Sashe 61
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gidan Alhaji Sulaiman Shinkafi a tsakiyar Falon Innani ne mata baje ana ta Bude wasu kayan alfarma acikin wasu Rantsatsun akwatina.
Masu kawo kayan auren Mubarak ne daga Kaduna Yan'uwan Hajiya Murjanatu sai wasu daga cikin Dangin Alhaji Jibril daga Zariya.
Innani na gefe da katon gilashinta sai faman washe baki ta ke yi ita da su Umma da Mama sai yan'uwan Mama da suma suna wajen.
Sai kuma yan'uwan Saliman duka matan masu aure a garin suna wajen yan nesa ne ba su riga sun zo ba sun ce sai ana biki saura Sati daya zasu Fara sauka a garin.
Yau ya rage saura sati Hudu Bikin Mubarak da Salima, shine suka kawo kayan aure akwatuna Shidda da ghana cike da kaya sai son barka.
An yi musu abinci jallop rice da Chicken sai lemuka na kwali da wanda su Surayya suka had'a musu na kayan Itatuwa.
Sauran kayan su Sanks kuma da za'a ba su su tashi da shi ya na chan gidan Surayya sun had'u da ita Amaryan tare da Siyama da Sultana sai Sajida da Saddiqa suka je suna kama musu sauran kuma suna gidan Abba da su aka tarbi maso kawo kayan auren.
An gama Bud'e kayan an saka albarka Gabadaya sun ba da kudin Dinki Dubu Dari, Umma kuma ta maida musu Dubu Hamsun na Tukwaicin su.
Nan suka Rantse ba za su karb'a ba Umma kuma tace sai sun karb'a suma kudin yabawa ce suka ba su.
Falon dai na Innani ya yi albarka sai Hira ake da Shewa su Sa'ima na ta Daukan Video kayan Suna Rangad'a guda.
Innani dai yau ba Masifa sai washe baki ta ke yi Allah ya kusa cika mata Burinta saura na Magajin gida da Sulsana Shikenan bayan ta gama ganin ya'yan su sai ta mutu daga baya.
Baki na shirin tafiya bayan sun ci abinci sun yi salloli sai suka fara Haraman Tafiya.
Umma taja Surraya gefe ta na fadin"Wai ina su Sultana ne? Shuru har yanzu basu kawo ba kada a yi aikin banza naga suna shirin tafiya ne."
Surayya ta Dauko wayarta Cikin Aljihun Doguwar rigar da ke jikinta na Shadda ta na fad'in"Bari na kara kiran su Umma."
Daga haka ta fita daga Falon Innani ta koma chan gefe ta na kiran Wayar Salima ammh sai aka gayamata ta na amfani da wayar.
Karamin Tsaki ta ja a ranta ta san Da angon Salima ke faman wayarta na kwazzaba, sai ta maida Akalan kiranta wajen kiran Sajida.
Kira daya ana Biyu ta Dauka cikin magana a hankali Surayya tace"Sajida ya naji shuru ne? Zasu fa tafi"
Da Sauri Sajida dagachan Bangaren tace"Laa gamu nan mun gama Saddiqa ce kinsan zata Tukami ta ci kayan Fulawa ta barke da zawo yanzu haka ta na Tiolet."
Surayya tace"Subhanallah ku kariso sai tasha magani. Ku yi sauri don Allah ko kuma ku ba ma Su Siyama kudin adaidaita su hayo da kayan su kawo mana don Allah Sajida."
Sai ta amsa mata da to shikenan sannan suka katse wayar.
Tana juyowa suka had'e da Sa'ima da Sauri tace"Sun ce fa kada su yi yamma ga hanya ba kyau."
Surayya tace"Wai Saddiq ce ke gudawa ammh nace su ba ma su siyama sakon su hayo adaidaita."
Sa'ima tace"Asshaa. Allah ya sauwake."
Tare suka koma cikin Falon Innanin, suka kara bama bakin baki da su d'an kara jira kad'an don Allah.
Innani ta tabe baki kafin tace"Wai kuna ta su jira su jira to su jira Uban me Tunda sun kawo kaya an karb'a kuma tsakani ga Allah sun ci sun sha ai sai kuma ku bar su yi haraman tafiya in ba so kuke su kwana anan ba."
Umma ce ta yi saurin cewa"Ai yanzu zasu tafi Innani."
Harara Umma ta samu kafin a tab'e mata baki, Allah ya takaita abun bata kara mgana ba sai dai ta fara Rage fara'a s ta na ta yamutse Yamutsen fuska kamar taga kashi.
Kafin su Siyama su kariso Surraya ta kira yafi sau biyar sai chan suka kariso Ita da Sultana Dauke da Botikai duk an yi rapping din su da Farin Salatif.
Yan mata Biyu ne suna kuma Sanye da kaya iri d'aya, Doguwar itace Sultana ta na sanye da Atamfa mai Ruwan green shi yasa mayafin su ma kalarsa kenan ita kuma Siyama bata da Tsawo ammh kuma ta fi Sultana jiki.
Da sallama suka shiga Falon Innani sai kallo ya koma kansu, har kasa suka gaida baki, su kuma suka amsa baki har kunne su a tunanin su d'aya daga cikin ce surukar ta su, Surayya da Sa'ima suka karb'i botikan da suka zo da shi suka Tura gaban bakin suna fadin na su ne.
Ba damar suce bazasu tafi da shi ba Tunda sun ce domin su aka yi sai suka Fara Godiya.
Sultana ce ta fara mikewa zata fita Saboda kallon da ake ta yi mata sai ta Tsargu, ita kuma Siyama har hankalinta ya tafi kan ganin kayan da akwatin da suka fara Daukan idanuwanta.
Sultana na mikewa kanwar hajiya Murjanatu ta kalli Umma cikin Dariya ta na fad'in"Ma sha Allah nace Hajiya wance ce surukar tamu ko?
Ta fad"a Lokaci d'aya ta na nuna Sultana da ke tsaye suna mgana da Surayyah.
Kamar Innani daman ta sani kasa kunni daman ta na gefen su cikin zabura tace"Wace? Wai sulsana?
Ta wani kyabe baki kafin yace"Ahir ba ita ce bace surukar taku wannan da kike gani jikata ce itama bikinta saura wattani kad'an ita zata auri babban Jikana magajin wannan gidan, shima domin kinsan magajin gida da kafiya ne yaki bari a had'a sha'anin ai da tare za'ayi, ita surukar taku da kike mgana zaku ganta wata figaggiya haka da iyayi da feleke wata doguwa haka dai to itace salimar ai bata shigo ba ne ko , ke Siyama ina kuka baro yar'uwan taku ce?
Ta fad'a ta na Daga Murya, Umma dai sai ta bige da mirmishi.
Matar ba ta damu ba ta yi ta fatan alheri.
Umma ta amsa da Ameen ta na fadin"Bayan an yi na Salima da wattani biyu za'ayi na su. Sadiq din yaro na ne ita kuma Sultana yar kanwar megidan ne tun ta na karama ta rasa mahaifiyarta sai na karb'ota na riketa a wajena."
Cikin jin dadi matar tace"Dakyau Tuwo na Maina. Allah ya nuna mana Allah ya sanya alheri."
Duk yadda suka so su ga Salima ba su samu ganinta ba saboda sun ce yammah suke gudu ga nisa.
Ita kuma tana gidan Surayya suna tare da su Sajida sai bayan tafiyar su suka Dawo gidan Saddiqa duk ta zurma Saboda gudawa sai da ta sha mgani.
Nan fa suka baje ana ta kara ganin kaya ana yabawa da kokarin Mubarak da cewa ga shi ya gama gininsa sannan kuma ga kayan aure na gani na Fad'a, Salima na gefe ta na ta latsa wayarta Siyama na ta mata kwakwazon tazo taga kayan aurenta.
Cikin Yamutsa fuska tace"Ke je ki yi ta gani, ni na san komai da ke ciki tun tuni."
Sai falon na Innani ya Dau Ihu da Shewa sai taji kunya da ta ga sun had'a ido da Umma sai ta tashi da gudu ta fice Mama ta bi ta da cewa"Salima kenan an gama ni karatu zan yi."
Dariya suka kara sakamata Sa'ima ko sai faman Turama su shahida ta ke cikin Family group din su na SS SHINKAFI'S.
Inanni na gefe ta gaji da iface ifacen da suke mata a falo ta fara masifa ta na fadin"Wai meye haka? Kun zo kun cikamin Ihu a falona ku kwashi kayan ku don Allah ku ficemin a daki zan kwanta ne na Huta."
Umma ce ta fara bata hakuri ta kuma Umarci su Surayya da suka kwashe akwatinan zuwa bangaren Mama.
Innani na jin haka sai ta sauya mgana tace a kai cikin Dakinta sai Sulaimanu ya Dawo ya gani.
Gudun fitinarta yasa akayi mata abunda ta ke so harta y'an ya'yansu Innani sai da ta tarkasu tace zata kwanta ne ba d'an jikan da zai Takura mata ita da gidan Danta.
Sai taron ya koma Falon Umma har da Mama da Sauran yan'uwanta ana ta Fira da shewa.
Alrady daman abinci da yawa aka yi shiyasa sai ya zama ba su da yunwa.
Shiryen shiryen bikin kusan duk an kamallah hatta kayan dakin Salima an gama siyan komai ba ma ita ba Har Sultana abu kad'an ne ya rage yanzu haka.
Daman hausawa sun ce duk abunda aka sanyama Lokaci sai yazo, ga shi har auran Salima da Mubarak yazo, kuma cikin ikon Allah ya gama gininsa nan kusa da gidan iyayensa.
Sannan kuma ya ce Salima zata cigaba da karatunta tunda Burinta ne.
Kuma Saboda auransa ta b'ata Shekara daya gida a zaune bayan sun gama jarabawar SSCE.
A yayinda yanzu su Sultana na First semester ne na SS3, ita da Siyama da yanzu suka kara zama manya yan mata wad'anda keranci Budurci ya gama kere su gabadaya.
Da bikin Salima ya taso Umma da sauran yayyen Sadiq sun so a had'a auran nan Lokaci daya ammh yace daman Shi Tun farko bai ce za'ayi bikinsa Rana daya da Salima ba.
Tunda shi Magajin gida ne sai aka yi masa abunda ya ke so.
Da kuma Dalilin da yanzu ya na kula da Sultanan sosai yasa ba wanda ya taba wani Tunani.
Suna waya sosai in dai zai zo daga Zariya yana siyomata tsaraba na kayan kwalliyar mata kuma yace in dai tana bukatar wani abu ta gayamasa zai yi mata.
Kashe mata kudi ya ke tuni Abba da Umma sun daina mata wasu walwalahu Tuni Sadiq ya cike wannan bangaran.
Shi kuma abunda ba su sani ba ya yi mata adalci ne, kuma ya na yin hakane saboda kada ya bada kofar da za'a fara Zargin boyayyiyar Rayuwarsa.
Sauran yan'uwansa kuma sun masa uzuri da cewa ya fara aiki a Abuja a bari ta cewarsa ya samu natsuwa sannan ya Fahimci in da ya ke aiki kafin a yi auran na su.
*********
*Abuja.*
_EL-Rufa'i & Patners, 24 Aminu road Kano cresent Abuja Nageria._
Monday.