← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 75

Sashe 6

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*Janafty*
*TMWB2K003*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641

Washegari kan mganar suka rabu da Tahir ya na ko zuwa makaranta ya nemi Hambali ya yi masa mganar, nan da nan yace kada ya daamu za'a samu duk da ya sanar da shi ba sa bukata a nan samaru sai dai wani waje na daban.
To an samu kafin mu su tashi daga makaranta sai dai ciki da falon da ya nema ne ba'a samu ba, sai dai Safecanten mai daki da kitchen a had'e kuma a Hanwa ne aka samu gidan.
Sabon gida ne ma yanzu ne ake son a fara ba da hayan gidan mai dauke da Dakuna hud'u a shekara dubu dari da Hamsin
Da Tahir ya nace sai mai ciki da Falo kad'ai Hambali ya gayamasa gaskiya yace irin d'akunan nan na Haya suna Wahala ga irin wanda aka fi saurin kamawa a irin anguwan waje wajen gari gwara kawai su karb'a.
Bai ce masa komai ba sai dai yace masa in za su karb'an zai kirasa a waya sai da ya dawo gida ya jira Sadiq ya Dawo sannan ya sanar da shi Halin da ake ciki.
Nan take Sadiq yace ba komai su kama wannan d'in.
Tahir ya kallesa shekesheke kafin yace"Ka na da dubu dari da hamsin din ne yanzu?
Sadiq yace"Akwai kudi a hannuna mana da na so na yi ma Abba magana sai kuma na fasa kasan akwai kudin alawuna na ba duka nake amfani da su ba, Tunda koda yaushe Abba na Turamun kudi sai na yi amfani da shi."
Jin haka yasa Tahir ya yi shuru bayan  ya kira Hambali yace su same shi a bakin Titi tare suka dumguma suka tafi ganin gida kuma Alhamdulillah Tsarin ya yi ma Sadiq sosai sai dai ya so da wasu a gidan Tunda shi kam ba zuwa zai yi ya zauna a inda ta ke ba ko Saboda Halin rayuwar nan da muke ciki.
Da ya yi ma Hambalin mgana shi kuma yace kada su damu duka d'akunan uku an kama daman wannan ne kad'ai ya rage kuma amare za'a saka nan da wata daya.
Sai Sadiq yaji dadin haka domin a na shi Tsarin ba Tsarin ya zauna a nan gidan Tare da Hasiya.
Karya suka yi ma Hambali da cewa wani dan'uwan Tahir ne ya yi aure shine suke duba masa gida shi kuma bai Damu ba ya na kan sana'ar shi ne Daman shi ya samo musu gida Saboda shi suka sani shi kuma suka bama kudin Hayan gida na Shekara cur.
Sai yamma suka dawo shiyasa Sadiq bai samu damar kiran Adda Fati ba sai da Daddare yace mata ya samu wani waje duk da kudinsa bai kai ba an yi masa ragi.

Sun rabu akan gobe da Safe tunda Tahir CDS zashi kuma sai ya fara biyawa Fada sai Sadiq ya rokesa kan ya raka Adda Fati ta ga gidan ya na masifa ya na komai ya amince shiyasa Sadiq ya fara tafiya ya barshi Tunda shi nan kafin akai kwangila za shi.
Lambar wayar Tahir ya turama Adda Fati shima ya bata na shi ammh Tahir bai kirata ba sai itace ta kirashi duk da taso suje ko ita da Rukayya ko Ramatu sai taga tafiyar ta su ta Safe ce sai ta yanke shawaran in taje taga gidan daga baya sai ta kai su.
Tunda ita ta na Sabongari ne a pizzet suka had'u da Sadiq ya saka complete kayan Bautar kasar sa sama sama suka gaisa suka samu abun hawa sai Hanwa.
Suna zuwa daman already makullin gidan na hannun Tahir shi ya Bude mata sannan ya bata key d'in Dakin lokaci d'aya ya na fad'a mata Shi zai tafi ne kada ya makara ganin saurin da ya ke yi yasa ta yi masa uzuri ammh ba tun yau ba ta Lura da Tahir din ya na da Basar da Mutane.
Alhamdulillah ta duba daki babu abunda babu ga shi sabon waje gidan ma ya  burgeta sosai ganin ba su da yawa ta kuma san in dai zama ne na gidan Haya Hasiya tasan kalubalensa zata kiyaye in sha Allahu.
Ta jima ta na duba Dakunan sai da ta kirga kofa saboda Labule tun kuma ta na gidan ta kira Adda Rukkaya ta fad'ama ita kuma tace sai gobe zata zo su yi mgana.
Cikin Farinciki Adda Fati ta dawo duk da bata gayamin inda taje ba ammh ta na cemin zata fita da Sassafen nan jikina ya ba ni wani abu.
sai ko ga shi ta na waye waye ta na ba da Labarin Tsarin wajen da zan zauna tabbacin chan taje da Safe kenan.
Ina jinsu da Rana suna mgana da Adda sai kuma aka bama Amma suka cigaba da mganarsu.
Tashi na yi na shige ciki domin maganar sam bata burgeni meye amfanin bad'i ba rai? Suna rawan jikin tarewar da ina da tabbacin bazai Daure ba sai wani abu ya Biyo baya.
Ai ni ina ganin abu ganin idona wajen su Adda Fati bayan hidimar kayan Dakina sai kuma suka Turomin Ramatu da magungunar gyara akan sai na sha sai suka bani dariya.
Auren Abubakar na farko ne na yi wannan rawan jiki ammh ko na Salisu Fargaba bata barni na saki jiki na yi wannan Shaye shayen ba.
Wannan ma na Tubure nace bazan yi ba da naga sun fara matsamin kawai sai na fashe musu da kuka ina fad'in"Nace ba na so ko? Haba ku kyaleni mana duk abunda ku ke yi ina sane ban yi muku mgana ba meyasa ni ku ke so ku tursasani aikata abunda ban yi ra'ayi ba. Wlh kuka matsamin zan yi tafiyata in da har Abada bazaku kara ganina ba."
Jin kalamaina yasa suka shafamin Lafiya suka cigaba da Shirinsu duk azatona Amma zata zo tariyata saboda nayi kewarta sosai Fushin Abunda tayi min yasa ko a waya ban yarda na yi mgana da ita ba.
Ashe bansani ba tace bata zo ba Adda ce zata zo kad'ai.
Ina da labulai na tun na gidan Abubakar na kofofi da yawa Shiyasa a auran Salisu ban siya ba wannan karon ma wankesu a sake yi aka goge sai dai sun karamin kayan kitchen da abubuwan da baza'a rasa ba.
Adda Rukayya kuma ta yi mana Atamfa mu h'udu da zamu ci yinin Tarewa da shi, Ramatu kuma ta yi min kayan maggi da sauran kayan Dake dake.
Chapter 6 · 0% Book details