Sashe 59
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ALHAMDULILLAH kawai zan ce acikin Shud'ewar Shekara d'aya da Rabi, wanda ya yi daidai da shekaru Biyu da wasu wattani da aurena da Assadiq.
A zuwa wannan lokacin ni Hasiya Mamman kona na riga nasan Ubangiji ya gama yi mini dukkan wani gata anan Duniya.
Ya bani rai da lafiya sannan ya bani kwanciyar hankali natsuwa da cikar Zatin aure a tare dani, sannan ya Turomin Namiji tamkar da Dubu ASSADIQ wanda ya kasance wani Kafad'a da na kan saukar da kaina a samanta cikin kuka ko Dariya.
In Dariya ne shi zai tayani mu Dara in kuma abun kuka ne shi zai taimakamin ya Sharemin hawayena.
Zaman aure daman hausawa sun ce zo mu zauna ne sannan kuma sunce zo mu sab'a ne.
Bazan ce ina cikin Farinciki dari bisa Dari ba akwai kananun matsalolin da ba su kai ma a fad'e su ba.
Assadiq ya gama min koma a wannan Duniyan Tunda ya tsamo ni daga cikin kuntattaciyar Rayuwar da ni ke ciki ya raya zuciyata da abun kawa da Soyayya ya kuma nuna min nima kamar sauran mutane na ke wanda Ubangiji ya Hallice su tare da Tarin Ni'imominsa.
Assadiq ya yi sanadiyar da na manta da Rayuwata ta baya gabadaya, na Fuskanci Farincikin da ke tare da Rayuwata yanzu Assadiq na sona sannan yana son Farincikina kuma Bukatuna daidai misali in bai fi karfinsa ba yana cika mun su.
Ya maidani yar gata sannan yar lele wacce na zarce duka yayyena sa'ar miji da gidan aure.
A wanchan Shekaran ne ya sakani na Zana Jamb daman SSCE na ta yi kyau bani da matsala duk da ya lura karatun bai wani Dameni ba ammh bai Damu ba ya zaunar da ni ya nunamin Muhimmanci ilimin ya'ya mata a wannan Rayuwar.
Da taimakon kalaman karfin gwiwansa da Aljihunsa da kokarinsa na Fara karatu a Federal Collage of Education da ke zariya, da kuma Amincewarsa ko nace zabinsa na fara karatu a kolejin a shashen Biology Computer.
Da Farko ina ganin wahalan karatun ammh kuma Jajircewan Assadiq yasa na fara jin dad'in kasancewata cikin Daliban kalejin ta zariya mai Dauke da Dalibai mabambamta daga garuruwa a fad'in kasar nan.
Duk abunda ban gane ba shi ya ke zaunar dani ya koyamin har sai na gane, sannan bangaren Computer bani da matsala babu abunda bai sani ba na Computer.
Yanzu haka muna hutun karshen Shekara ne in mun koma zamu shiga NCE2.
In muna da karatun Safe tunda Regular na ke yi tare muke fita, ya sama min abun hawa sai na wuce shima ya ke tafiya wajen aikinsa in kuma aka tashi na samu abun hawan da zai kawoni har gida ya na bani ishasshen kudin kudin mota tare da kudin kashewa har ma wani Lokacin in ce masa kudin ya yi yawa hararata kawai ya ke baya cewa komai.
Duk abubuwan da suka faru na Farinciki ne a Rayuwata, Amma ta yi rashin lafiya mun je har gadan mallam Mamman tare da Assadiq ya gaida Amma da Adda, sai dai bai Kwana ba ya Dawo ya barni na kwana Biyu tare da Amma sai dai muka Dawo Tare da su Adda Fati.
Sannan Itama Amma tazo garin Zariya sau daya ta Dubamu kwananta uku a gidan Adda Fati ta sauka.
A zuwan ne ta taramu gabadaya ta yi mana Nasihan mu nemi Dangin Babanmu mu yi zumunci da su in muka ce zamu yanke zumunci Allah bazai kyalemu ba.
Sai muka nuna mata, cewa ai suma basa neman mu sai ta fashemana da kuka da cewa in Aka je Lahira Mahaifin mu ita zai ma kaico tunda bata nuna mana Muhimmancin Ahalinsa ba, ta Horemu da kada mu Damu su basu neme mu ba, mu sani suna da Hakkin zumunci a kan mu kamar yadda mu ma mu ke da shi a kansu Ruwanmu ne in mun ga Dama mu sauke wannan nauyin.
Da wannnan Nasihan nata yasa muka fara zuwa wasu sha'anin na su, ni saboda makaranta ma, ba kasafai na ke shiga ba, tunda Tun farko daman ina da wani bakin fenti da bakowa ke ina Rab'ana ba.
Kuma asabar da Lahadi Tare da Assadiq muke cinyesu a gida da Fita siyon kayan kwalama a kantina kantina Zariya da Suya spots har sun gaji da gane kammanin mu.
Restaurant kuwa sun samu bakin Aljihun Assadiq sai yadda suka yi da shi tunda na Lura shi Namiji ne mai son Fita irin wajejenan tare da matarsa.
A lokacin ya siyamin kayan alfarma kala kala a wajen maman Suhailat da Dogayen Riguna takalma da Hijabai ba na shigar banza sannan duk wanda ya gani yasan ina cikin jin dad'i da kwanciyar Hankali ballatana da duk ya siyamin Dogayen Rigunan na wajen Maryam's Eyptian Abaya masu kyau da yarari.
In na saka su sai na zama kamar balarabiyar kasar Saudiya Saboda Hasken Fata ta da ya karu tunda ina Samun ababen gina jiki, sannan abun mamaki na kara kiba na cika kamar bani bace wannan Hasiyar da kashi duk ya bayyana ajikina ba.
Mun taba zuwa bikin Yaron Baba Tanko wanda yan'uwa da Dama da suka ganni sun yi ta mamakin ganina da Irin sauyin rayuwar da na samu su azaton su ina chan cikin Wulakantciyar Rayuwa ne.
Har Baaba ta Lagos sai da ta yi maganar chanzatawata, Goggon kona kuwa ba kunya ta tambayeni wani miji na ke aure?
Mirmishi nayi ban bata amsa ba, Sai Adda Rukayya ce ta ba su amsa da cewa ma'aikaci ne kuma ya na karatu, nasan suna ta mamakin chanzata tare da mamakin ya aka yi na iya zaman aure kuma wani abu bai samu mijin ba? Tunda har suna tambayan shekara nawa da auran nawa ?
Adda Fati tace shekaru biyu da wani abu.
A fuskarsu sun kasa boye mamakin su, Baba Tanko da ya shigo ya ganni har na gaishesa bai iya gane ni ba sai da ya shiga ciki aka masa bayani sannan ya iya gane ni.
Da ya dawo zai fita kai tsaye ya kalleni ya na fad'in"Hasiya ko ba ke ba ce Hasiya ba?
Ina mirmishi nace ni ce Baba, kai tsaye yace"To to ammh nace bazaki jima ba zaki tafi ba ko?
Nasan abunda ya ke tsoro shi yasa ban Damu ba na gyada masa kai.
Kamar yadda yace ban jima ba na tafi ammh na yi ta sharan hawaye acikin adaidaita.
Duk da haka ba kowa ya ke zama kusa da ni ba sai yan'uwana da suka zame min Dole, ban ga laifin Baba Tanko ba Tunda Har yau Mijin Adda Rukayya in dai ya na gida ban isa na shigar masa gida ba, in kuma na shiga sai dai in baya nan da na Fahimci zuwana na kawo ma yar'uwata matsala.
Rabona da gidan tun wani zuwa da nayi ya tare kofar gida yace bazan shigar masa gida ba, na yi kokarin kada na nuna naji zafi ammh sai da na nuna hakan da na koma gida kuka na fashema Assadiq, shi ya yi ta lallashina ya kara Tusamin yakana da Iklasi acikin zuciyata ya kuma kara Sanar da ni cewa jarabawa ce in na yi wasa da Tauhidi to zan gaza har a wajen Ubangiji.
Da nasihansa da shawarwarinsa yasa yanzu na daina damuwa da ire iren wad'anan kananun abubuwan.
na maida Hankalina wajen karatunaa, ban dauka bayan Ramatu zan kara yin wata kawa ba sai ga shi Shigata kwaleji na had'u da Wata Safiya Ahmad, group d'in mu daya da ita kamar wasa sai ga shi mun saba har mun zama kawaye.
Ita yar anguwan kaya ce sannan ita batayi aure ba, abunda yasa ma muka Saba ita ta fara muna ta na so na da kawa, sannan gata da Hankali da natuwa ga kokari, shiyasa sai na amimta da ita muke kawance da juna.
Tasan ina da aure ta kuma san inda na ke zaune ammh bata san wani Labari a kaina ba.
Assadiq kuma bai taba ganinta ba sai dai yakan ji sunanta a bakina, tunda baya zaman gidan sai weekend, saboda aiki da kuma karatunsa.
Ko matan gidanmu yanzu ba na bi ta kansu kwata kwata duk da yanzu Ummi ce kad'ai Fadila sun tashi ammh kafin ta shin su sai da suka yi Rabuwar uwaka da Ubanka da juna ita da Ummi fad'a har da shigar mazajensu cikin maganar.