← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 75

Sashe 12

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe baki ta yi kamar yadda nima na washe mata sannu da gida ta min kafin tace in ba damuwa na san musu butoci suna so su yi sallah.
Ganin suna da yawa yasa na dauko musu botiki karami na zubo musu a ruwa aciki na bata buta guda biyu ta na min godiya.
Chan kuma sai gata ta dawo min da botikina da butocina ta kara cewa na san mu su ruwan sha.
Kitchen na shiga na samu katon jug dina na zuba ruwaan tunda nima shi na ke sha ba ni da pure water duk da akwai dubu biyun da ya bar mun ammh yaron ma da zan aika babban aiki ne.
Na cika musu shi na had'a musu da kofunansa guda hud'u na kawo mata ta karb'a ta na fad'in sun gode.
Cikin yanayina nace"Ku yi hakuri ba ni da pure water"
Sai ta yi dariya kafin tace"Bakomai kin ji"
Har ta juya ina shirin Rufe kofata ta juyo ta na fadin"Nace ki fito mana ki zo ki ga yanayin jeren namu kinsan ku ne yaran zamani sai mu gama kokarin mu ku ce bamu yi daidai ba."
Kamar tasan nagaji da zama ni kada'i da Sauri na fito ina amsa mata da toh.
Akwai key din kofar ta baya shi na cire na Rufe kofar na bi bayanta sai min hira ta ke yi.
Muna shiga sauran matan suka bi mu da kallo ni kuma na gaishe su suka amsa cikin sakewa itace naji ta na musu bayanin anan gidan na ke.
Gani mai hankali Ummi zataji dadin zama dani.
Ina jinsu suna ta min godiyan ruwa, falon ga kaya nan zube ina ga ciki ne kanfintocin ke had'a gadon wata mata na gani ta na salla a kasa acikin raina sai naji ban kyauta ba meyasa ban basu Darduma ba?
Gefe na koma na tsaya ina kallon abubuwan da su ke yi, ban san me ya tsaidani ba ammh naji gwara na zauna cikin mutane da na koma daki ni kad'ai kamar wata mayya.
Gani na tsaye yasa matar nan tajani kitchen wai nazo na rika nuna musu yadda zasu jera kayan kitchen d'in, aiko zuwa na ya yi amfani da sun mata barna duk sun fara yaaga mata wasu kwalayen kayan sai da nace musu su bar su a kwalayensu in ba haka ba in ta jima ba ta yi amfani da shi ba za su lalace.
Muna kitchen din suna ta aiki nima ina taya su babu bambamcin da Falt dina komai iri daya ne har girman ni da ya ke ba ni da wasu kaya yasa dakin nawa bai cika ba ammh ita ko da ta ke da kaya da yawa waje ya cika Damkam.
Har sun gama gyara ciki sun fito falo bamu sani ba, sai da wani cikin samarin nan ma su kwashe kaya ya shigo ya na fad'in"Wacece Hasiya a nan?
Mu muna kitchen shiyasa ba mu ji ba su kuma ba su dauka ni ce Hasiyan ba sai suka ce ba Hasiya anan wajen.
Sai da ya fita ya kara dawowa yace matar dakin nan dake kusa da nan ake tambaya mijinta na jiranta.
Muna cikin aiki wata yar matashiya ta leko ta na kiran sunana.
Cikin mamaki na juya ina amswa da Sauri tace"Au daman ke ce Hasiyan?
Sai na gyad'a mata kai.
Da sauri tace"To ki je ga mijin ki chan ya dawo ya na jiran ki."
Sai naji abun wani barambarakwai namiji da suna Hajara.
Idanuwana na zuba mata har ta fice daga kitchen sai naji kamar ban ji daidai ba.
Hajiya Zainab ce tace"To maza mana kije kada ya gaji da jira ransa ya baci."
Jiki na a sanyaye na yi mata dariya na wuce suka bi ni da kallo.
Ban dauka da gaske ba ne sai da na fita na ganshi tsaye a kofar dakina ya jingina da kofar, sanye ya ke cikin kananun kaya riga da wando.
Hannunsa daya akwai Ledan d'ayan kuma ya tusa cikin Aljuhun wandonsa.
Hasken gen din kusa damu ya haske Fuskarsa domin ni dai inaga tunda nazo gidan nan sai cikin dare suke bamu wuta kila ta lalace ne ko suna gyara.
Kafafuwana kamar baza su daukeni ba haka nake takawa zuwa gareshi.
Tunda na fito yasan nice saboda yanayin jikina da ya gani.
Idanuwansa na kaina har na kariso gabansa cikin sanyin muryata nace"Sannu da zuwa."
Bai amsani ba illah cigaba da kallon Fuskata da ya yi cikin d'an hasken da ke wajen.
Ni kuma na sadda kaina kasa ina faman tura hannuna cikin Hijabin jikina.
Ajiyar rai ya sauke ganin ina Lafiya domin har ga Allah tunda ya tafi baya cikin natsuwarsa.
In ya ce zai zo ya dubani Tahir ya hanashi ya fara fad'in hakan ba shi cikin Tsarin su ba shi kuma Tsoro ya ke ji kada wani abu ya samu yar mutane ba shi da ta cewa.
In kuma yace Tahir din yazo su je sai yace bazai je ba shima kuma ba inda zai je.
Yau din ma Tahir din bai sani ba ya Sulale ya taho saboda ya gaza samun cikakiyar natsuwa.
Numfashi ya sauke kafin yace"A tsaye zamu gaisa?
Jin haka yasa da sauri na fito da hannu na mai dauke da key din dakin ya matsa baya na bude dakin hannuna na rawa.
Ni ce a gaba sannan ya bi yo bayana dakin da Dubu ban kunna Fitila ba.
Shi ya kunna hasken wayarsa sannan na samu damar ganin fitilan saman kujera na karisa na kunna haske ya cika Dakin dayake tunda na Fahimci basa barin wuta da rana sai na ke sokata a chaji kafin na kwanta zuwa Safe ta cika da Chaji.
Bai jira ni na zauna ba ya samu waje ya na kallona Lokaci daya ya na fad'in"Zauna mana."
Ba musu na zauna kujeran da ke yamma da shi.
Ledan hannunsa ya sauke a gabansa kafin yace"Kina lafiya ko?
Sai na kasa amsa masa da baki kai kawai na gyad'a masa.
Cikin natsuwarsa yace"Kin tabbata?
Sai na dago ina kallonsa kafin na yi mirmishin yake ban yi mgana.
Shi kuma sai ya yi tsam saboda Sai yaga kamar wani kallo na yi masa na irin baka kyautamin ba.
Baya so ma ya na kallona Tausayi na ke ba shi mganar gaskiya.
Shuru na wani lokaci kafin yace"Naga mutane a gidan ne sosai."
Cikin muryata nace"Eh wacce zata tare a dakin chan suka kawo kayan daki"
Jinjina kai ya yi kafin yace"Good akallah zaki samu yar'uwan zama"
Sai na gyad'a masa kai alamun hakane.
Daganan muka yi shuru har na tsawon mintina goma ba wanda ya kara mgana.
Wayarsa ya duba yaga kafin ya Dago ya na fadin"Lokacin sallar isha'i ya yi zan tafi ina so na tsaya a masallaci na yi sallah."
Da idanuwana da suka cika da Ruwa na kallesa kafin na samu zarafin magana ya mike tsaye ya na fadin"Ba abunda ki ke da bukata in zan dawo sai na taho miki da shi?
Sai na samu kaina da fad'in"Bakomai."
Kudi ya ciro cikin Aljihunsa yazo har gabana ya ijiyemin tare da ledan nan ya na fad'in"Ki rike a hannun ki kin ji ko?
Bansa ta ina raunin ya nuna kansa ba sai ji nayi hawaye na bin fuskata.
Shima hawayen ya gani ya sa ya dakata da mgana jikinsa a matukar sanyaye yace"Hasiya Lafiya? Me ya faru?
Da sauri na saka hannu na share hawaaye na kafin na kira sunansa.

"ASSADIQ.."
Chapter 12 · 0% Book details