Sashe 45
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da Safe kuwa wasan buya na fara yi da shi, shi ko a jikinsa ni kuma ba na ma iya Had'a ido da shi Saboda kunyar abunda ya faru jiya.
Ai tundaga ranar ban kara marmarin ya kunna mana kallo ba, kwana biyu tsakani yace nazo mu yi kallo.
Kai tsaye nace a'a bazan yi kallon ba yau.
Cikin mamaki ya kalleni kafin yace"Ko kina tsoron kada a yi abun ran nan ne?
Sai da ya fad'i haka na kallesa sai kunya ta kara kamani sai na juya sum sun na koma kitchen ina rarraba ido shi kuma ya bi ni da dariya Lokaci d'aya ya na fadin"Kizo mu kallah na yi miki alkwarin makamacin abun wanchan ranar bazai kara faruwa ba"
Ina jinsa ban fito ba ganin naki zuwa yasa shima duk bai ji dadin kallon ba sai ya kashe shima ya koma ya kwanta ya na mirmishi shi kad'ai.
Ranar jumma'a da Safe Tahir ya kirasa yace gobe zai dawo zariya.
Sadiq na jin haka yace"Ni kuma ina hanya."
Tahir yace"Hanyar ina?
Sadiq yace"Zariya"
Tahir yace"Shine baka gayamin ba?
Sadiq yace"Ina shirin kiran ka ne sai gashi ka kira."
Tahir ya katse wayarsa da Tsaki ya bar Sadiq na Dariya.
Jin Tahir zai dawo gobe yasa ya ce min gobe zasu yi tafiya shida megidansa, ai sai naji ba dad'i tunda kusan Sati uku muna tare da shi mun saba da juna a kusa da junan mu.
Bani da yadda zan yi ni na had'a masa kayansa daman ya wanke sai dai ba guga
Sai da Safe ya tafi bayan ya bani 5k nace masa akwai kud'i a Hannuna.
Bai damu ba ya Rike hannuna ya sakamin aciki sannan yayi min kiss a saman goshi.
Ni na rakasa har bakin kofa sannan ya karbi akwatinsa yace na koma daki.
Sai naji kamar zan yi kuka cikin Muryan Shagwaba nace"Yaushe zaka dawo?
Kallona ya ke yi ko Kiftawa ba ya yi, sai gani ya yi na fara hawaye ina Kif kif da ido.
Sai kawai ya sauke akwatin hannunsa ya shigo cikin Dakin.
Bansani ba sai ji kawai nayi ya kama kaina kawai ya had'e bakin mu waje d'aya.
Wlh abun na ransa daman ya na so ya kara Kissing din Hasiya ko zai samu sukunin da ya rasa tun ranar da ya fara jin Damshin bakinta.
Ban hanasa ba sai ma rike hannayensa da na yi ina ba shi Damar haka sosai.
Kissing muka yi har na tsawon mintina goma sannan ya saki bakina, sai na koma na lafe a jikinsa ina maida Numfashi.
Shima rumgumeni ya yi yana fadin"Zan dawo da wuri kin ji ko? In ma na dad'e zamu rika waya ko?
Sai na gyada masa kai, dagoni ya yi ya na sharemin hawaye.
Ina yi masa Bye bye ya na yi min har sai da na ga fitansa daga get sannan na koma na Rufe kofata.
Kan kujera na zauna ina jin wani kewa na Rufeni har miyan bakina na Dangwalo ina d'andana miyan bakinsa tare da jin bugun zuciyata na karuwa daga yanayin da na sani a baya.
*****
Ya na komawa dakinsu ya share ya gyara kafin Tahir ya dawo.
Tahir kuma sai yamma ya shigo garin, Ganin Sadiq sai ya aminta da cewa tun jiya Sadiq din ya dawo kamar yadda yace.
Sadiq na faman tambayan Tahir yaya ya baro su Hajja?
ya yi banza da shi ganin haka yasa sai ya kama kansa.
Sai da Tahir ya yo wanka yazo ya na shiryawa sannan ya kalli Sadiq da ke kwance lokacin ma Tunanin Hasiya ya ke yi.
Kai tsaye yace"Ammh kai dai baka da Kirki mun yi fa mgana da cewa rana d'aya zamu taho."
Sadiq kamar bazai tankasa ba sai chan yace"A jiyan ne na sauya Ra'ayina."
Tahir ya yi tsaki kafin yace"Sai kaje chan kaji da banzan ra'ayin ka."
Sadiq bai ma jinsa hannunsa na saman bakinsa d'ayan hannunsa kuma ya yi matashi dashi sai mirmishi ya ke yi shi kad'ai.
Tahir ya kallesa kafin ya ja wani Dogon Tsaki ya wuce wajen kayansa yana shiryawa sai kunakunai ya ke yi domin bakaramin haushin Sadiq yaji ba.
Tunda ya dawo bai samu waya da Hasiya ba saboda Tahir kuma baya so yasan ya na waya da ita shiyasa sai Ranar litini da yaje wajen aiki ya samu ya kirata suka gaisa yaji lafiyanta.
Sultana ce ke ba shi mamaki yarinyar nan ta maida turo masa sako kamar Ibada Good mrning da Good Night.
Kuma yasan duk sata ake yi ta Turo masa shidai bai taba kiranta ba kuma yana da Dalilin yin haka
Ahalin da ya ke ciki ne neman mafita game da Hasiya baya so kuma Sultana ta shiga Tunaninsa yanzu.
Yana ta nazarin adadin kudin da zai bama Hasiya wanda zai riketa bayan ya rabu da ita.
Yasan ba shi da matsalan kudi Saboda Duk wata Abba na saka mai kudi, sannan Sauran Sisters dinsa ma suna saka masa kudi sannan ga kudin da Federal ke biyansu na Bautar kasa duk da Shigowar Hasiya Rayuwarsa yasa ya kashe kudad'e sosai.
Ya zauna da Tahir ya fad'a masa Hasiya kasuwanci ta ke so.
Tahir ya kallesa kamar sakarai kafin yace"Lalle yarinyar nan bata da Hankali wa zai bata jarin da zata yi wannan kasuwancin?
Sadiq ya Had'e rai kafin yace"Ni zan bata Tahir."
Tahir ya kunshe bakinsa kafin yace"To ai sai ka bata. Ka dai tabbatar bayan ka bata ka Rubuta mata takardan sakinta, domin ko wata daya ne da kwanaki ya ragemana a garin nan."
Sadiq ya kallesa bai ce komai ba ammh sai yaji kamar kwanakin ma suna kara gudu ne, a baya ya fi kowa kosawa da gama Bautar kasarsa ammh yanzu sai yaga kamar Kwanakin na Gudu ne ya manta shekara d'aya yanzu kamar kwana ce.
In zai je duba Hasiya sai dai ya je bayan ya D'au Excuse daga wajen aiki sannan ya ke zuwa ya Dubata.
Wani abu da ya zame ma Sadiq jiki shine tsotsan bakin Hasiya.
In ya kwanta har mafarki ya ke yi duk sai ya kasa sukuni, in ko ya samu yaje sai ya dan tsotsa ko kad'an ne ba da yawa ba.
Ni kuma gabadaya ya sabar min da wannan abun Shikenan nima in bai zo ba na rika shafa bakina kenan ina jin wani kewa har cikin kashin jikina.
In kuma yazo kunya ke sakani ba na zakewa ammh in ya fara sai na bashi had'in kai.
Daga dai kiss baya ko taba kirjinaa sai dai ya Rungumeni kawai.
Da na yi masa mganar naga ya na zuwa ne ko ya dawo garin ne?
Sai yace min suna kawo kaya zariya ne, shiyasa ya ke lekoni saboda ya Damu dani.
Sadiq ba tare da ya farga ba kwanaki suka zo suka yi ta tafiya kamar ruwa, sai gashi ana saura sati daya su kamallah Service dinsu.
Duk sai hankalinsa ya tashi ya kasa sukuni a karkashin ransa kuma sai yake jin wani irin kasalan jiki.
Acikin zuciyarsa kuma ya na jin wani irin nauyi da farko ya kasa gane komai sai daga baya ya Fahimci na kewar HASIYA ne.
Ya riga ya gama Tattara kudin hannunsa da niyar zai bama Hasiya na jarinta da zata fara kasuwanci.
A daran ana gobe zasu je Zonal office nan ciki zaria su karb'i Takardan shaidar kamalla Bautar kasar su sannan daga nan kowa sai ya yi ta kansa.
Shi kuma daman ma'aikatan da ya yi Bautar kasa sun nemi da zasu rike shi a matsayin cikakken ma'aikaci ya ki ce musu komai.
Tahir kuma sai damunsa ya ke da ya saki yarinyar nan?
Yasan rabuwa da Hasiya shine mafitansa shiyasa ya zauna ya yi Tunanin Rubuta mata saki ammh ya kasa ya yaga takarda sama da goma ammh ya kasa iya sakin Hasiya.
Tunani kawai ya ke yi kamar bai yi mata adalci ba tunaninsa in ya Saketa wani hali zata shiga?