← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 75

Sashe 2

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tausayama Rayuwar Hasiya matuka duk da ya ji labarin a bakin Tahir sai dai shi ba yadda ya Dauka ba ne.
Yaji duniyar ta tsaya masa Lokacin da Amma ta durkusa a gabansa ta had'a Hannayenta waje d'aya ta na kuka ta na rokomsa da ya rufa mata asiri ya auri Hasiya.
Alokacin kallonta ya yi a tsorace kafin yace"Aure kuma Amma? Meyasa zaki ce na auri yarki Ahalin baki sanni ba bakisan komai a game da ni ba?
Amma ta bude baki cikin kuka ta na Fad'in"Bansan ka ba Abubakar ammh wlh tallahi naji lokaci d'aya ka shiga raina ina ji kuma ajikina bazaka taba cutar da Hasiya ba."
Sadiq ya dad'e ya na kallon Amma ajiyan ya na tunanin ita ko meyasa zata yi haka?
Cikin Sarkewar murya yace"Ba ni da kowa sannan ba ni da komai da me zan riketa? Sannan in dai a wajena ne ba zata samu kyakyawan rayuwar da ki ke mata fata ba, Saboda ni d'an makaranta ne ba ni da komai sannan ban mallaki komai ba Amma"
A lokacin Amma ta fad'i wasu maganganu da suka sanyaya masa jiki da su ne silar da suka saka ya amince ya taimaki uwar da ke bukatar taimakonsa indai yasan Darajan Mahaifiya.
Kafarsa ta kama ta rike lokaci d'aya ta na fad'in" _Ka ciyar da ita da abunda kaci Abubakar, Sannan ka Tunfatarta da ita da abunda ka tufatar da kanka, sannan ka ijiyeta a inda ka ke Rayuwa  Ba rayuwar Kud'i ko dukiya Nake son Hasiya ta yi ba. a'a ina mata Fatan rayuwar natsuwa kwanciyar Hankali mai Dorewa har Abada._"

Ya na wannan Tunanin ita kuma Amma na warware musu yadda tattaunawarsu ta jiya ta kaya tsakaninta da Abubakar.
Tahir na kallonta ji ya ke kamar ya tashi ya fita domin gani ya ke kamar Tatsuniya ta ke faman maimaita musu sannan ji ya ke kamar ya bude baki ya gayamata Sadiq ba maraya ba ne da yasa ta yi wasa da rayuwarsa Abun alfaharin wani kyakyawan Ahali ne sannan dan gata ne da bai Chanchanci auran kaskanci kamar yadda ta cutar da shi wajen aura mata zabiyar bazawaran yar ta ba.
Amma ta share hawaye da Haban zaninta ta na fad'in"Ba na so na tafi da Hasiya garin mu  saboda nan ne ta saba da shi fiye da ko'ina sannan zata fi sakewa in ta na ganin yan'uwanta a kusa da ita da wannan dalilin yasa na Roki Abubakar da ya aureki Hasiya sannan ki yi hakuri ban nemi jin ta bakin ki ba duk da addini ya baki wannan damar ni na yanke miki Sadakin ki da kaina nace ya bada Dubu talatin mun yafe komai Daga bangaransa.

Na tara ku ne ku zama shaida sannan na raba minti saboda Mutanen da ke zagaye damu suma su shaida hakan. Isuhu ma naji dadi da ya zama shaida wanda da ni da shi zamu iya gayama Adda abunda ya faru wanda bata sani ba ni zan bishi mu tafi na bar Hasiya Hannun mijinta Abubakar da na ke da yakinin zai rike min ita bisa gaskiya da Amana. Sannan na barta hannun ku Inna talatu Ramatu Fati da Rukayya Hasiya ta ki ce Amanarta da kula da Rayuwarta duka suna Hannun Allah ne kuma suna hannunku. Ku kular min da ita don Allah tunda kuna gani Rayuwarta ba ta yi daidai da irin kyakyawan Rayuwar da ku ka samu ba."
Sai kawai Amma ta fashe da kuka wiwi. Adda Fati ma ta fara tayata Inna Talatu ne ta ke fad'in"Ki yi Shuru Aisha in sha Allahu kyakyawan Niyarki ta Alheri bazata tafi a banza ba. Hasiya kuma kada ki damu ki kaddara kina tare da ita in sha Allahu."
Amma ta gyad'a kai cikin muryan kuka ta kalli Sadiq da Tahir da kansu ke kasa kamar ba sa wajen tace"Abubakar ga Hasiya nan. Ka rike hannunta ka da ka saketa har abada. Ka zame mata bango wanda zai kareta ga duk wani abun k'i, ka zame mata tudun Dafawa Abubakar ka kare rayuwarta ga dukkan wani barazana. Nasan Hasiya bazaka taba samun matsala daga bangaranta ba zata zauna da kai ta yi hakuri da kai sannan zata yi maka biyayya har karfin iyawarta Allah ya baku zaman Lafiya tare da zuru'a mai albarka a Tsakanin ku."
Tahir a saman lebensa yace ba Ameen ba Sadiq kuma sai ya samu kansa da amsawa acikin ransa.
Inna talatu ta bude murya ta na amsawa da Ameen Ameen.
Amma Adda Fati ta kallah kafin tace"Kayan Hasiya na jere su na wuyan ki Fati na bar komai a hannunki."
Adda fati ta jinjina kai kafin tace"In sha Allahu Amma."

Adda Rukayya ta sake kallah kafin tace"Rukayya ke ce Babba. Ki rike girmanki ki ja yan'uwanki ajiki kada ki manta bayan su baki da yan'uwan da suka wuce su, Ki zama Alkaliya mai adalci a tsakanin kannen ki, ki yi hakuri da su don Allah bayan ba ni ke zaki cigaba da Bibiyan lamarin su. Sannan kada ku manta da Dangin babanku ku bisu ku yi zumumci da su ko da su baza su yi zumumci da ku ba hakki ne ku a kan ku ku yi zumunci da su."
Adda Rukayya kanta na kasa tace"In sha Allahu Amma"
Amma ta juya ta na kallon Ramatu Lokaci d'aya ta na fad'in"Ramatu ba sai nace miki komai ba. kinsan matsayinki a rayuwar Hasiya basai na yi miki wata mgana ba, nasan zaki yi komai domin ganin Farinciki a rayuwar Hasiya nagado miki sosai Allah ya saka miki da Alheri ya Dauwamar da zaman lafiya a tsakanin ki da mijinki."
Ramatu ta amsa da cewa"In sha Allahu Amma Ameen nima nagode."
Kowa sai da ya yi mgana a dakin nan ban da ni da kaina ke kasa ko motsin kirki ban yi ba.
Amma ta kalleni na wani Lokaci kafin ta kira sunana ina Dagowa ta ga hawaye suna bin kumatuna alamun kuka naci a zaunenan da na ke.
Cikin mirmishi Amma tace"Hasiya baki ce komai ba?
Ajiyar rai na Sauke kafin nace"Amma me zan ce? Kin riga kin yi abunda baki shawarce ni ba, gaddama ko saba Umarninki ba Halina ba ne ammh wannan karon na kasa yi miki biyayya. Na kasa jin auran nan a raina Amma na kasa."
Ba Amma kad'ai ba hatta Sadiq da Tahir a tare suka dago suna kallona.
Ni ko idanuwana na Runtse sai hawaye Sharr cikin kuka nace"Nasan rayuwata cike ta ke da tarin kaddarori ina cikin Tsaka mai wuya Amma, Kinsan na sani aure ba shi ne mafita a cikin Rayuwata ba.
Nayi auran nan na farko me na tsira da shi bayan saki da Tozarci? Ban karaya ba na sake yin wani auran shima me na Tsira da shi bayan Sakin wulakanci da Tozarcin da ya biyo baya Amma meyasa kuma zamu kara koma gurbin da muka san karshensa? Kin so ni kin yi son kai Amma kin jefa Rayuwar sa cikin Rayuwata Alhalinsa kinsan karshen hakan daidai ya ke da asaran dukiya da asaran lafiya da wani abunda wannan karon bamu san me zai Faru ba."
Na karishe fad'a cikin kuka Amma da Sauri ta mike ta na fad'in

"Hasiya.."

Cikin Daga murya nima na mike ina Daga mata hannu Lokaci d'aya ina Fad'in"A'a Amma. Wannan karon baki yi daidai ba. Kin so ni ki ki shi, Kuma Hadisi ne kyakyawa ka so ma Dan'uwanka abunda ka ke so ma kanka. Amma na riga nace na gama aure a duniyar nan indai ta sanadina Rayuka zasu rika baci suna shiga mawuyacin Hali wlh na Hakura na Hakura Amma."
Bansan lokacin da naji wani irin kuka ya fito daga kasan raina ba sai gani kawai suka yi na zube a kasa ina wani irin gunjin kuka domin kafafuna ne suka daina daukana da ya sa dole na bi zabinsu na zube a kasa.
Kuka na ya tada Hanifa da ke bayana da Sauri Adda Rukayya ta yaye hijabina ta saukota duk ta had'a zufa. Kokarin kamani su ke in tashi naki Amma sai ta fashe da kuka ta kasa mgana.
Cikin kukan na d'ago muka Had'a ido da Assadiq.
da rarrafe na karisa gabansa cikin fitan hayyaci nace"Ka yi ma girman Allah ka sakeni ASSADIQ. ka da ka kara minti d'aya da aure ne a tare da kai  ka tsira da rayuwarka don Allah. Ka gani bazan damu ba, Salisu ma ranar da aka daura ma aure ya sakeni ammh duk da haka bai Tsira ba yana nan yana jinya Abubakar ma sai da komai na shi ya kare sai da komai na mahaifinshi ya kare duk saboda Dalilina ka sakeni ni ba kamar sauran matan da zasu samu kwanciyar Hankali ta sanadin aure ba ne ni Hasiya na yarda Annoba ce sannan gobarace ni duk inda na shiga sai naci Dukiya ko na taba lafiya."
Na karishe fad'a ina wani irin kuka Amma ta dakamin Tsawa lokaci d'aya ta na fad'in"Hasiya lafiyan ki kalau kuwa?
Cikin kukan na cigaba da fadin"Amma me yasa kika yi min haka batare da sanina ba? Kina so ki dauwama kina ganina cikin kunci ? To wannan auran ne zai sakani cikin kuka kamar yadda sauran suka zo suka kare haka shima wannan zai kare kamar ba'a yi ba."
Wannan karon Adda Fati ce ta zo ta kamani ta na fad'in"Hasiya wani irin mganace wannan?
Ta ke fad'a itama kamar ta yi kuka ina kallonta fuskata har ta koma jajur Saboda kuka nace"Eh mana da kun bar na zauna da rayuwata da ya fiyemin auran nan shine ke jawomin komai, in ban auri kowa ba wazai ce nayi sanadiyar rasa lafiyan wani? Balle ace an rasa dukiya!? ni rayuwata ba tare da kowa ba ta fiyemin kowacce Rayuwa da ki ke yi min Fata Amma."
Chapter 2 · 0% Book details