← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 75

Sashe 34

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hankalinsa na kan Links din da ya ke Sakawa shiyasa bai ga su Siyama ba.
Abba da Umma kuma kamshin Turarensa suka fara shaka shi ya sanar musu wanzuwarsa a wajen.
Umma kallonsa ta ke yi cikin Alfahari.
Sadiq na Dabam ne acikin zuciyarta duk da ba duka Rayuwarta ta yi tare da shi ba ammh akwai karfafan alaqa tsakaninta da Abunda ta Haifa.
Abba ma cikin Tarin alfahari ya ke kallonsa ya na jin wani annuri acikin ransa da Allah ya ba shi Sadiq a lokacin da ya riga ya fidda rai da Samun magaji.
Mama kuma kallonsa ta ke yi ta na auna kwarjininsa ba ta isa ta ce ga wani abu na rashin d'a da ya taba Had'a ta da Sadiq ba, bai taba nuna mata bambamci Tsakaninta da Umma ba, bai taba nuna bambamcin Tsakanin ya'yanta da ya'yan Umma ba.
Zuciyarta ta kasa jin Haushinsa Saboda Tarin kyakyawan Dabi'unsa.
Siyama da Salima sun shige Shashen Mama ba su lura da shi ba.
Ammh Sultana ta ganshi shiyasa ta tsaya kyam ta na kare masa kallo Zuciyarta na Harbawa.
Sai yanzu da ta kara wayau sannan ta had'u Da Sabbin kawaye a makaranta ta kara sanin muhimmancin Sadiq a Rayuwarta.
Ba ta san ta Tsaya ta na kare masa kallo ba, ta shagala da alfaharin yanzu wannan Had'adden gayen na ta ne ita kad'ai tuni wani alfahari ya cika kirjinta tare da wani kaunar Sadiq da tun daman ta na cikin zuciyarta Boyewa ta yi,
lokaci d'aya kuma kishi ya zo ya lullubeta na yadda zai fita har wasu matan su kalle mata abunta.
Sultana bata gama Fahimtar kanta ba ammh ta riga ta tabbatar da abu d'aya.
Ta na cikin Sahun mata ma su mugun kishi kishi ma na Hauka, ba ta kaunar taga wani ya rab'i da abunda ta ke so bata so ta kare rayuwarta a haka kamar yadda mahaifiyarta ta rasu ta bar duniya ta bar Baba da wasu matan kuma ya na cigaba da Rayuwarsa.
Ba ta son ta yi aure ta rika rab'a mijinta da wata kamar Umma da Mama, ba ta son ta yi auri taga wata matar na haihuwa da mijinta da ta ke so bayan ita, ba ta son ganin ya'yanta sun taso kamar su Salima da su Anty Surayya ta fi son komai in ya kasance nata ne to ya zama natan har gaban Abada nata ita kadai da bazata taba sharing d'insa da kowa ba.
Ta na cikin wannan Tunanin bata sani ba har ya gama saka Links dinsa ya Dago da kansa da su Umma ya fara cin karo suna masa mirmishi.
Shima cikin sauri ya maida musu da martanin mirmishin nasu sai dai ya yi Saurin kauda kansa gefe saboda ya na jin nauyin Umma da Abba a kan abunda ya aikata ba da sanin su ba.
Inda ya kai kallon nasa ne ya hango Sultana Tsaye kofar bangaran Umma cikin kayan makaranta goye da jaka a bayanta.
Abunda ya ba shi mamaki abu d'ayane zuwa Biyu, na farko ta yi kiba kamar ba wannan siririyar yarinyar Sultana ba na biyu kuma kuresa da idon da ta yi yasan tare suka ta shi a karkashin Rufi d'aya ammh bai taba sanin Sultana da kallo haka ba. yarinya ce mai kunya da shuru shuru.
Ya yi mamakin yadda ya ke kallonta ido cikin ido itama kuma ta na kallonsa bata Dauke idanuwanta ba.
Bai dauke kansa ba sai da yaji Umma na kiram sunansa sannan ya Sauke Numfashi ya karisa ga Umma ya Rankwafa ya gaisheta.
Ita ma kamar Abba Rumgumesa ta yi ta na fadin"Auta na ya kara girma."
Ya na mirmishi yace"Umma ta kina lafiya?
Ya fad'a ya na shafa fuskarta acikin ransa kuma fad'i ya ke Umma ki yafemin na yi miki Laifi.
Cikin jin dadi Umma Ta rike hannunsa ta na fadin"Lafiyata kalau sai dai ina kewar Auta na."
Kai ya kad'a kafin yace"Umma zan yi dogon Hutu wannan karon Autan ki zai dade tare da Ummansa."
Umma ta washe baki ta na kallon Abba kafin tace"Da gaske Auta?
Kai ya gyad'a mata sai kawai ta Rumgumesa ta na fad'in"Allah ya yi maka albarka Abubukar Sadiq"
Ya amsa mata da Ameen Ameen shi da Abba.
Sai a lokacin yaga Mama sakin Umma ya yi ya karisa gabanta ya Rankwafa ya na gaisheta ta saka hannu ta Dagosa ta na amsa cikin Sakewa.
Jinjina kai ya yi Lokaci d'aya ya na fadin"Mama duk kuna lafiya ko?
Mama tace"Lafiya kalau mu ke Sadiq ya zariyan?
Ya amsa mata da Alhamdulillah, Abba ya duba agogon Silban da ke hannunsa ya na fadin"Zamu makara fa Magaji."
Da Sauri yace"Mu je Abba."
Key din motar ya mika masa ta kamfanin Toyota.
Sadiq ya shiga gaba Abba na binsa a baya su Umma suka rakasu da Allah ya tsare.
Ba su bar wajen ba sai da suka ga Fitan su daga gidan sannan kowacce ta nufi bangaranta.
Umma bangaren Innani ta leka Allah Sarki ta iske ta barci ya kwasheta a kasa daga zaune sai ba ta tasheta ba ta koma bangarenta da Niyar in da idar da Sallah sai ta koma ta tasheta.
Ko kafin su Abba su dawo masallaci Umma ke da girki Ranar ita da Sultana da Hajiya yar aikinta sun gama had'a komai na abincin rana.
An kai na shashen Mama, Abba kuma da na Sadiq Umma tace akai bangaran Abba tunda tasan in suka dawo zasu zauna tare su tattauna.
Na Innani ne Umma ta Umarci Sultana da dauka ta kai mata sannan ta tasheta ta yi sallah.
Sultana ba ta yi niyar zuwa ba saboda tun jiya su ke fad'a da Innani daga jiya da Safe kafin su tafi makaranta ta shiga gaisheta sai tace ta kunna mata Tv tashar Larabawan nan.
Ba musu ta zo zata kunna sai Tv ya ki yi ashe kan soket din ya lalace.
Innani taji shuru ba'a kunna ba ta kara mgana Sultana tace ya lalace.
Ai Innani bata jira taji me ya lalace ba ta fara salati ta na salallami da cewa Sulaimanu ya siya mata Tibi ammh Sultana ta lalata mata Saboda mugunta da keta.
Ita kuma Sultana taji Haushi tace ba ita bace sannan ta daina ce mata muguwa.
Ai ko Innani ta harzuka ta lalubo sandarta ta daidai Saitin Sultana ta Rafka mata sai a saman kafarta sai da wajen ya kumbura sannan bai isheta ba ta bita da Zagin cewa Albasa ba ta yi Halin Ruwa ba, ba Halin Kuluwa ta Dauko ba bakin Hali da mugunta na Ubanta shitu ta gado.
Sultana na kuka ta bar bangaren Innani ta kuma yi alkwarin sai ta nemota bazata kara komawa ba jiya kam duk wanda ya shiga sai ta gayamasa Sultana ta lalata mata Tibinta Saboda muguntar da ta gada wajen Ubanta Shitu.
Saboda Umma ce shiyasa ta kasa mata gaddama.
Ganin ta na Tura baki yasa Umma ta yi dariya ta na fad'in"Ke da Kakarki taki kuma yau Sultana? Ba mai ji kan ku fa ke da Innani."
Sultana ta kwabe fuska kafin tace"Muguwa fa ta ke kirana yanzu."
Umma tace"Ki je ki kaimata zaku shirya ne."
Ba ta da Halin yin musu sai ta yafa mayafin Maryam's Egyptain Abayan da ke jikinta mai kalan sararin Samaniya
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418

Sannan t Dauki Farantin abincin Innani zuwa Banagaranta.
Ta na shiga ta iske ta bata Falon ga dai Sandarta da gilashinta nan.
Dankwafar da abincin ta yi a kasan Cafet din sannan ta saka kafa ta shure sandar Innani kamar itace da kanta ta Daketa.
Innani da ke cikin Dakinta bayan ta idar da sallah taji motsi daga ciki ta wage Murya ta na fadin"Waye nan?
Shuru ba'a yi mgana sai kawai Innani ta yi tsaki ta na fadin"Ko ma wani shegen ne kada ya yi magana. A fitar min daga daki tunda ba d'an wani ya gina min ba Ehe."
Sultana na jin haka bata kara ko Second ba ta fice daga bangaren innani da gudunta.
Innani ta ji gudun sai dai bata san ko waye ba kyafci ta yi kafin tace"Yanzu haka cikin ya'yan Suwaiba ne. Ina ga ja'irar nan ne Salima Mara kunya."
Bata san cewa Yar gaban goshinta ba ce Sultana da suka yi fad'a.
Sultana na komawa tace ma Umma ta kai mata Umma ta kalleta ta na Fad'in"Kin ta sheta ta yi sallar?
Sultana tace"eh"
Saboda in tace a'a Fad'a Umma zata yi mata..
Daman tare suke cin abinci da Umma suna zaune a tsakiyar falo Sajida ta kira wayar Umma ta Dauka suna mgana anan taji Umma na cewa Yaya Sadiq ya ce zai jima a wannan Hutun kafin ya koma haka kurum taji sanyi acikin ranta ko bakomai zata rika ganinsa Sosai ta na jin dadi.
Chapter 34 · 0% Book details