Sashe 60
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ranar da sukayi tsiyan ina gidan har da Dambe ina gefe ban ko rabasu ba, Maman Sulaihat ce ke raba su fad'an mganace ta tsegumi da kananun maganganu.
Da cewar ita Fadilan Ummi ce taje gari ta na yawo da cewa wai ta na jin ihunta ranar Daren farkonta sannan ta ce kuma ta na jin ihun mijnta in suna kwanciyar aure.
Wani Tudu wani ganganre Fadila taji Labari shine tazo ta tada bala'i daga gani dai ba gaskiya a lamarin Ummi Tunda tace itama Fadila tace mijinta ba shi da karfin mazantaka Tundaga yanayinsa wuyansa kamar marikin lema.
Abu kamar wasa kamar abun Dariya, Sai ga shi sun had'u suna ta Tona ma kansu asiri,da mazajensu kuma daga gani suna zama ne su yi hirar, Dambe suka yi kace kace kamar wasu yara Maman Suhailat na ta ce min nazo mu yi rabo na yi baya, ni ba ma a wannan gidan ba na riga nasan irin wannan abubuwan na gidan Haya Tun zaman mu a garin Samaru.
Su kansu kwanaki chan gidan da muka zauna da naje kwanaki gaisuwa Maman Salihi mahaifiyarta ta rasu Ramatu ta gayamin na biyamata muka ke gidan tare shine zuwa na Farko Tun bayan aurena.
Gidan duk ya watse kaltume ta tashi ita da Maman Boy suma ance fad'a ce ta had'a su kaca kaca abun dai ba dadin ji ballatana gani, shiyasa na kiyayi kaina da mutanen da ke zama a gidan haya sannan na san duka Tarin kalubalen da mata ke Fuskata a zaman gidan Haya.
Bayan Fadila ta tashi an saka wata wata ya'yanta Biyar, Sai Ummi ta koma kamar jaba saboda yadda ta ke Dari dari da mutane ba Halin kuma ni ta Dawomin bayan ta san abunda suka yi min duk da ta so hakan ammh kwata kwata ban bata Fuska ba.
Saboda Sau daya maciji ke saran Mumuni, bazan kara saken da wata zata shiga jikina daga baya kuma ta Tozartani da kaddarata ba.
Yanzu babbar waya ce ke hannuna ta kamfanin Infinix, sai dai har karamar wayar ta na Hannuna ita d'ayan layin ke ciki sai kuma ita ya siyamin Layin Airtel na ke amfani da shi Saboda makaranta sannan na ce masa ina son na Fara kasuwanci kuma ya bani goyon baya ammh yace na bari mu samu jari mai Tsoka Tukunnah.
Ina zaune ne a wani yammancin Alhamis tunda muna Hutun makaranta ina Tunanin wani irin kalubale na taba fuskata a zamana da Assadiq?, Na duba na hango na kasa hango ko d'aya sai wata matsala guda daya da ta fara cin mu tuwo a kwarya.
Abu na Farko shine da gaske ne na Fara Fahimtar Assadiq na Boye min wani abu, duk yadda muka zama Rufin asirin juna bai yarda a kirasa a waya ya yi ta a gabana ba, in dai ya na tare dani to wayarsa ta na kashe ne sai dai ko in ya fita daga gidan sannan yana yin wasu abubuwan marasa gaskiya..
Na fara Fahimtar bai gayama Yan'uwansa na kauye ya aureni ba, Tunda har yau bai taba had'ani da wani na shi ko a waya ba, Sannan na yi nayi har na gaji bai taba kaini garin su ba, daganan sai na fara Fahimtar akwai wani abu Tunda ai ya na zuwa ganinsu akai akai kuma yana kawomin Tsaraba yace Daga kakarsa.
Ammh ya ki amincewa da ya kaini na gansu, har na gaji da tambayoyin su Adda Fati na zauna na Sharara musu karyar cewa ai ya kaini naje na ga Ahalinsa.
In ma na Cigaba da matsamasa sai ya Sauya fuska kwata kwata ya nuna baya son mganar abun na Damuna, kada yazo mu fara tara zuru'a a samu matsala fa, tunda chan kwanaki na fara zargin ko ina da ciki ne ganin wattani uku ban yi batan wata ba ina Shirin yi masa mganar sai kuma naga Period dina daga kuma watan bai karamin Tsallake ba sai na watsar da Zargin cewa ina da Shigar ciki ne.
A yanzu haka ko wata Daya Assadiq bai cika da Samun wani aiki a garin Abuja ba, ya tafi Sati uku bai zo gida ba mun yi mgana da shi yace min sai yagama sanin kan wajen gabadaya ko zai fara zuwa min weekend sai da ya barmin komai na kayan abinci da Ishaahen kud'i a Hannuna ko da wata bukatar ta taso.
Sannan ya siya mota duk dai ba wata babba bace, Assadiq ya mallaki yar karamar motar hawa tun kafin ya samu wannan aikin na garin Abuja.
Yadda abun ke damuna a raina yasa na kasa sukuni ga shi na yi karya ba Halin na samu Ramatu ko Adda Fati mu Tattauna.
Ammh tabbas jikina ya bani akwai wani matsalan! Kuma ina da kyakyawan zato akan cewa yan'uwan Assadiq ba su san da ni a matsayin matarsa ba.
********
*GUSAU.*
Asabar, 12:10pm.