← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 75

Sashe 55

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na dad'e da Lura da Assadiq ba shi da walwala acikin kwanakin nan, Saboda ya rage hira da bani Labarai sannan wasu abubuwan da muke kafin mu kwanta da Daddare irin su kallo ko fita yawo duk ya daina sannan Rikenin da ya ke yi a jikinsa shima ya daina ballatana wasannin da ya sabar min kamar dai ya na jan baya dani ne. Kuma na tambayesa ko wani abu na yi masa? sai yace bakomai gajiyan aiki ne kawai. Yau jumma'a ne da La'asar ya ke dawowa daga wajen aikinsa, tun bayan da na idar da sallah na fito Falon ina Dakon jiransa kamar yadda na Saba na tuna da Safe kafin ya fita yace na shirya in ya dawo zamu fita ina ta Murna a zatona wajen cin abinci zamu je ko kuna wayon zaga garin da ya saba fita dani. Sanye na ke da Atamfa Riga da sikat sai na Daura saukakken Dankwalina hoda na shafa da man baki, da wuri na gama abinci Farar Shinkafa da wake da Miya Tunda ina da kayan miya satin da ya wuce mun je kasuwa mun yo Cafane mai yawa. Ina jin an fara knookig din kofata na Mike da Sauri Farinciki ya cika zuciyata sanin da na yi Assadiq ne sai dai ina zuwa na bude sai da na Rage Fara'ata ganin ba wanda na yi tunanin gani ba ne. Maman Sulaihat ce matar da ta tare a falt din kusa da na Fadila. Yake na yi mata bata ma jira mun gaisa ba ta tureni kad'an ta shigo Cikin Dakin ta na fadin"Ina ce dai megidan bai dawo ba ko? Sai da na Rufe kofar sannan na biyo bayanta ina Fad'in"Bai dawo ba Mama." Saboda Mama na ke kiranta Tunda ta Haifeni ya'ya gareta zaka zaka zaka mata da maza, biyu mata biyu sun yi aure, sannan ta na da budurwa yanzu a gabanta da balaggagen Namiji. Ko da nazo har ta samu waje ta zauna ta yi rashe raahe ta na faman washemin Fararan hakoranta masu Dauke da hakorin makkanta ya na tashin kyalli. Kujeran da ke fuskantarta na samu na zauna ina gaisheta ta amsa cikin Fara'arta, ni har mamaki na ke yi yadda ta ke son shigemin Alhalin nasan su Fadila sun gayamata komai game dani Tunda tun bayan tarewarta suna hulda da ita, ita ma d'in ta na Huld'a da su. Abunda na lura da matar bata san ta girma ba, ba ruwanta da shigema yara sa'anin ya'yanta, sannan ga surutu haka zata zo ta yi ta min surutu ta na dukan ruwan cikina kaza an yi kaza ni dai ban taba bata Fuska ba. Sau d'aya na taba shiga Dakinta itama matsamin tayi sai na shiga na Duba kaya bayan ta je kano ta dawo, da yake babbar yar kasuwa ne babu abunda bata siyarwa kama daga Atamfa leshi, materila, Dogayen Riguna na Hajiya Maryam's Eygptian Abaya +201123302418 Saboda ingancin su yasa ta ke sara a wajenta, ga takalma, zannuwan gado komai da kuka sani ba abunda bata siyarwa. Babbar yar kasuwa ce sosai to ta tab'amin matsamin na Shiga naga kayan na saka albarka Tundaga Lokacin ta cigaba da matsamin da cewa ban yi ma megidana tallah ba ne a yi mata ciniki. Yanzu ma bayan shigowarta mganar ta faramin cikin mirmishi nace"na gaya masa yace ba shi da kudi ammh in ya samu zaki jimu." Cikin yar dariyanta tace"Ai bakomai wlh waye baisan yadda Rayuwar nan ta yi Tsada ba yar nan? Ai mazaje na kokari wlh Allah dai ya saka musu da Hairan." Na amsa mata da Ameen hankalina na kan agogon wayata naga har Biyar Saura Assadiq bai dawo ba. Sama sama naji ta na fadin"Wai a ina mijin naki ya ke aiki ne? Naga da Sassafe ya kan fita? Kallonta na yi cikin mamaki kafin nace"Bansani ba." Cikin mamaki tace"Baki sani ba fa kika ce? Cikin son kauda zencen nace"Eh mana Tunda ban taba zuwa ba, na dai san yana aiki da wani kamfani ne." Jin haka yasa sai ta yi shuru ganin yadda na Had'e fuskata. Sai ta basar cikin tafa Hannu ta fara mgana da cewa"Ke yar nan na tab'a ki da Alheri sai naji wani Labari a bakin makotan zaman ki? Cikin mamaki na kalleta kafin nace"Wani Labari? Ai sai ta gyara zama kafin tace"Fadila da Ummi suka sameni har daki suna gayamin wai na kiyaye ki, kina da Farar kafa, kaza da kaza maganganu dai kala kala wai har suna fadin kin yi aure aure kina talauta mazan da kika aura har fa Wanchan yar fara ta na ce min na yi a sannu kada na Rabeki ki yi sanadiyar karayan arzikiina." Har ta gama mgana ina kallonta Daman ai nasan za'a rina sai naji raina bai baci ba. Cikin Sanyin Murya nace"Ai gaskiya suka fad'a miki" Sai ta wani tabe baki kafin tace"Wani gaskiyan, tuni na warware su dukkansu nace ni ba'a haka dani, kin gani nan wlh nasan Allah kuma ina da Ikilasi na kuma san Tauhidi na kuma san Allah ke yi ba wani ba tuni na zagesu na Fattake su yi ni har za su nuna min wannan mganar? Ni da kanwar uwata ta haifi yarinya sak irin ki itama duk wanda ta aura sai bala'ai su rika fad'a musu auranta Biyar wannan na Shiddan bai dad'e ba shima hukumar Costume ta kame kayan mijin, kuma wajen cucukun Fitowa da kayan sai dai komai na shi ya kare karkenta dai kannensa suka mata Duka suka saka ya saketa da cewar itace sanadin Faruwar haka jama'a ina zamu kai kan mu a wannan Rayuwar sam ba Allah a ran mu? Ta fad'a ta na wani rike Hab'a irin abun ya Dameta. Sai na kasa mgana a raina ina fad'in daman akwai mata ma su ire iren kaddara na? Kafin ma na tambayeta ta fara bani Labarin komai tundaga Tushe sai ga shi ina sharan kwallar Tausayin yarinyar nan sai naji ashe ni nawa mai Sauki ne, ta na fad'amin duk inda yarinyar nan ta zauna na Sati daya sai anga bala'i da Iftila'i. Ni ina ganin kaina ashe akwai wasu wad'anda suke Fuskarta mummunar Rayuwar da ta fi nawa, ashe ashe ni yar aljanna ce. Saboda yadda Hankalin mu ya tafi yasa bamu ji buga kofar ba sai da naji kiran wayata dake gefe. Da Sauri na Duba sai naga Assadiq ne ina rawan jiki na Daga. Cikin Dakushewar Murya yace"Ki na ina ne? Ina buga kofa baki nan ne? Da Sauri na mike ina Fad'in"Ina nan mana ban ji ba ne." Ganin na Nufi kofa yasa ta mike ta na fadin"Na shiga uku ba dai megidan ne ya dawo ba ko? Kai Tsaye nace mata shine ya dawo. Sai ta mike tana gyare gyaren mayafi ta na fad'in"An yi abun kunya ke kuma ba sai ki fad'amin ya na hanya ba." Ni dai bam kara kulata ba na nufi kofa na Bude ya na tsaye rataye jakarsa sai Wata Leda dake hannunsa. Ina kauce ma kallonsa na mika hannu zan karbi' ledan hannunsa ina Fadin"Sannu da zuwa." Hanani Ledan ya yi ya maida ledan bayansa ya na kallon idanuwana. Cikin mamaki yace"Me ya faru? Naga idanuwan ki sun sauya ne, ko kuka yi ne? Kafin na samu zarafin mgana Sai ga Maman Sulaihat ta na yar dariya yace"Sannu da zuwa." A dakune ya amsa mata ya na kallona cikin mamaki. Da Sauri nace"Ta shigo mu gaisa ne." sai ya matsa ya bata hanya ta fita ta na cemin sai an juma. Sai da ta fita sannan shima ya shigo ni kuma na kulle kofar na bi bayansa. Ya na Tsaye a tsakiyar falon ina Shigowa ya mikamin ledan hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"Fruit ne ki yanka min" Da Toh na amsa kafin na karb'a, shi kuma sai kawai ya nufi hanyar cikin Dakin ya na kara fad'in"Zan yi wanka." Sai na bi shi da kallo kamar ba Assadiq ba duk ya sauya. Da ya ke sanin yanayinsa in ba da Safe ba bai cika wanka da Ruwan zafi ba. Kitchen na koma ina duba ledar hannuna, Kankana me da Ayaba sai abarba da lemu. Kara wankewa na yi na jera acikin Filet, sannan na had'a masa abincinsa da Ruwan gora, sai bakin Lemu daman shi ya ke sha shiyasa baya bari ya yanke mana. Ko kafin ya fito na had'a masa komai na shimfid'a masa Darduma a falo. Ya na fitowa sanye da Riga da wando saukakku ya zauna na zuba masa abinci bai ce min komai ba ya fara ci. Ina ta kallonsa da mamaki yadda ya kasa yarda mu had'a ido da juna. Sannan yau bai matsamin mu ci abinci tare ba cewa kawai ya yi naci abinci nace masa eh? Daganan bai kara mgana ba. Fruit din me ya Turamin gabana ya na fad'in"Baki ci ba." Cikin yake nace"Ai baka bani ba." Da mamaki ya Dago ya na kallona ni kuma Daman ya sabamin in dai irin su Fruit ne ya na bani a baki.. Ko abinci ne ma in muna ci tare haka zai ta cika Cokali ya na bani a baki. Bansan ko ya gane manufata ba ne yasa ya Dauko kankana ya nufi bakina da shi ni kuma na Bud'e ya sakamin. A haka har muka shanye gabadaya, ni na tattara komai na maida kitchen, ina mamakin me ya samu Asssdiq ne na gansa haka? Kwanukan da muka bata na Tsaya wankewa, da gyaran kitchen din shiyasa na bata lokaci. Ina fitowa falon na gansa kwance kamar yana waya, sai dai ya na ganina ya yi saurin katse wayar ya na lumshe ido kamar mai barci. Sai na nuna kamar ban gani ba , na wucewata ciki, na zauna ina jiran ko zan ji ya kirani kan mganar Fitarmu ammh sai naji Shuru. Na fita falo bansan iyaka ba ammh sai ya nuna kamar ya na barci kuma ina da Tabbacin idanuwansa Biyu. Da nagaji sai kawai na fito na Tsaya a kansa ina fadin"Assadiq mun fasa fitan ne? Shuru ya yi min, sai nayi Tunanin barcin ya ke yi sai na kyaleshi. Ammh ni kaina duk yanayina ba Dadi, Sai mangariba ya tashi ya tafi masallaci kuma bai Dawo ba sai bayan
Chapter 55 · 0% Book details