← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 75

Sashe 43

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A falo ya kwana kamar yadda muka Saba da Safe kuma shi ya fita ya siyo kwai na soya mana sanin bayason karni yasa na saka ma kwan kayan kamshi irin su citta da Tafarnuwa.
Muka sha Tea tunda ya siyo mana Buredi mai taushi.
Da rana kuma yace na yi masa Danwake da salat mai kwai shi na yi mana muka ci muka koshi Tuni na manta da su Ummi ban kara bi ta kansu ba Tunda ba na fita koda yaushe muna cikin Daki tare shima in ya Fita sai dai in za shi masallaci ko zai fita siyan wani abu.
Da daddare kuma Tsire yaje ya siyo mana da Yourghour muka sha muka kwanta da Safe kuma ya je kasuwa ya narko min Cefane wannan karon bai siyo Kifi ba sai nama sai kuma ya Siyo naman kan rago yace na Dafa masa yana so, cikin Lokaci kankani na zage na Dafa masa mai romo da yaji kayan kamshi kuma yaci da yawa tunda ko Taliyar da na Dafa da rana bai samu ci ba da Daddare ma shi na Dumama masa yaci da Burrdi.
Ni daman naman ganda bai Dameni ba ban ci wani da yawa ba, shiyasa ya kalleni yace"Yarinya baki san Dadi ba."
Mirmishi kawai nayi ban yi mgana ba Zama na da Assadiq zama ne na Mutumtu juna yadda ya ke tafiyar dani kamar kanwarsa nima sai na Dauke shi da Daraja sosai.
Koda yaushe muna tare da juna bamu cika Fira ba sai ta kama ammh yana tayani shara ko zuba ruwa banda girki ko wanke wanke domin yace bai iya ba ammh yana wanke bayi sannan in zai yi wanki ya had'a da nawa ya yanke dauraya kawai nake yi masa na Fita waje na shanya.
Ranar ko na fita shanya muka had'u da Ummi ta kalleni nima na kalleta kamar bazan yi mata mgana ba sai kuma na Duba Wani abu da yasa na Juya na yi mata sallama ta amsa a yamutse daganan na koma na cigaba da Shanyar kayan mu ni da shi ta tsaya kam ta na kallona kuma nasan bayan Fadila ta dawo sai ta gayamata.
Suna ganin mijina ammh kuma ba Fuskar da za su san wani abu akanshi kuma Assadiq ya gayamin tare suke sallah da mazajensu Ummi a masallaci anguwan nan.
Ammh iyakarsa da su gaisuwa shikenan.
Tun bayan auran mu sai wannan zuwan nasa suka taba waya da Amma tun bayan tafiyarta.
Sun gaisa sosai yace mata zamu zo mu gaisheta tace mu yi zaman mu.
Adda ce da aka bata su gaisa ta yi masa mganar ko ya sanar da Danginsa game da Hasiya? Sai yace mata Eh sun sani'.
Sai Adda tace"To tunda sun sani yakamata ka Dauketa ka kaita taga Ahalibka suma su ganta"
Sai ya amsa mata da Insha Allahu.
Tun ina saka ran zai ce min zai tafi har na sakankance.
Watarana in bamu jin dafa abinci sai yace na shirya muje mu ci abinci a waje Dalilin Assadiq na san wasu daga cikin Gidajen Abincin garin zariyan da abaya ban san su ba.
Kuma in zaman shurun ya yi mana yawa sai yace nazo mu yi kallo sai ya kunna mana kallo acikin karamar Na'urar computer dinsa ashe akwai kallo aciki.
Ba na Hausa ba ne Fina finan Sai dai akwai fassaran Turanci, shine ya ke min bayanin Abunda suke fad'i in muna kallo duk da Rabi da kwata ba na gane komai.
Ammh kuma ina jin dad'in haka dalilon haka mun samu sakewa da Sabo da juna sosai.

🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure
Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka
*Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃

*Janafty*
*TMWBK2K013*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641
Chapter 43 · 0% Book details