← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 75

Sashe 67

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ni ko ba biki ne ya yi biki ba da yasa ban ji kiran wayar Assadiq ba.
Wayar ta na cikin Jaka kuma Adda Fati na bama ajiyar Jakar da Safe kuma basa nan suna makota gidan suke wai aikin abinci.
Ita da Adda Rukayya ni dai nace ba na jin dadin na yi kwanciyata Dakin Zahra'u.
Yaran gidan ma sai da muka zo na san su wlh, da ya ke kuma ba son mutane suke yi ba Daga yan'uwan matar gidan kad'an sai mu Dangin megidan Daga Zariya.
Ita naji ma ana fadin a gidansu take nata taron ita uwar bikin, gidan sai bai wani cika ba sai mutane kad'an masu Shigowa.
Abinci ma a wani waje aka Dafa sai dai aka kawosa a dafe kawai aka fara ci.
Na samu sakewa kad'an Tunda matar gidan ta na da Kirki ita da ya'yanta Yan zuwa Bikin ne marasa Mutumci wato ya'yan su Baba tanko da Baba Saminu daga Zariya.
Ina ga ko ba su so mu zo ba ne bansanin mu su ba, ni dai tunda na samu Zahra'un ta jani Dakinta sai Washegari na fito.
Hajiya Murnajatu sai godiyan kudin da Adda Fati ta bata ta ke yi mana.
Bata gane mu ba sai da Adda Fati ta yi mata bayani sannan ta gane mu.
Shi ko Baba Jibril din ban san ko ya gane mu ba, mun dai gaisheshi da Safe da suka Shigo gidan suna gabda Tafiya Daurin aure.
Angon ma daga nesa na ganshi ni ko a Hanya muka had'u bazan iya ganesa ba.
Su zahara'u sun yi sha'aninsu sun yi gayyar kawayensu ba laifi, sai bayan La'asar Su Baba Jibril suka dawo ni kuma sai a lokacin na yi wanka na Saka Atamfata.
Tunda sai da na jira su Adda Fati suka Dawo kayammu na wajen su.
Su ne ke shiga cikin yan'uwa ni kam sanin bakin fenti na yasa na ke sahale kaina a gefe.
Ina dakin zahara'u in nagaji da kwanciya na mike da ya ke ina al'ada ba na sallah Shiyasa.
Ina ji da yammah ana karadin Saukan Amare daga Gusai ban fito ba.
Sai bayan mangariba Adda Fati ta leko tace nazo muje Za'a raka Amarya gidan ba na son zuwa sai nace su je kawai ba na jin dadi.
Har ga Allah ban so zuwa ba sai da Fathihatu ta shigo Daukan abu ta ganni kwance cikin Fara'a ta min mgana ko lafiya?
Nace mata lafiya lau sai kawai tace na tashi mu karisa gidan Amarya.
Na kasa yi mata musu sai na tashi na saka mayafi, jakata ce har yanzu ta na Hannun Adda Fati na ganta a hannunta sanda tazo min mganar tafiya raka Amarya.
A motarta muka tafi ni da ita gidan duk ya watse sai kalilan duk jam'ar na gidan Amarya.
Ashe ba Nisa tafiya kad'an muka yi sai gamu mun iso gidan a waje ta faka Motar sai a ka kirata a waya, ta tsaya ta na mgana sai tace na Dauki wata karamar kula muje gata nan zuwa.
Sai na yi gaba saboda sha'ani sabon get din gidan ya na Bude ne ina Turawa na shiga.
Haraban gidan akwai haske tar kamar an kuna gen ne ko kuma kila wuta ne domin naga anguwan ko'ina da haske.
Ina shiga gidan na rasa ina zan nufa Tunda Kofar falon da na gani kamar a Rufene kuma ina jin hayaniya daga ciki.

Bansan ta inda Tsohuwar nan ta Bullo ba ganinta kawai na yi a gabana, yadda ta ke dogara sandar hannunta ne yasa na tabbatar bata gani.
Kamar kila Motsi taji sai ta fara fadin"Waye anan ne?
Cikin mirmishi nace"Ni ce iya."
Innani ta yamutsa kafin tace" ni sunana Innani yar nan nace ko cikin yan'uwan mijin ki ke ne ko?
Sai na amsa da Eh da Sauri tace"Taimaka min ki Dubamin gilashina karfen nasara ba Tabbas daga Fitowa ai na sha iskar Ubangiji ya na fuskata ya fad'i daganan ne na nema na rasa."
Da toh na amsa mata ta na nuna min inda tabi da sandarta ni kuma na Duka ina Dubawa sai ga shi na ganshi kusa da kofar falon.
Na dauko mata na goge mata na karisa gabanta na saka mata shi fuskarta ina fadin"Iya ga shi nan na gano miki."
Innani jin gilashi a Fuskarta yasa ta kara gwale ido ta na kallona.
Nima ita na ke kallo abun mamaki Irin kayan da ke jikinta nima shi ne ajikina.
Kafin mu samu Zarafin mgana dagani har Tsohuwar da tace sunanta Innani wata mata ta fito da Sauri.
Ta na Dube Dube ta na ganin mu sai ta Sauke Numfashi.
Da ya ke na juya baya bata fuskata ba sai ta kariso ta na fadin"Saliha ashe Innani na tare da ke? Na tsorata da na Duba ciki ban ganta ba."
Juyowa na yi muka had'o ihu hudu da ita sai da mukaji wani iri.
Kallona ta ke yi nima ina kallonta cikin mamaki.
Innani ce ta tabe baki kafin tace"Wata Salihar? Yaran da tunfa muka zo ban kara ganin su ba, wata yar mutumci ce ta taimakeni kin ji yar nan Allah ya yi albarka."
Ta fad'a ta na Dafa kafad'ata, Umma ta kalleni ta kara kallona nima na kalleta sai kuma na sunkuyar da kaina ina gaisheta ta amsa cikin Sakewa kafin tace"Ayya to mun gode"
Da kai ma amsa mata Hannun Innani ta kama suka wuce ammh ta waiwayi ta kalleni nima kuma ina ta kallonta har suka shige cikin Falon.
Kila ta na mamakin kayan jikina ne, ni kuma Muryanta ne naji ta yi kama da na wacce na sani.
Sannan kamminta ne ya yi kama da na wanda na sani Ammh na kasa tuna komai.
Sai kawai na Cigaba da Tsayuwa ina jiran Wacce muka zo tare.
bazan iya Shiga gidan ni kad'ai ba Tunda bansan kowa ba.

Mata muntashi tsaye mu yaki infection (sanyi) Wani ciwone Mai nacin gaske Wanda idan kikayi wasa xaihanaki jindadin Aure Sannan maganin shi saikin daure da nacin shanshi Akai Akai toh kufito🤌🏽 KUSAI TSIMIN TABAJE DOMIN MUNA DAFASHINE DA INGANTATTUN SAIWOYI MASU AMFANI AJIKI DAKUMA LAFIYA, CIWON SANYI, SANYIN MARA, BASIR DASAURANSU INSHA ALLAH DUK WANI CIWO INDAE NA SANYINE ZAIZO KARSHE DA YARDAN ALLAH KIDAE KIDAURE KIDUNGA SIYAN TABAJE KIJEFI TSUNSTU GOMA DA DUTSE DAYA💃💃💃
Akwai infection Wanda yake nuna kanshi Akwai Kuma kurman infection Wanda baxaki San kinada shiba Amma yanacan yana Miki illa domin duk kyan Kayan mata baxakiga aikinsu ajikinki ba ko Kuma sumiki aiki bayanda akaso ba
Anason duk bayan wata 1 mace tasha maganin infection sbd samun lafiyar jikinta
Alamomin shi sune
Fitar farin ruwa
Kaikayin gaba/ko kuraje
Jin zafi yayin sex
Daukewar ni'ima
Daukewar sha'awa dadai sauran su
Kafin kifara Shan maganin mata yakamata ki fara Shan maganin infection
Ina Yan mata Budurwa kema Yakamata kidinga Shan maganin infection Dan kariya da lfy ki karsai kinyi Aure infection ya Riga yamiki illa Baki saniba Allah y bamu lfy y karemu Ameen 🙏

*Janafty*
*TMWBK2019*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641

https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE

Na dad'e tsaye bayan shigewar matar nan da tsohuwar da ta kira kanta da Innani ciki kafin Fathiha ta shigo.
Ganina tsaye yasa ta rike baki ta na fadin"Kina tsaye? Me yasa baki shiga ba?
Mirmishi na yi mata ammh ban yi magana ba sai ta yi gaba ta na fad'in"Muje."

Ni kuma jin haka sai na bi bayanta har zuwa cikin kayattacen Falon Amarya da yaji komai na kayan more rayuwa masu kyau da inganci.
Sai dai me? A falon ma duk da akwai wasu daga cikin yan'uwan uwar ango akwai na Amarya aciki ma su sanye da irin kayana.
Mamaki sai ya kara kamani suna kallona nima kamar yadda na ke kallon su, cikin mamaki Sa'adatu da ke falon ta kalleni ta na fadin"Laa Sadiya ga irin ankon mu?
Ta fad'a ta nuna ma wata da ke kusa da ita wacce ke latsa wayarta.
A tare suka kara kallona kafin ma na yi mgana Fathihatu ta kalli kayan jikina kafin tace"Laa iri d'aya kuwa ni ban lura ba."
Sadiya tace"Yar'uwan ku ce?
Fathihatu ta gyad'a ta na fadin"She is a Cousin."
Sannu dayar tace min ta farkon kenan Sadiya nima na amsa mata da Sannu, dayar wayarta ta cigaba da latsawa.
Wurga ido na fara yi ina neman su Adda ban gansu a falo ba sai na Fara Tunanin ko sun koma gida ne.
Sai wata cikin dangin Ango tace sauran suna d'ayan dakin suna ta sallah.
Sai Fathihatu ta jani zuwa Dakin da Amarya ta ke ciki tunda ga Hayaniya nan muna jiyowa.
Ni ban shigaba daga kofar dakin na mika mata kular hannuna nace zan fara shiga wajen su Adda Fati sai ba ta musa ba ta karba ta bude kofa ta shige ciki ni kuma sai na shiga Bedroom din da ke kallonsa.
Chapter 67 · 0% Book details