← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 75

Sashe 57

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Wani office muka shiga tace na zauna saman wani karamin gado, na zauna a darare ina kallon yanayin Office din, Sirinji naga ta na had'awa sannan ta zo da wani igiya na Roba tace na bud'e Hannuna na Dama  na bude na mika mata ta rike, sai ta Dauremin hannu da wannan igiyar, sai ga jijiyo sun bayyana a guda daya ta soka alluran ta zuki jinina sai da na Runtse ido saboda naji zafi, ta cire ta na min sannu, auduga ta sakamin a wajen tace na rike saboda Tsaida jinin.
Na ko rike wajen gam saboda tun farko ni ba na son ganin jini sosai haka a gabana.
A zato na an gama ammh sai naga ta fita tace min bari tazo ba Dad'ewa sai ga shi ta dawo da wata kwalba karama sai sirinji a gabana ta fasa kwalban ta zuga mganin cikin Sirinji, na zata wani abun zatayi sai naga ta kara nufoni cikin mamaki na bita da kallo ganin haka yasa ta na mirmishi tace"Allura tsaida jini zan yi miki Tunda naga kamar jinin bai Tsaya ba ne"
Sai na Dukar da kaina ina daga audugan da ke hannuna naga jinin kad'an ne, sai na Dago ina kallonta Lokaci d'aya ina fadin"Ai jinin kamar ya Tsaya"
Cikin Sauri tace"To ai har da na Rage radad'i ko baya miki zafi wajen?
Kamar wata gaula haka na gyada mata kai sai ta min mirmishi kafin tace"To bari na yi miki yanzu zaki daina jin zafin"
Ban gama mamaki ba naga ta yaye min Hijabi ta ce na gyara a Duwawu zata yi min ni dai kamar an dinkemin baki haka na mike na bata baya na ta d'an ja sikat dina kasa ta tsiramin alluran nan sai da na yi yar kara.
Sai ta farablilayamin wajen ta na fadin"Sorry sorry Madam.."

Ni dai nasan na koma na zauna sai kuma daganan na fara jin kaina na Juyawa, Ina ganin Nurse din ta fita ta dawo da wani abu Hannunta ta kariso kusa dani har kuma bayan ita naga wasu sun shigo dakin ammh bazan iya tantance fuskokinsu ba.
Daganan ban kara sanin inda kaina ya ke ba sai misalin karfe Biyar na yammah.
Na farka na gani kwance kan gado ba Hijabi a jikina sannan a gefen hannuna na Dama a wajajen Damtsena an sakamin Bandage an Rufe wajen, ina kokarin mikewa kaina naji ya saramin saboda yadda naji gabadaya jikina kamar ba nawa ba.
Cikin tashin hankali na koma na kwanta ina mai Dafe kaina Lokaci d'aya ina fadin"Wash kaina."

"Sannu Siya kin ta shi? Are u ok?
Muryan Assadiq na ji a gefena da Sauri na juya ina kallonsa bansan ko yaushe ya shigo ba, ban kuma san ko Daman ya na cikin Dakin ba.
Na kasa mgana sai shi ne ya kariso ya Rike hannuna mai lafiya ya na kara min sannu.
Cikin mamaki na kallesa kafin nace"Me ya same ni? Jinin ne bai Tsaya ba?
Ina kallon cikin idanuwansa na yi mgana ammh shi sai naga ya kauda kansa cikin Dashewar murya yace"Ya kike jin jikin ki yanzu?
Cikin karin mamaki na bi sa da kallo, da Sauri na yi kokarin tashi, sai ya Rikeni ya tadani har ya na fad'in"Ki yi a Hankali kada ki fama Hannun ki."
Sai a lokacin na Tuna da Raunin da naga an lullubeshi da Bandeji.
Cikin karin mamaki na kara kallonsa ina fadin"Me ya faru dani? Me ye wannan a hannuna? Na ji ciwo ne ko?ina jin hannun ya yi min nauyi sosai."
Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Ki yi hakuri Nurse ce tace kina zaune saman gadon nan sai gani tayi kin fad'o, ashe fad'uwar da kika yi Allura ta cake ki a hannun ki, kuma wajen ya yi rami sosai sai da aka yi Dinke shine Dalilin da kika ga an saka miki Bandage kenan."
Ina so na kallesa yaki bari mu had'a ido, ni abunda na ke so na tambayesa yaushe na fado daga saman gadon? Sai na shiga Tunanin abunda ya faru ammh na kasa tuna komai
Ina shirin kara mgana sai ga likitan ya shigo ya dubani ya na min sannu.
Har ya na fadin"Sory Madam ina ke miki ciwo?
Cikin sanyin murya nace"Kai na sannan ina jin kasala."
Sai ya juya ya na kallon Assadiq kafin yace"ba zata yi aiki da hannunta na Tsawon kwana uku ba, kada ka Damu zan baka mganin da zarar ta sha kan zai sauka sannan zata ji dadin jikinta."
Assadiq sai ya jinjina kansa kafin yace"Ka tabbata ba matsala Dr?
Dr. Yace"In sha Allahu kada ka damu."
Ni dai bakina ya yi nauyi na kasa mgana ma har Assadiq suka fita da Likita ba jimawa ya Dawo.
Shi ya taimakanin na saka Hijabina da takalmina muka fito.
Nures na ta yi mana sannu ina ta wurga ido ko zan ga nurse din da dibi jinina saboda ina so na Tambayeta garin yaya na fad'o daga saman gado? Abun kamar hankali bazai Dauka ba.
Sai da muka jira Assadiq ya karb'i wasu Takardu guda biyu da takardan mgani, sannan muka fita ya na rike da Hannuna har bakin Titi muka samu adaidaita sai gida.
Muna zuwa shi ya shiga dani har daki ya na rike da Hannuna kuma muka ci sa'a ba kowa a tsakar gidan.
Ni dai gabadaya jikina da kaina baya min dadi kwantar da nayi ya yi yace na bari ya fita yanzu zai dawo.
Ya d'an jima sai ga shi ya Dawo da ledoji abinci ya siyomana jallop din shinkafa da kaza sai madaran Holladian mai sanyi.
Bakina takaf naji ya yi min sannan hannuna naji kamar ba nawa ba.
Ganin nace ba zan ci ba yasa ya Dagani cak ya Dora saman cinyarsa ya shiga bani a baki sai da na koshi.
Gabad'aya fa na koma sai yadda ya yi dani Tunda kasalace ta Rufeni.
Shi ya tattara komai zuwa kitchen ya kaini Tiolet yace zai min wanka.
Na bude baki na Rufe na kasa mgana.
Wai saboda kada na Fama Hannuna.
Sai ga shi ya zage ya yi min wanka da Ruwan sanyi sai dai sun yi Dumi Tunda suna cikin bayi ne.
Kunyar duniyar duk suka kamani ammh shi ko ajikinsa.
Ya sani na Dauro alwala ya Daukoni cak a jikinsa ya kawoni kan gado.
Shi ya shafamin mai,ya kuma sanyamin kaya sai dai na lura kwata kwata baya son kallon cikin Idanuwana.
Saboda an riga an tada sallar a masallatai yasa bai je masallaci ba ya yi a gida ni kuma yace na yi a zaune in bazan iya Tsayuwa ba.
Hakam kuma na yi bayan na rama azahar da la'asar din da suka Kubcemin sai na yi mangariba.
Ranar ko Kofi bai bari na Dauka ba shi ya Dinga tarairayata.
Dakyar na iya jiran sallar ishai ina idarwa sai barci Sai da asuba na tashi Lokacin da naji ya na shafa Fuskata da Hannunsa mai Dauke da Danshin Ruwa.
A iya kimanin kwanaki ukun da Likita yace na Huta Assadiq shi ya rika yin komai, kafin ya fita wajen aiki har shara sai ya yi, sannan ya sama mana abun karyawa in kuma zai Dawo ya Taho mana da Takeway.
Ranar kwana na hud'un da na Dage ni zan yi wanka da kaina Tunda na daina jin kasalan da ciwon kai, tunda ya bani panadol na yi ta sha.
To a wajen wankan ne bandage din ya  cire kansa, na dade ina mamakin Hannuna Domin naga wani waje a dantse hannuna inda ke da tsokar nan ya yi wani abu a wajen.
Kamar dai wani abu ya shiga wajen, sai dai na watsar da wannan Tunanin ne da Tuna ance har Dinki an yi min sai nayi Tunanin shaidar dinkin ne.
Sai da na fito ne na nuna masa wajen ya Duba sosai sannan ya kalleni kafin yace"Ba ya miki zafi ko?
Kai na gyad'a masa, sai ya yi mirmishi kafin ya sauke ajiyar rai.
Bai gwadamin takardan gwajin ba sai da Daddare ya nuna min kuma ya yi min bayami.
Yace Blood group dina ONegative ne sannan Gytoype dina AA ce.
Shima ya ce min Bood groups dinsa O ne, Sannan Bangaran rukuni kuma AS ne shi.
Ni duk ban wani gane nufinsa ba ma ammh sai na nuna masa na gane kawai  bayan na tambayesa me ye amfanin shi gwajin da muka yi?
Kai Tsaye yace min"Saboda tseratar da kan mu da haihuwan ya'ya masu Dauke da wasu cutuutuka."
Sai na gyad'a masa kai alamun na gane.
Cikin Satin nan haka ya rika ji dani kamar Tsoka d'aya a miya, Ba mu sake fita ba sai da Sati ya zagayo yace na shirya muje yawo mu mike kafa, ban taba Tunanin cewa Assadiq ya shiryama Daran Ranar ba. Sai da muka zama Daya sannan abubuwan da suka faru suka fara zuwa kaina.
Kofar doka muka je ya siyo mana gasassun kaji guda biyu da kayan Fruit, sai kuma madaran Holladian har ina masa mganar sai ya yi ta kashe kudi wajen siyan kayan kwalama.
Sai kawai ya yi dariya yace min"Anthing for u my Wife."
Mun dawo gida shi ya ciyar dani nima na Ciyar da shi, cikina har sai nace masa ya cika sannan ya kyaleni.
Sai dai bai tsawaita Daren ba yace muje mu kwanta Tunda tare yanzu muke kwana.
Ya matsamin sai na kara yin wanka ni ko na so na bi lafiyan gado saboda nagaji.
Ammh sai ya hanani sai da na yi wankan nan na samu zaman lafiya shima ya shiga ya yo wankan.
Koda ya fito har na kwanta kawai sai ji nayi ya Dagoni cak sai kasa ya Saukeni ya na kallona yace"Sallah zamu yi?
Ina fiki fiki da ido nace"Sallar kuma?
Kai Tsaye yace"Shafa'i da Wuturi ai bamu yi ba."
Nasan in nace wani abu bazai yarda ba yasa ina Tura baki na koma tiolet na Dauro alwala koda na fito har ya saka Jallabiya ya shimfid'a sallaya.
Sai kawai nima na saka Hijabi na bi bayansa.
Mun yi raka'a Hudu a rarrabe sannan ya yi mana addu'a sosai.
Na Dauka da ya rikeni ya fara Sumbatata ire iren wasaninsa ne da ya sabarmin sai nima na Saki jikina ina ba shi had'in kai.
Ashe Assadiq ya sauya Tunani a kaina, ni dai na san ya daukeni sai kan gado ya kuma yi min Rumfa da Faffadan kirjinsa da babu komai da ya yi mana shamaki.
Ni kaina yar rigar barcin jikina ya cire min ita fatarmu na gogan juna zukatan mu na Fitar da wani Sauti.Ras! Ras!.
Ban taba Tunanin Assadiq namiji ba ne ne sai da ya maidamu abu d'aya sannan na kara jinjina mganar nan ta Hausawa da suka ce maza suna suka Tara.
Ban ko sha wani abun gyara ba, na dai san ina shan Fruit da madara sai abun mai kyau sannan Hankalina na kwance inaga shi ya taimaka wajen kara ma Assadiq kaimu wajen samun Biyan bukata daga Jikina.
Kusan mintina arba'in sannan naji ya kamkameni ya na fitar da wani Sauti mai kara, ni ko na yi wani yaraf ina jin gabbaina duka sun saki wlh naji azaba daga kasana domin rabona da Namiji Tun Abubakar, Salisu dai bamu kai ga ma wannan Sharad'in ba.
Shi ya fara tashi yaje ya Tsarkake jikinsa sannan ya zo ya na tashi na, kunya suka sani na kasa tashi, ganin haka kawai yasa ya yi dariya ya fita falo shi ya bani damar tashi da Sauri ina Raruman Hijabina na fad'a makewayi na yi wanka.
Ina wanka ina Runtse ido sannan ina Mirmishi, ni kad'ai ko sunan Assadiq na tuna acikin raina sai naji jikina ya yi min wani iri.
Ashe kowata mace na Bukatar Sinadarin d'a namiji a tare da ita bansan haka ba sai da na kasance da Assadiq a wannan daran sannan na kara Tabbatarma da kaina Cewa Nima ina Bukatar Namiji.
Har na fito na sauya rigar barci na kwanta bai Dawo dakin ba sai chan naji Shigowarsa.
Sai nayi kamar ina barci ina jinsa ya hayo gadon ya lafe a bayana Lokaci daya ya Rumgumeni.
A cikin kunnina ya ke min Rad'a cikin Sanyi da wani salama a muryansa yace"Nagode Siya. Yadda kika farantamin a wannan Daran kema Allah ya faratamiki kin ji ko?
Kin motsi na yi sai ya fara min cakulkuli ai sai na bangare ina Dariya.
Kunyarsa nake ji shi kuma ya san haka sai ya kyaleni ya koma ya kamkamni ya na sauke Numfashi.
Ni na samu barci ammh shi ya kasa sai Tunane Tunane ya ke yi.
Salama da natsuwa yake ji suna Shigarsa duk da farko shed'an ya so ya yi masa wasa da kyakyawan niyarsa.
Shed'an na fad'a masa ta yi aure aure wasu sun rigasa sanin inda ya ke son sani yanzu.
Ammh tunda ya kasance a wajen ya ji ya daina wani kokwanto Hasiya ta zama shi, shima kuma ya zama ita na Har Gaban Abada.
Chapter 57 · 0% Book details