← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 75

Sashe 74

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya so kwarai kudin da zai bama Siya su kai 300k ammh abu ya ci tura Tunda Big sis ta ishesa da kiran ya turo da kudin gyaran jikin Amarya da kudin kwalliya daman bata san yana da Niyar bada wa ba.
Dubu 100k ya Turama Surayya, ita kuma ta cire 30k ta turama Surayya Dee marubuciya mai Saida saiwowin Gudiyo, da ya ke ita Surayyan ta santa tana tsiyan Littafanta har suka Saba sosai ta yi mata ragi sosai ta had'a mata ma su kyau da inganci duk da daman kayanta suna da kyau sosai.
Daga Kano aka saka a mota sai Gusai Surayya ta karba sakon cikin murna nan da nan tabi Tsarin mgangunan suka Fara dura ma Sultana a cewar su sai sun gigita Kanin nasu yaji ya Ciji yatsan tsaikon da ya tsaya Tuntuni bai yi aure ba.
+234 803 277 3332
Sun yi anko, wannan karon Less da Atamfa, da suka damesa da kiran ya Turo kudin ankon Sultana yace ba shi da kudi su a matsayinsu na yayyenta mata su siya mata mana.
Shi kuma Duk Tattalinsa na Siya ne itama ya na so ta siya kaya masu yawa na alfarma a kallah ko da ba su kai na Sultana ba itama dai ta shaida Tunda bai yi mata lefe ba.
A tsarin da ya tsara daman aa satin da Bikinsa ya rage sati daya da Sultana zai je zariya, satin Biki kuma ya je Gusai daman kuma ya Rubuta takardan hutun Sati daya na auransa in ya yi sati Biyu a gusau sai ya koma Abuja ya yi daya sannan yaje Zariya yaga Siya duk da yasan zai mata laifi ammh ba shi da mafita ne.

*******

Shi baisan duk na san bikinsa da Sultana ya matso ba tunda muna mgana da Saliha tace min ta na nan tafe cikin Sati mai shiga in sha Allahu.
Sanda yazo ya na fad'amin zai jima a Gusai  kafin yazo ban nuna masa na Damu ba.
Sai dai na yi matukar mamakin da yace min kudin da ke acct dina 256k na Dauka na siya kayan sawa ya so ya yi min lefe na alfarma ammh kuma bashi da kudi ammh ko yanzu bai cire rai ba a gaba in ya samu zai siyamin duk abunda na ke so.

Sai na fara hawaye shi ko ya Dauka na Kukan Farimciki ne nan kuwa a cikin zuciyata na wani irin kishi ne da Tunanin kudin fad'ar kishiya ya kawomin.
Ina ganin Hoton Sultana a kwanakin nan Tunda Saliha na yawan sakata ta na Tagging da Amaryan Magajin gida, gwara ita yar gatace kowa na santa ni fa bani da kowa a baya sai Allah. Assadiq bani ya ke so ba jikina ya ke so Sultanace abar son sa kuma itace uwar ya'yansa. Ko kuma nace ita ya zab'a ta zama uwar ya'yansa bani ba.
Na yi ta masa godiya ina sharan hawaye, shi kuma sai ya Rumgumeni ya na fadin"Shii ki daina kuka Siya in da ina da shi kasuwar duniya zan kai ki ki dauki duk abunda kike so domin na nuna miki kin chanchanta a wajena kuma matsayin ki ya zarce yadda ki ke Tunani ko hasashe."
Kallonsa na ke idanuwana na tara kwallah kafin nace"Ka tabbata ka na so na Assadiq?
Gyadamin kai ya yi kafin yace"Kina da Shakku me a kan son da na ke yi miki SiyaAssadiq?
Sai na kasa mgana sai kuka, kawai sai na Rumgumesa ina fadin"Ban damu ka so ni ba Assadiq, ammh ina rokon ka ka ji tausayina watarana ka Tsaya a baya na, ka zame min bango abunda zan jingina in ji sanyi a raina."
Cikin wata irin murya yace"in sha Allahu bazan taba barin ki ba, ki saka a ranki ko da kowa zai gujeki ni Assadiq ina tare da ke har Abadan."

Ko da karya ya ke fad'amin sai naji zuciyata na yaudarana da cewa Assadiq na sona ba shi da zabi ne.
Ni da kaina na had'e bakin mu waje d'aya ina Sumbatarsa.
Sannan ni da kaina na gayyacesa kan gadon mu muka gudanar da sunna, sannan ni da kaina na ja ragamar duk abubuwan da suka faru.
Ya yi ta sakamin albarka kamar zai lasheni, kafim ya tafi sai da ya siyamin kayan abinci sannan ya yi min Cefane.
Mganar kaya kuma na shawarcesa da cewa ko na siya wajen Maman Suhailat ne? sai yace kudina ne na yi duk abunda ya kamata.
Jin haka yasa bayan tafiyarsa na Kira Adda Fati na gayamata ita da Ramatu har Amma sai da na kira.
Ita Adda Rukayya tace ne akwai kawarta mai saida kaya zata yi mata mgana, ammh sai Amma tace tunda makociyata na saidawa ba'a haka na yi mata cinikin yafi na kai wajen Tunda an zaune lafiya.

Nima sai na aminta da Shawaran Amma shima da na kirasa na gayamasa abunda Amma tace sai ya yi mirmishi yace"Madallah da Amma Madallah da Uwar da ta haifi Hasiya matar Abubakar Sadiq."
Sai ya bani dariya a kalamansa na san shima ya aminta da na siya Hannun Maman Suhailat.
Haka ko a kayi wajenta na siya, da ya ke ta na kaya ta fito min da su na zaba da takalma, mayafai hijabai, da Tamfiofi da lesuna  sannan sauran kudin kuma na Rage muka shiga kasuwa da Ramatu na siya akwatina Guda Biyu sai Inears, sai Dankunneye jaka Biyu na siya wajen maman sulahait nafi siyan kaya tunda sune na ke da karancin su a hakan ma na godema Allah, tunda Assadiq ya siya min wasu a baya.

Wannan zirga zirgan yasa na manta da Kudurina na zauna na yi Tunanin ya na da kyau na aikata abunda zuciyata ke Umurtana kuwa?.
Sai naga kamar in nayi hakan ban kyauta ba, gwara na Tsaya a iya matsayina kada naje garin neman gira na rasa idanuwana.
Saboda haka yasa na daina Duba Status din Saliha Tunda har kirana ta yi tace min ta zo garin, ta na kara min Tuni tunda nace mata zan zo mata Biki.
Ranar Al'hamis ma ta kara kirana sai kawai nace mata ba na jin dadin jikina zai yi wahala nazo, duk sai bata ji dadi ba ta ce har ta fad'ama sauran Sister's dinta zan zo mata biki.
Kenan har ta ba su labari?
Abunda ban sani ba tuni har sun san ta na zumunci da yar'uwan mijin Salima.
Har ita Saliman ta gayamata ta yi ta mata kwatancena sai tace bata gane ni ba.
Har Safiyar Jumma'a ban bari zuciyata ta Rinjaye ne ba, sai da rana da na yi kiran Assadiq bai Dauka ba, Tuni kishi ya Rufemin ido zuciyata ta bani ya na chan tare da Amaryar so wacce ya ke so.
Kawai sai na kwanta ina ta kuka ni kadai bani da mai lallashina sannan na Bude wayata naga Hotunansu Saliha sun ci gayu daga inaga Abu suka yi ga shi nan duk sun saka kaya iri daya.
Amaryan ta sha kyau har tagaji da kyau kamar ita ta yi kanta.
A raina nace Dole Assadiq ya so Yarinyar nan saboda kyakyawace ajin Farko gata yar yarinya karama.

*****

Ranar Daurin aure.

A garin shinkafi aka Daura auran Abubakar Sadiq da Sultana, Abba ya  ba da auran Sultana Mallam Shitu kuma ya karb'an ma Sadiq.
Daurin auren da ya samu mahallata ma su yawan gaskiya Tahir duk sai da ya gayyato abokan karatunsu na Zariya har da su Jb da Mb da suka zauna Daki daya Cikin makaranta.
Wasu ma Sadiq ya manta da su Ammh Tahir bai manta da su ba.
Abokan kasuwancin Abba duk sun hallata mazajen su Surayya Harda Alhaji Jibril da ya zama na Hannun Daman Abba shi da Mijin Salima Mubarak.

Sannan yan'uwan Mallan Shitu da abokan arzuka duk sun hallata har da wasu daga cikin cllasmate din su Sultana da Siyama.
Hatta da Dangin Umma da Mama sun Hallaci wannan Daurin auran.
Bayan an gama daurin auran daman daga Gusai sun taho da abinci wad'anda za su koma Gusai suka Tsaya suka yi sallah suka ci abinci a nan gidan mallam Shitu.
Wadanda zasu koma daga nan aka Raba musu Takaway mai tsire da Lemuka.
Sadiq ba shi da wasu abokai Daga Tahir sai Jb sai Mb sauran duk sun tafi, Jb ma daganan ya wuce kano Mb ne kawai sai Tahir, Tahir ma yayyensa duk sun zo ammh daga shinkafi suka wuce Daura Hajja da matan su kasim suna Gusai ana cin Biki da su.
Saboda matsalan hanya  Karfe uku suka baro shinkafi zuwa Gusai
Abba da Mutanensa sun riga su yin gaba su Surayya suna ta kiran Assadiq yazo ga mai Hoto ya zo shi fa ake jira.
Ango na ta fama da Babban Rigar Shadda mai ruwan kasa, takalmimsa baki da hularsa dara kalan aikin jikinsa agogon hannunsa ma baki ne,
Cikin kayan da Abba ya Dinkamasa ne Tahir ma  Babba rigane a jikinsa kamar shine angon.
Duk da a saman Fuskarsa ya na Fara'a ammh daga kasan ransa damuwa ne damkam aciki sai ya ke ji kamar ya ci Amanar Siya me yasa bai fad'a mata gaskiya ba Tun farko?

Shi dai ya ke kawai ya ke yi, ammh kuma ya rasa sukunsa kaddara ta riga fata daman chan Allah ya Rubuta masa Hasiya da Sultana su ne matansa anan duniya.
Ba shi da wani Tsumi ballatana Dabara hakan wani kadararren Lamari ne daga cikin littafin kaddaransu Wato Launil Mahafuz.
Chapter 74 · 0% Book details