Sashe 17
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba jimawa ta fara girki ranar ma ni na san mata kayan miya tunda na nika shi na tafasa shi ya ma kusa karewa, na gayamata ta saka a kawo mata daga gida nan ba'a samun kayan miya to ina ma d'an aiken? Ko almajirai ni dai ban taba gani ba ko suna shigowa anguwan basa zuwa gidanmu.
Ni na rika damun Adda Fati da waya ina mata shagwaban bata kara zuwa Dubani ba sai ga shi ta zo ita da yaranta gabadaya da Habiba suka min yini ita tazo min da kayan miya mai yawa har na Diban ma Ummi tunda itama da aka kawomata kayan miya da kayan lambu ta dibar min har kofar daki na tazo ta bugamin na bud'e ta bani na karb'a ina mata Godiya.
Sannan na rakasu su Adda Fati Dakinta suka gaisa ta tarbesu hannu bibbiyu ta ba su ruwa da lemu ta na basu hakuri cincin ya kare naace kada ta damu na wajen nawa da ban cinye ba na basu sauran sun ci.
Ko da yaushe na shiga dakin Ummi sai naji kamar nawa ne Saboda ya Tsaru sannan koda yaushe cikin kamshin Turaren wuta.
Sannan Ummi akwai Daukan wanka da gayu ni dai ta na Burgeni sosai.
Da zamu tafi ta bama Hanif da Hanifa Dari biyu ta kuma rakomu har barandar Dakinta.
Da muka koma Dakina Adda ta yi ta yabon Hallayar Ummi ta na min Fad'an mu zauna lafiya da Amana.
Shinkafa da miya na yi mana muka ci muka sha sai bayan la'asar suka yi shirin tafiya.
Da Adda Fati tace ina Abubakar sai nayi mata karyan ya na wajen aikinsa.
Sai dai wani abu daya ya bata mamaki ita da Habiba suka kwashe kayan akwatina suka jeramin acikin wadrope ammh ko abunda ba'a so ba su gani na Miji na ba.
Da Adda ta tambayeni sai na rasa me zan ce mata sai karyan ya kai wanki ta fad'omin nace mata da Safe ya kwashe ya kai wanki.
Adda Fati har ta na ce min me yasa ni bazan kwashe na wanke masa ba.
Nace shi yace ma barshi zai rika kaiwa ana wanke masa.
Araina ko nace ina na ganshi ma? Na dai wanke sauran kayana da suka yi datti Tunda ya siyamin sabulun wanka da na wanki tun washegarin ranar da na tare.
Tunda ya zo ya kawomin wayar nan bai kara zuwa ba, kuma a Waya bai wuce sau biyu ya kirani ba.
Shima muna gaisawa yaji lafiyata sai yace min baya nan sun yi tafiya ne ammh in ya dawo zai zo.
Ya tambayeni ba ni da wata damuwa nace masa Eh! Tunda ga ranar bai kara kirana ba nima ban taba gigin kiransa ba na cigaba da Lallaba Rayuwata a yadda kaddara ta zab'wmin.
Jin dad'ina da Tarewar Umma in muka gama aikinmu zata zo dakina ko naje dakinta mu sha Hira da ya ke ta na da Surutu shiyasa duk wani Labarin da ya Danganceta ta na fad'amin da na Mijinta sannan in muka yi girki muna zuba ma junan mu.
Ban tab'a bata labarin Mijina ko yanayin Rayuwata ta baya ba.
Abu d'aya na taba gayamata da ta taba cemin hala ni buzuwa ce? Nace mata a'a Amma bafullatana ce Babanmu kuma Bazazzagi ne.
A lokacin Dariya ta yi ta na fadin"Shiyasa sunan ki ya zama Hasiya kenan? Daman sunan Fulani ne."
Ni kuma sai nace mata"Ba sunan Fulani ba ne sunan kanwar babanmu mai rasuwa na ci Hasiya."
Daganan kuma sai ranar kawai tazo dakina mu yi hira tace min"bata taba ganin mijina ba ko matafiyi ne?
Sai na samu kaina da ce mata Eh Saboda bani da mafita bayan wannan bata san komai a kaina ba.
Ummi ta iya girken girken zamani Sosai ni kuma na fi iya na gargajiya.
Tunda na saka Adda Fati zuwanta ta kawomin garin Damwake tunda na yi Ummi taci tace mijinta na son Damwake zan koya mata.
Nace mata me zai hana? Shikenan sai muka had'a kanmu ni da Ummi in ta na girki na kan shiga in gani sai dai ko in mijinta ya na nan in baya nan tare mu ke yi ni kuma daman mijina baya nan ta kan kai dare a dakina sai Mijinta mai suna Muhammadu ya dawo sannan ta ke min sallama ta koma Dakinta.
Bani da wata damuwa Rayuwa daidai misali mai sauki ni ke gudanarwa.
Muna waya da Amma kullum tunda kudin da ya sakamin a wayar sun kai Dubu uku har lokacin ba su kare ba.
Ummi kuma ta na da Sati biyu tace min zata koma aiki Tunda ta na koyarwa duk sai naji ban ji dadi ba Tunda mun fara sabawa.
Sai dai ba ni da yadda zan yi tunda Saboda ni bazata fasa zuwa aikinta ba.
******
*KADUNA.*
_Area: Malali_
8:35pm.
Zaune ya ke a falon gidansa mai cike da kayan alatu na more Rayuwa.
Wata takarda ne a hannunsa ya na Dubawa.
sanye ya ke da Riga da wando farare rigar bata da Hannu kamar na shan iska ne acikin gida.
Babban mutum ne domin zai iya kaiwa kimanin Shekaru Hamsin da Takwas zuwa da Tara a duniya.
Alhaji Jibril kenan ma'aikaci ne a Hukumar Nepa ta jakar kaduna wanda ya fi shekaru ashirin yana aiki a wajen.
D'aya daga cikin ya'yansa ce ta yi sallama a kofar falon na shi ya amsa mata Lokaci daya ya na bata izinin Shigowa.
Wata gajeriyar matashiyar Budurwa ta shigo wankan tarwada ta na sanye da Doguwar riga baka ta yane jikinta da bakin mayafi Dauke da faranti da nug a saman ya na Tiririn zafin Ruwan lipton din da ke ciki.
Gabanta ta karisa ta ja karamin Tebur kusa da shi ta Dora a saman wajen.
Sannan ta duka ta na fadin"Barka da Hutawa Baba."
Cikin mirmishi ya na kallonta ya amsa mata da cewa"Yauwa sannu da kokari Zahra'u yar Baba."
Kanta na kasa ta murmusa shi kuma sai ya ijiye takardan Hannunsa ya sunkuya ya Dauki mug din ya dan kurba sau biyu, kafin ya sake Dagowa ya na kallonta cikin jin dadi yace"Allah ya yi miki albarka Zahra'u."
Ta amsa da Ameen Ameen Baba.
Mikewa ta yi zata fice bayan ta yi masa sallama saboda Tsarinsa in ya na cikin Falonsa ya na Hutawa baya bukatar ganin kowa ko da kuwa Uwar ta su ce.
Zahra'u ce kad'ai ta kan shiga Saboda ita ke hada masa Tea din da ya kan sha in ya na Hutawa kafin ya shiga barci.
Kiran sunanta ya yi da"Zahra'u."
Ta amsa ta na juyowa da sauri yace"Mubarak ya shigo kuwa?
Girgizamai kai ta yi kafin tace"A'a Baba ammh ina jin duk inda ya ke yanzu ya na hanyar gida."
Kai ya jinjina kafin ya yi mata alama da Hannu da ta tafi shikenan.
Har ta kule ma ganinsa ya na binta da kallo.
Kiran wayarsa ya katse masa tunanin da ya so ya fad'a.
Ya na ganin mai kiran jikinsa na rawa ya Dauka ya na faman washe baki.
Sun jima suna mgana kafin su yi sallama ya sauke wayar ya na kurama zanen kwalliyar cafet din dakin kallo.
Wani tunani daki daki na shiga kansa
Ya fara kasuwancin Shigo da gwala gwalai tun shekaru biyar da suka gabata kuma ya tara abunda bai Tara ba Tun fara aikin gwammatin sa.
Bai san Alhaji Sulaiman Shinkafi ba sai ta sanadin wani abokinsa Alhaji Sheshe shi kuma Alhaji Sheshe sun fito daga mahaifa d'aya ne da Alhaji Sulaiman Wato garin Shinkafi.
Ya san ya na da sha'awar kasuwanci da zai rika kawo masa manyan kudad'e saboda ya raina matsayinsa a yanzu sai ko Alhaji Sheshe da ya kasance abokinsa ne shi ya had'a shi da Alhaji Sulaiman har ya Bude masa ido a kan kasuwancin Shigowa da gwala gwalai.
Tsawon shekaru biyar din nan suna Huld'ar arziki, Bai taba haduwa da iyalan Alhaji Sulaiman ba shima bai taba had'uwa da na shi iyalan ba.
Sai dai yasan wasu mutane Biyu masu matukar Muhimmamci a rayuwar Alhaji Sulaiman.
"MAGAJIN GIDA.."
"INNANI.*