← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 75

Sashe 42

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sai ruwan gora da bakin lemu katan daya sai Fanta ya na Dauka zuwa Kitchen. Da sauri na Fito bai sani ba ya Dauki Katan din bakin lemun zuwa Kitchen ni kuma sai na Dauki na Fatam na bi bayansa. Ya fito kenan muka kusa cin karo, da Sauri muka kalli juna kafin ya yi mgana na rigasa da cewa"Sannu da zuwa." Bai amsa ba abun Hannuna ya karb'a Lokaci daya ya na fadin"Yarinyar nan na Lura baki jin mgana ko? Sum sum na wuce zuwa Falo na samu kujera na zauna. Shima ya kai sannan ya fito da bakin lemu ya zo ya ijiye nima ya Daukomin Fanta ya bani na karb'a. Cikin dakin ya koma sai gashi ya Fito da karamar Na'urarsa ya koma ya zauna ya kunnata. Ya na aikinsa lokaci bayan Lokaci ya na shan lemunsa. Sannan sai ya kalleni ya kauda kai har dai yaga ban sha lemun ba ya min mgana sai na Dauka ammh na kasa Budewa duk ya na kallona. Bansan ya taso ba sai ganinsa nayi a gabana kawai ya mika Dogon hannunsa ya karb'a ya bud'emin sannan ya maidamin ya na fad'in"In nace baki da karfi sai ki ga kamar ban fad'i gaskiya ba." Baki na Bude kafin nace"Laa..! Bai barni na karisa ba ya saka hannu ya rike hannuna ya Tura lemun a bakina sai da na kurba sannan ya saki hannuna ya koma ya zauna da wani kallo na bisa, shi kuma bai kara kallona ba ya cigaba da abunda ya ke yi. Muna nan zaune yana aikinsa ni kuma ina faman kallonsa, Fanta kad'an na sha Saboda gas kada ya rika tasomin bayan na kwanta, Shi kuma Tas ya shanye coke dinsa sannan ina gani aka kira wayarsa kamar bazai Dauka ba sai kuma ya tashi ya na kallona ta gefen ido ni kuma sai nayi kamar ban gansa ba. Fita ya yi waje inaga ya yi wayarsa sannan ya dawo ya cigaba da abunda ya ke yi ganin yamma na yi ne yasa na tambayesa me zamu dafa? Ya yi shuru sai kuma chan yace kada na Dafa komai tukunnah. Bamu muka tashi daga falon nan ba sai da aka kira mangariba ni ce ma da nagaji da zaman na d'an kishigid'a. Sai da ya juyo ya ganni ne yace min na tashi na zauna an kusa kiran mangariba. Shi fita ya yi masallaci ni kuma sai nayi nawa a gida, bai dawo gidan ba sai bayan isha'i da ya dawo wanka ya Sakeni ya sauya kaya zuwa wani Saukakken yadi ni kuma yace na yi wanka zamu fita ne. Ban musa ba na shiga na yi wanka na sauya kaya zuwa wanda na dinka da Auran mu, na saka farin Hijabina shi ya Kulle Dakin muka fita. Bai gayamin ina zamu ba sai da muka hau adaidaita muka isa sai naga An Rubuta Usmaniya Restaurant. Karo na Farko da na Taba zuwa Restaurant a rayuwata kenan Dare ne ammh kamar rana mutane sai harkokinsu suke yi. Ga masu zuwa cin abinci nan birjit wasu irin mu wasu kuma su kad'ai. Zabin abunda zan ci ya bani sai na rasa me zan ci sai nace a bani White Rice da Miya. Shi kuma sai yaci chips da Maltina kawai ya ce ni bazan ci chips din ba? Sai na girgiza masa kai. Bai kara mgana ba sai ya yi mgana aka kawomin Ferfesun kaza sai da aka kawo naji kunya tunda muna cikin wani babban Falo ne ga mutane suma duk a zaune sai dai kowa ya na Harkan gabansa ne shiyasa nace masa bazan ci ba. Harara ya sakarmin kafin yace"Duka zaki cinye tunda ba asaran kudina zan yi ba." Ba wasa a mganarsa yasa na fara ci kad'an kadan. Lemun Holladian ya ce a kawomin tunda yaga ban cika shan masu gas din nan ba. Karshenta dai sai da kowa ya watse ya barmu ina ta cin abinci sannu sannu. Ga shi cikina ya cika na kasa cinye Ferfesun kazan shi kuma tuni ya gama yana gefe ya yi fuska a bunsa. Ganin haka yasa na kira sunansa"Assadiq." Juyowa ya yi ya na kallona bai amsa ba ganin haka yasa nace"Na koshi wlh." Zai yi mgana saurin na kara cewa"Wlh kalli cikina". Gani ya yi kamar ina kokarin Bud'e masa cikin yasa da Sauri ya mike yace mu tafi. Muna tare da shi ya ciro walet dinsa ya ba su wani kati kamar dai Atm ne suka cire kudinsu. Mun fito daga wajen kenan yana tafiya ina gefensa sai faman kalle kalle na ke yi ina kara kallon wajen chan garin kallon na ci Tuntube na kusa fad'uwa sai da ya tareni. Cikin Tsareni da ido yace"Me ki ke kallo haka? Cikin Sauri nace"Assadiq ina ne nan? Sai da ya sakeni sannan ya rikemin hannu muna tafiya zuwa bakin Titi yace"Kina jin ana cewa kango? Sai na gyad'a masa kai shi kuma ya Cigaba da fadin"Nan ne kango" Kara bin wajen na yi da kallo ina fadin"Wajen da na kyau." Bai yi mgana ba sai ma kokarin tsaida mana da abun hawa da ya ke yi. Mun koma gida tara da wani abu na dare gashi na koshi da yawa shiyasa muna komawa na yi shirin kwanciya shi kuma sai da ya kara yin wanka ni har mamakinsa na ke yi baya gajiya da wanka ne?
Chapter 42 · 0% Book details