← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 75

Sashe 69

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jin haka yasa tace to mu tafi mun yi sallama da Hajiya Murjanatu tace kafin mu tafi mu shiga mu gaishe da Babanmu tunda hayaniyar Daurin aure bai sa ya san da zuwan mu ba.
Ni dai har ga Allah ban yi niyar zuwa ba ammh bani da mafita.
Abun mamaki tare da ita mukaje bai ganemu ba sai da ta yi masa bayani sannan ya ganemu ya dago ya na kallonmu kai Tsaye yace"To to cikin ku wacece mai kashin Tsiyan nan ne?
Sai Adda Fati da Adda Rukayya suka kasa magana.
Hajiya Murjanatu tace"Haba Abban Zahara'u wannan wani irin mgana ce?
Kai Tsaye yace"Maganar gaskiya ne Murjanatu akwai mai kashin Tsiya acikin su ko ba da ita kuka zo ba ne?
Kaina na kasa na kasa mgana ammh naji wani abu mai daci ya Tokaremun zuciya.
Ganin su Adda Fati sun kasa mgana yasa na dago ina kallonsa nace"Ni ba ni da kashin tsiya, ni Mutum ce kamar ka  kuma Baiwar Allah da ya Halliceni tare da Ni'imominsa."
Sai shima ya Tsaya ya na kallona kafin ma ya samu zarafin mgana naja jakata na fice daga falon ina kokarin maida kwallata.
Ko ajikinsa sai ma ya zakud'a kafad'a kafin yace"ance ta yi aure kwanaki in ji dai shima mijin bata nakasa shi ba ko?
Adda Rukkaya tace"Suna zaune lafiya."
Sai ya yi mirmishi kafin yace"Dakyau, Ina ita mahaifiyar taku? ko ta na chan garin na su ne da akace ta koma?
Adda Fati tace"Eh ta na chan tace a gaisheku da Fatan Allah ya ba da zaman lafiya"
Cikin jinjina kai yace"Ameen ku gaida Gida"
Da haka ya Dauki wayarsa da ake ta kira tun dazu.
Su Adda Fati suka fito jiki a mace Hajiya Murjanatu ta rasa ina zata saka kunyarmu.
Su Adda Fati ne suka Tsaya tabasu abun Rabo na jaka da kofi sai kayan Fulawani ni a bakin Titi muka had'u da su, kuma har muka isa tasha muka Hau mota ba mu yi ma juna magana ba.

Gidan Adda Fati muka sauka ni da ya ke ba na sallah ban Tsaya ko cin abinci ba na had'a kaya na wuce gida nace naci achan, ba su hanani ba ganin yanayina sai da na koma gida naci kuka na har na godema Allah.
Sai da yammah Saliha ta kirani tace ga su sun zo gidan ba ta ganni ba.
Murya a chunkuse nace mata mun Dawo Zariya tun dazu.
Jin muryata wani iri yasa tace lafiya? Ni kuma sai na ce mata ina Mura ne fatan samun sauki ta yi min tace suma sai gobe za su koma Gusau sauran ne da za su zo daga gusau mota ta lalace musu a hanya sai da yammah suka iso.
Fatan sauka lafiya na yi musu sannan muka yi sallama.
Na zauna na yi ta Tunanin inda mutanen da na had'u da su a kaduna suka min kama da wanda na sani ammh na kasa ganewa.

(Da ya ke Yan gidan su Assadiq ba su da mugun kama da juna, Gwara ma yan Dakin Mama ita suke Debo suna yanayi da juna akan dakin Umma Sadiq ne ma ya ke kama da Surayya kamar kwabo da kwabo).

Sai a daren muka yi mgana da Assadiq shima dai ji na wani iri sai da ya yi mgana sai nace masa mura ne. Sai yace kila iskar Mota ce tunda na gayamssa tun dazu muka dawo.
Matsamin ya yi na siya magani na sha na kwanta na amsa masa da toh.
Washegari dakyar na iya rarrafa jikina na yi share share tunda dakin ya yi kura jikina nake jin ya na min wani iri sannan Jinin da na ke yi a kallah kwana Biyar sai ga shi har Sati bai Dauke ba.
Sai na fara Tunanin kamar ba lafiya ko shi ya ke sakamin kasala ban sani ba ko abinci na rage ci da ga Tea da Safe sai Dare na Dafa Indomie.
Yau din ma Tea na sha da Safe zaman kadaici ya isheni mun yi waya da Safiya Ahmad da Safe tace mun kusa komawa makaranta.

To daman Assadiq ya bar min karamar Computer dinsa Saboda makaranta shi kuma sai ya siya Sabuwa kuma da ya ke muna yi a makaranta sannan shima ya Koyamin sai ya kasance na iya Sarrafata yanzu.
Duk da ya maida komai na shi cikin Sabuwar da ya siya bayan ya goge komai aciki fina finai Kawai ya barmun sai karatun Qur'ani.
Sai ni kuma na saka Safiya da ta zo ta Turamin Abun karatun mu na Computer aciki.

Tunda aka yi Hutu ban Daukota ba, kallo bai wani Dameni ba sai in Assadiq na nan ne mu yi tare, in kuma baya nan sai dai na gaji da danna waya ko na yi barci karatun Novel din ma da na fara yanzu na Daina bani da juriyan karatun ne kwata kwata.
Na Dauko na kunna kenan sai hannuna ya kai kan wani Draft da aka saka SSSHINKAFI a jiki ban taba Lura da wajen ba.
Ko sanda Take na Assadiq ba ko'ina ya ke shiga a gabana ba, wasu app d'in ma duk sai da ya san ya musu pin in ba shi ba, ba wanda zai iya shiga ciki.
Kamar wasa sai na Shiga sai naga Wani Hoto ne guda daya a wajen akwai alam ya makalene ba'a goge shi duka ba.
Kamar bazan shiga Hoton ba sai na Danna sai ga Hoton ya bayyana.
Hoton da sai da ya sa na tashi da Sauri Cikin kif kifta idanuwana na mamaki da Al'ajabi.
A cikin Hoton naga mata Biyun da na gani a kaduna, sannan har da Saliha aciki da yaran matan da ta nuna min Siyama da Sultana.
Sai wasu kuma da sun kai su goma sha a Hoton sun saka kaya iri daya na wani bakin leshi da Fari, sun saka Assadiq a tsakiya shima cikin Fararan kaya harda babban Riga.
Sai dai fuakarsa ta yi karama a Lokacin kamar Hoton ya jima ko wani sha'ani ko kuma sallah ne aka yi wannan Hoton.

Na gefe da gefensa sun Dafashi gabadayansu suna dariya ga Fararen Hakoransu nan a bayyane da Mirmishi da Fara'a sai gashi na samu kaina da Kara zooming din Hoton domin na kara Tabbatar ma da kaina abunda na gani shin gaskiya ne ko ni ce ban gani Daidai ba?
Sai ga shi na kara tabbatar ma da kaina abunda na gani zahiri ne acikin wannan Hoton.
Sai da na kara kura ido sai na samu amsar kokwanto na tunanin da waye sukamin kama?
Ina ganin Fuskarsu yanayi da na wanda na sani to ba kowa ba ne face ASSADIQ.!
Na dimuace sannan na shiga wani yanayi da Tunanin su waye wad'anan a wajen Assadiq? Wani lungu daga zuciyata ta bani amsawa da cewa"Ba sa wuce Yan'uwansa."
Sai kuma na ce a fili to ai yace ba shi da kowa sai kakarsa to wad'anan fa a ina ya same su?  Kamar ana min Wahayi naji bakina ya furta"Kenan Assadiq ya yi miki karya ke da yan'uwan ki."
Chapter 69 · 0% Book details