← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 75

Sashe 27

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maimakon yaji Alhaji Jibril ya karbi mganar Innani sai kawai yaji ya na Fad'in"Ba Mubarak na ke mgana ba Innani ina mganar Yar wajena Zahra'u da d'an wajen ku Abubakar Sadiq."
Sai falon ya Dau shuru kallo ya koma kan Alhaji Jibril.
Innani ko ta na jin abunda yace ta wani yamutsa fuska kafin tace"Wani Abubakar Sadiq din da wata Zahra'un?
Da sauri Mama tace"Magajin gida dai Innani da kika sani Sadiq."
Innani ta rafka salati ta na tafa Hannu har da wani cire gilashinta ta kare ma Alhaji Jibril kallon sama da kasa sannan ta maida gilashin nata lokaci d'aya ta na fadin"Ammh kai a wani gari a ka haife ka?
Ta fad'a ta na wani yamutsa Fuska
Alhaji Jibril cikin Ladabi yace"Ni haifaffan garin Zariya ne Innani aiki ne ya kawoni kaduna har kuma na yi aure na tara iyalai."
Innani ta wani tabe baki kamar taga kashi kafin tace"Ba shakka. Hala baka jin bayanin da na yi maka ba ne? Naga alamun baka gane bayanin namu ba ne bari na yi maka gwari gwari shi magajin gida da ka ke mganar a had'a shi da wannan Gajerar yar taka da matar sa wannan yar fara yarinyar Doguwa sulsana itace wacce zai aura ba domin ma Magajin gida yace a dakata ba ai da yanzu kila ma an samu Rabo."
Kunya ta kama Abba da su Umma na kalaman Innani da suka yi Tsauri.
Ita kuma Innani tunda taji yace yarsa ta san wannan gajeran ce tunda yar mai Tsawon da auranta har da ya'yanta.
Hajiya Murjanatu ko bakinciki ne suka mata runbdgu lokaci d'aya yasa ta kasa mgana illah kallon mijinta da take yi cikin Tuhuma meyasa baban bintu ya ke raina mata wayau ne haka? Ta yaya zai yanke Hukunci kan yarsu ammh bazai sanar da ita ba.
Sai da yazo ya yi mganarsa kuma ba ta samu karbuwa ba daga baya kuma cin zarafi na neman biyowa baya
to cin zarafi mana Innani tace gajerar yarsa da kushen Halitta a lamarin kenan.
Alhaji Jibril kuma ya kasa kallon matarsa ballatana su Innani ko da akazo wannan gabar bai ji ya karaya ba.
Sai ma kara Rusuna kai da ya yi ya na fad'in"Ai shiyasa da naji haka na so na Binne mganar a rai ku ka matsa har sai na sanar da ku."
Innani ta kallesa a rene  sai taji bala'in haushinsa take ji wato daman ba Domin Allah ya ke wannan ladabin ba saboda ya samu biyan bukata ne lalle aiko sai dai  ya bi wani sarkin.
Mubarak kuma Mamansa ya kallah itama ta kallesa sai dai ba su da ta cewa a yanzu tunda ba su da wannan Hurumin.
Abba ne ya yi Saurin cewa"Bakomai Alhaji Jibril na yaba da karamcinka. magajin gida kuma mijin mace hud'u ne bayan ya auri Sultana zai iya karawa da Ita Zahra'un."
Innani na jin haka bata bari ma ya Rufe baki ba ta saka musu kuka mai had'e da ihu.
Har da kurma ihun wayyo Allahta ta shiga uku.
Abba da su Umma suna Rige rigen isa gareta domin jin abunda ya sameta.
Ammh sai Innani ta cire gilashinta ta fara goge hawaye da Haban zaninta Lokaci d'aya ta na fad'in"Shikenan Sulaimanu shikenan zai saka a yi ma Susalana kishiya itama a kashe min ita kamar yadda aka kashe min kuluwata."
Ta karishe fad'a ta na mai kara fashewa da kuka kamar wacce ake yankata.
Umma ta kalli Abba shima ya kalleta Hajiya Murjanatu ta isa gaban Alhaji Jibril a sannu ta na fad'in"Me ka ke shirin aikatawa Baban Batul?
Kallonta ya yi kafin kai tsaye yace"Abunda kunnen ki yaji miki Murjanatu."
Da haka ya kauda kansa, Abba ko da su Umma suna ta faman lallashin Innani ammh taki daina kuka.
Kara fad'i ta ke yi za'a kashe mata Sulsana kamar yadda kishiyoyo suka kashe mata Kuluwarta.
Abba ya kalleta ya na fadin"Innani ki daina da Fad'in haka Hauwa fa lokacinta ne ya yi ba kasheta abokan zamanta suka yi ba fa."
Innani ta dago da idanuwanta da bata wani gani ta zabgamasa harara kafin tace"Matsa ka bani waje kai me ka sani? Kai dai a yi sha'ani kawai ammh a ranar gobe kiyama akwai tarin Hisabai a gaban Ubangiji ko tawa da Shitu kad'ai ta isa b'ata lokaci."
Mama ta so ta yi dariya ammh ta Daure ammh sai da ta juya baya ta na tarin karya.
Abba ya jinjina kai kafin yace"Shikenan naji ki bar mganar na nan don Allah."
Innani tace"Ta ya zan bar magana kana neman kace za'a yi ma Sulsana kishiya tun ma kafin ta shiga gidan?
Sulaimanu anya kana so ka gama da duniya lafiya ban sallamaka ba.?
Umma ta yi saurin taran Innani da cewa"Haba Innani bai kamata ba."
Kawai sai Innani ta cigaba da kukanta shi kuma Abba kunyan Alhaji Jibril yasa yace"Innani addini fa ya bamu damar auran mata sama da d'aya Hudu ya ce mu yi in muna da Hali."
Innani ta dago ta na kallonsa ranta bace tace"Wlh ko bayan raina a ka yi ma jikata Sulsana kishiya ban yafe maka ba Sulaimanu."
Ba su Abba kad ai suka zaro ido ba hatta da Alhaji Jibril da Hajiya Murjanatu.
Abba ya kalli Innani kafin yace

"Innani.."

Bai karisa ba ta katse shi da daga masa Hannu Lokaci d'aya ta na fad'in"Da wanda ya biya Sadakin da wad'anda suka zo daurin auran dukkan su Allah ya tsine musu ba su da albarkata kai har da shi magajin gidan inda ya sake ya yi ma jikata Kishiya ba ni ba shi har abada ni da shi uban kowa ya yi ta kansa."
Ai ta na fad'in haka sai jikin su Umma ya yi sanyi su san ta gama mgana Tunda har magajin gida bai Tsira ba.
Alhaji Jibril ya yi shuru ya na wani nazari kafin Daga bisani kamar an zabure sa ya mike zuwa gaban Innani ya Durkusa ya rike hannuwanta.
Ita kuma cikin masifa tunda ba gani take yi ba tace"Waye wannan kuma?
Da sauri yace"Ni ne Innani.".
Sai da ta ji muryansa sannan ta Saurara ammh fa ya sha harara da tabe taben baki.
Cikin Ladabi yace"Innani kada ki damu tunda baki so ba wanda zai yi ma Jikarki kishiya ko bayan ranki in sha Allahu"
Ba kunya ba komai Innani ta washe baki kafin tace"Ko kai fa? Ka ga dai an riga an ba shi ita kuma dangi kowa yasani nace maka ma ba domin magajin gida yace a dakata ba da yanzu kila har da rabo."
Alhaji Jibril yace"Bakomai Innani in Lokacin ya yi a sanar damu in sha Allahu zamu zo."
Innani tace"In sha Allahu kuwa Allah ya yi albarka kada ka damu kaji ko? Ba domin Sulsana ba ce da Tuni mun amimce ammh kada ka damu ka Siyama nan da Salima wannan Saurayin d'an naka ya zab'i daya acikin su sai a yi had'in zumuncin ba shikenan ba."
Alhaji Jibril yace"Shikenan ko Innani yadda kikace haka za'a yi"
Innani ta washe baki ta shiga saka masa albarka.
A daidai Lokacin aka fara kirayen kirayen sallar la'asar yasa mazan suka tafi masallaci matan suka yi na su a gida.
Suna dawowa Alhaji Jibril yace za su tafi Abba yace ya zata kwana za su yi sai gobe yace yau zasu koma sai kuma wani jigon.
Umma tace in sha Allahu suma suna nan zuwa tunda su sun fara zuwa saura su.
Hajiya Murjanatu yake kawai take yi ammh abun na cin ranta ta kosa su bar gida taji Dalilin Baban Batul da na aikata musu wannan Tozarcin.
Innani ko harda ita a masu rako ta na ta Allah ya shi albarka ammh ta tafka musu tsiya saboda son kanta.
Umma ta ba ma su zahra'u kyatan Turaman atamfofi da Turare sai Batul da bama Takalmi.
Mama kuma ta ba ma Fathihatu Kyautar Turaren wuta mai kamshi zuwan maiduguri.
Kamal kuma Abba ya basa kudi da baisan adadin su ba shi da Batul.
Karfe hud'u da rabi suka bar Haraban gidan Alhaji Sulaiman bayan Alhaji Jibril ya bama Innani kudi da yawa da su siyama duk ya rabama 5k kowacce ammh ban da Salima wacce ke cikin Shashen Mama bata ko Fito ba.
Duk da Mubarak yaso ya kara ganinta ammh har suka bar haraban gidan bai ga ko mai kama da ita ba.

Suna fita daga gidan ko anguwan Hajiya Murjanatu bata bari sun fita ba ta kalli Abba da ke gabam Mota Inda Mubarak ke driving tace"Baban Batul me nake jin ka aikata ne haka?
Ko waiwayowa bai yi ba cikin Kaushin Murya yace"Murjanatu ba anan ya kamata mu yi wannan mganar ba. So behave u self kina gaban yaran mu ne"
Sanin haka yasa sai ta danne mganar ammh abun na cin zuciyarta.
Abun takaicin ma su ke da ya mace ammh su suke kai tayi ana musu wulakanci kuma tasan haka kurum Baban Batul bazai aikata haka ba sai yasan ya na hangen riban da zai samu akan hakan.
Chapter 27 · 0% Book details