yi ya na Jan Hancina kafin yace"Siya fushi ki ke dani Saboda ban zo miki wanchan satin ba ko?
Ban ce masa komai ba ya cigaba da Fadin"Ki yi min afuwa Siya ta, kinsan yanayin aikin namu, sannan ga nisa in nace duk sati na rika dawowa akwai gajiya acikin Lamarin, ammh ina nan ina kokarina Dauke ki zan yi na maida ke kusa da ni in sha Allahu."
Ina jinsa a raina nace ji karya ba Sai dai kila Sultana ka ke nufi.
A fili ko dan motsawa na yi kafin nace"Ni ba fushi na ke yi ba, Barci kawai na ke so."
Jin haka yasa ya juyo dani muna Fuskantar juna kafin yace"Kin tabbata.?
Sai na gyad'a masa kai cikin sanyin murya nace"Na tabbata."
Saboda ina so ya kyaleni, ban san kuma wata Doguwar mgana sai ji na yi ya rumgumoni a jikinsa ya na fadin"Nan ne wajen barcin ki kin sani ko?
Sai na gyad'a masa kai, kaina ya kwantar saman Kirjinsa lokaci d'aya yana shafa sumar kaina zuwa bayana.
Runtse idanuwana nayi kamar mai barci ammh ba barci na ke yi ba.
Kamar yadda shima ba barcin ya ke yi ba ya lula cikin Tunanin mafita.
Da gaske ya ke yi ya fara Tunanin neman Muhallin zama a Abuja.
Kuma in dai ya samu to da Siya zai tafi domin ya na Azbatuwa saboda rashinta.
Sultana kuma ta zauna a Gusai ya rika zuwa ya na ganinta.
Barci ne ya kwasheni ban sani ba, shi kuma sai da Dare ya Tsala ya samu barci.
Da Safe sai da na bari mun tashi mun karya, mun yi wanka ni kuma na gama Share share da goge goge, ya na zaune saman kujera ya na aiki a laptop dinsa na dauko nawa na zo kusa da shi na zauna.
Bai damu ba ya Dauka wani abu zan nuna masa na bangaran karatuna.
Hankalinsa na kan abunda ya ke yi yace"Kun kusa komama makaranta ko?
Kai Tsaye yace"Eh Monday ta sama."
Na fad'a ina Nuno masa Hoton nan sai da na kallesa sannan nace"Assadiq su waye wad'anan da nagan ku kun yi hoto tare?
Da Sauri ya Dago ya na kallon Abunda na ke Tura masa, Sandarewa ya yi a zaune kamar ruwa ya cinyesa.
Duk da Safiya ne sai da naga ya fara zufa sannan rashin gaskiya da Razana ya bayyana Kuru kuru a saman Fuskarsa
Sai na yi mirmishi kafin nace"Abokan karatun ne ko?
Da Sauri yace"Eh Eh, tare muka yi karatu da su a zariya."
Cikin kallonsa nace"Ayya sai kuma naga kamar a gida kuka Dauki wannan Hoton? Hala gidan daya daga cikin su ne?
Da Dauri yace"Eh.! Eh."
Sai ya kasa mgana da Sauri ya karb'i Computer a hannuna a gaba ya latsa Delete ya goge shi.
Cikin mamaki na kallesa kafin nace"Me yasa ka goge min?
Kai Tsaye yace"Ba shi da Muhimmanci ne."
So na ke ya kalleni ammh ya kasa duk ya Daridice alamun rashin gaskiya Muraratun
Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa, ina ganinsa ya na ta kara Dube Dube a cikin Computer Tunaninsa ko kila akwai wani abun da in nagani zai Tsarwarsa komai.
Ban nuna masa na Damu ba, ko na nuna na Fahimci ba shi da gaskiya.
Yadda ya kasa samun natsuwa yasa na kara Tabbatar da Zargina.
Tashi na yi na bar masa falon ganin yadda gabadaya ya rikice ya kasa aikin gabansa sannan ya kasa iya kallon Barayin da na ke saboda kunya da nauyi.

Assadiq bai taba kawo ma ransa da cewa Hasiya ta had'u da yan'uwansa a kaduna ba, Shiyasa sai ya yi Tunanin tunda ya goge Hoton ba lalle ta Zurfafa Tunani a kansa ba, ballatana har ta gano wani abun ba.
Ya so ya kama kanshi Sanda yaga Hoton ne tambayar da na yi masa ita ta bashi Tabbacin ban Fahimci komai da ya Danganci Hoton ba.
Abunda bai sani ba na Dinkesa ne a baibai kamar yadda shima ya jima ya na Dinke ni.
Har ya gama Weekend dinsa ya tafi Ranar Lahadi da yammah ban kara nuna masa wani abu ba, abunda ya kara bani mamaki ko kafin Tafiyarsa sai da ya nemeni kuma na bashi Had'in kai sai bayan tafiyarshi na zauna Ina Tunanin haka Assadiq zai ta moran jikina a banza ni ya so ka shemin Rayuwa ya hanani haihuwa.
Shi kuma zai yi auransa da Matar da ya ke so kuma Danginsa ke so ta haifa masa kyakyawan Zuru'an da ya dad'e ya na fata.
Ni kuma ko Oho rayuwata bata da wani amfani ban chanchanci samun wani abun Farinciki a Rayuwa ta ba Tunda Kaddarata ta zo a haka, sannan ina Dauke da Bakin Fentin da zai iya shafar Rayuwata kila har bayan Mutuwata.
Na yi kuka kamar raina zai fita kukan da ya zame min sana'a a kwanakin nan ga shi ba ni da bakin mganar da zan iya taran wani na yi masa mgana, Wannan al'amarin abunda ya shafi Rayuwata ne ban zan so na zame ma yan'uwana Damuwa a koda yaushe ba.

Na yi Tunanin Ramatu sai kuma na Fasa Tuna itama na yi mata karyan, naje garin su Assadiq naga Ahalinsa ni ma kuma sun gani, yanzu ban isa naje musu da wata mgana ba.
Amma ce na yi Tunanin kira sai da kuma na Kirata na kasa gayamata abunda ke damuna.
Sai kawai na Bige da ce mata"Amma in bawa ya shiga matsanancin Damuwa  sannan ya rasa mafita wani irin mataki ya kamata ya Dauka?
Sai Amma tace"Matakin da zai Dauka shine na Dogara ga Allah, ya maida Lamarinsa ga Ubangijin Sammai da Kassai, ya kaskantar da kansa a gabansa ya Rokesa mafita Allah shi Kowa ne in nace kowa ina Nufin kowa da komai shi ke samar da mafita da warwara al'amuran mu cikin gaggawa in ya so hakan Hasiya, ko kuma ya jinkirta al'amarin har zuwa Lokacin da zai Ribanya maka kyakyawan Tanadin da ya yi ma bawa."
Da kalaman Amma na yi amfani na maida lamarina a wajen Ubangiji, na Dage da Ibada ba rana ba Dare na yi kuka na roki Allah in har aurena da Assadiq akwai alheri aciki Allah ya Daidaita al'amarin da kansa, in kuma babu Alheri Allah ya sa ya sahalemin cikin kwanciyar Hankali ba sai Rayuka sun baci ba.
A haka muka zo muka koma makaranta, sai hakan ya rage min Damuwa na dage da karatuna gefe daya kuma muna tare da Safiya Ahmad.

Assadiq bai zo ba sai bayan Sati uku, a kuma zuwan ne ya biya min kudin makaranta sannan ya bani kudin Handout da sauran Bukatu da zai tafi ya Turamin 50k yace na ijiye a acct dina, bayan 10k din da ya bani a Hannu yace min na zirga zirga ne.
Duk da ina addu'a ammh muna taba juna a waya ni da Saliha so na ke kada Lokacin Bikin ya bace min a lokacin ne na ke so na kara tabbatar da abunda na ke Zargi a kan Assadiq.
Abu kamar wasa sai ga shi mun kulla Zumunci da Saliha ita ke fad'amin ma yar'uwanta Sajida ta haihu a Gusai ammh bazata samu zuwa ba, sai biki Saboda ya yi nisa da ya ke mun yi Saving din Lambar juna muna ganin Statue din junan mu.

Anan naga ta Dora Hotunan Taron suna na yan'uwanta da aka yi a Gusai.
Wani Hoto da yaja Hankalina Shine wanda Maijegon tare da wata ta rike Jajarin a Hannunta Fuskarta da yanayin mirmishinta kamar Assadiq.
Sai da na yi Tagging na Tambayeta"wannan ma yar'uwarki ce Saliha?
Sai tace"Yes Big sis kenan itace Babba a gidanmu Sunanta Surayya itama anan Gusau ta ke aure"
Wannan Hoton har Daukansa na yi na rika Zooming ina ganin abun mamaki.
Ina da Hotunan a Assadiq a wayata wasu tare mukan Dauka wasu kuma shi ya Turamin na rika Dubasu ina mamakin ga kammani nan Zahiran da suka kara bani Tabbacin abunda na ke Zargi.

Sannan kuma in ban manta ba a lokutan baya ya sha fad'amin sun tafi aiki da Megidansa Gusai kenan Gusai ne anihin mahaifarsa.
Saboda kara samun Tabbaci yasa na Tambayan Saliha da cewa su yan wani gari ne?
Ma'ana assalin su, kai Tsaye ta ce min su Asalin Mahaifinsu mutumin Shinkafi ne.
Kawai a raina sai nace shikenan Hujjoji masu karfi sun kara tabbatarmin da wad'anan matan da ma had'u da su a kaduna sune Ahalin Assadiq da ban sani ba.
Sai na Kudira a raina mamakin da zan ma Assadiq bai taba zaton zan iya basa wannan mamakin ba.
Na kudiri wani niyya acikin Raina Niyar daga ni sai Ubangijina suka sani.
Zan shayar da Assadiq mamakin da ya shayar da ni, kila ma nawa mamakin yafi gigitasa fiye da nawa.

*******
Chapter 72 · 0% Book details