Sashe 49
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Umma ta Dake ta na gayama Innani illar shan wannan jike jiken da ba wanda yasan wasu itatuwa ne ma Innanin ta jika zata Dora ma Abba, shi kuma bai isa ya yi mata Musu ba haka ma su Baba Sammani suna mgana yanzu Innani sai ta iya cewa ina Ruwansu da sha'anin D'anta.
Ilai kuwa Baba Sammani ganin ana ta Daga da ita ta Dake yasa cikin Lallashi yace"Innani tunda har an fara na asibiti ki bari zuwa gaba sai ya fara shan na kin"
Ai sai Innani ta kallesa a Dage kafin yace"Kaji min wani Tsirfa da Iyayi ko shisshigi Tusa kai ba kwarjini, ina Ruwan ka da sha'anin d'a na da zaka rika Tsoma min baki ? Ba asibiti ba asibito dole zan gina Sulaimanu da maganin Tsarin jiki tunda har kuna gani magauta sun fara sako sa a gaba."
Ta fad'a ta na wani kumfar baki Duk ta gama Tofe na kusa da ita da Miyan bakinta.
Juyawa ta yi ta na neman wanda zata aika chan idanuwanta suka hango mata Sultana da Sauri ta ya fito da Hannu sai da ta zo gabanta sannan tace taje ta Dauko mata karamin kofi ta Tsiyayan ma Sulaimanu mganin nan.
Sadiq duk yana jinta baya so ya yi mgana ne Hayaniyar Innani ba ta karewa daga an hanata wannan sai ta koma kan wannan.
Sai da Sultana ta Dawo da Kofin Inanni ta cika shi da wani kalan mgani baki har ya na wani yauki yauki ta kalli Sadiq ta na fadin"Magajin gida d'ago min Sulaimanu dakyau ko bai sha ba, Dore zan masa tunda ni na kawosa duniyar nan ba wata ba."
Bude Idanuwansa ya yi da suka Sauya Launi kafin cikin sanyin murya yace"Innani mu ga mganin"
Da yake shine sai batayi gaddama ba ta mika masa ya amsa ya na gani da ya shinshina sai yaji ma yana dan tashi, da Sauri ya kauda kansa kafin ya yamutsa fuska ya na fadin"Innani wannan wani irin mgani ne ya na wari?
Innani ta kallesa sai dai batayi mgana ba saboda magajin gida ne.
Innani naji ta na gani Sadiq ya sa Salima da Siyama su Dauke maganin gabadaya suje su watsar da shi suka Dauka suka fita suna toshe Hanci Innani ta shaka kamar ta Mutu. Abba ko fadi ya ke Sadiq ya ba shi zai sha shi kuma kai tsaye yace"Abba in Innani na fama da rikicin Tsufa kai fa? To wlh ka sha wannan abun in ma baka da wata cuta tabbas sai ka samo ta."
Kowa sai danne dariyansa ya ke yi, Umma ta yi mirmishi daman tasan maganin Innani mutum daya ne kuma Allah ya kawo shi a lokacin daya dace.
Sadiq ya takarkare ya na yi ma Innani bayanin ire iren wad'annan mgangunan da cewa ba wai yace maganin gargajiya ba su da kyau ba ne a'a ya na magana ne akan irin nata gaskiya ba shi da wata manufa in ma maganin zata samo masa taje wajen masana abun su had'a mata na su bawai tace ita zata had'a da kanta ba a ransa ma ya fara Tunanin Allah kadai yasan da wani hauka ne Innani ta Had'a waje d'aya ta jika.
Kamar Innani ta Hakura ashe ba ta Hakura ba, kawai ji akayi ta saka Ihu da kuka ta na fad'in"Shikenan tunda Magajin gida ya zubar da mgananin da ta jika ma Sulaimanu saboda Magauta"
Ta kalli Sadiq ta na fadin"Sulaimanu fa Jifan magauta ne ko bakwa ganewa? Mutane yanzu sam ba Allah a ransu tunda anga ya na dan fita Harkokinsa shikenan za'ayi masa Sanadin samunsa Tir mutane dai ba Allah acikin ransu."
Sadiq ya kalleta cikin kaushinsa kafin yace"Ba Allah a ran mutane ko ke ce ba Allah sam acikin ranki ?
Sai Falon ya Dauki shuru Innani ta yi kasake ta na jin Magajin gida.
Cikin bacin rai yace"In kin san akwai Allah meyasa zaki rika Tunanin wai magauta ne suka jefi Abba? Wannan ai Tunanin wad'anda ba Allah ne a ransu innani."
Innani sai ta fara juya bakinta kafin tace"Ni wlh akwai Allah a raina Kawai dai ina gaya muku gaskiyan yadda Mutane suka Lalace ne."
Sadiq yace"Ke dai kika lalace da shigen rashin Dogara ga Allah. Kuma Allah ne baki sani ba sannan baki da Tauhidi Shiyasa bakisan Takwalli ba."
Ya karishe fad'a cikin kaushinsa.
Abba na kishingid'e yace"Abubakar kyale min uwa hakanan don Allah."
Sadiq yace"Abba ka bari na sanar da ita wanene Ubangijinta domin na Tabbata bata san shi ba"
Ba Innani kad'ai ba kowa da ke falon sai da ya bi shi da kallon mamakin kalamansa.
Shi ko cikin Daga Sautinsa yace"Man Rabbuka?
Ya fad'a ya na mai kallon Innani kai Tsaye, Innani ta fara kyafta kyafta idanuwanta ta cikin gilashinta ta kasa mgana.
Cikin Karin d'aga Sauti Sadiq ya cigaba da fadin"Man Rabbuka wanene Ubanginjinka?
Rabiyalahul Lazi halaQani, Warrabani bini'imatihi_ Ubangijina shine Allah wanda ya Halliceni, kuma ya reneni da ni'imominsa.
Bi'aiyi shai'in Ta'arufu Rabbuka?
Da wani alamomi ka ke sanin Ubangijinka? Aarufu Rabbi alamatil kasira, _ Ina Sanin Ubangijina da alamomi masu yawa, minal laili wannahara, Wa shamsu walqammar, Daga cikinsu akwai dare da yini,da Rana da wata.
Man Halaqa samawati wal ardi, wa shamsu walqamara, Wanene ya hallaci sammai da kassai? Sannan da rana da wata?
Alllah Shine wanda ya hallici kasa wacce muke tafiya acikinta, kuma ya Hallici sama wacce take sama, kuma ya hallici wata da Taurari wa'inda suke cikin sama kuma ya hallicci mutane da duwatsuna, da itatuwa da dukkan komai, Allah shi ya ke saukar da Ruwan sama kuma ya ke azurta bayinsa, kuma ya ke ba su lafiya, kuma shi kad'ai yafi chanchanta da mu bauta masa."
Ya na kawo nan ya dakata ya na kallon Innani tare da Fuskokin mutanen da ke falon. da alamu jikin kowa ya yi sanyi sannan an natsu ana Sauraransa.