← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 75

Sashe 33

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shi dai yasan ya sauka a tasha kuma ya samu mashin zuwa anguwansu.
Bayan mai mashin ya saukesa ya biya shi kudinsa sannan ya dauki Jakarsa da ya zubo sauran kayan da ya ke son ya kyautar da su in zai koma sai ya tafi da wasu daga gida.
Jikinsa ba kwari ya karisa jikin get din gidansu ya kwankwansa.
Mallam Tajudeen ya zo ya bude karamar Kofar ya na ganin Sadiq ya washe baki ya na fad'in"Yallabai barka da zuwa."
Ba wannan Annurin da zumud'in a Fuskar Sadiq yace"Mallam Tajudeen na same ku Lafiya?
Ya amsa masa Lokaci d'aya yana kokarin karban Jakar hannun Sadiq.
Shi kuma sai ya hanashi ya na dan mirmishi yace"Har gobe ni d'alibinka ne kuma mai biyayya a gareka."
Ya na fad'in haka ya sawo kansa cikin Haraban gidan.
Sai dai me? Gabansa ne ya yanke ya fad'in hango Abba da ya yi a haraban gidan Jingine jikin Motarsa.
Yana sanye da Shadda har da babban Riga waya ya ke yi, sai faman daga Hannu ya ke yi lokaci d'aya ya na ta saba hab'an gefe da gefem Babban Rigansa.
Kunya da wani irin nauyin jiki da na zuciya suka lullube Sadiq da ya sa kafafunsa suka kasa daukansa zuwa ga Abba.
Cak ya tsaya ya kasa gaba ballatana baya sai kawai ya zabi ya tsaya domin ba shi da karfin gwiwan fuskanta Abba a daidai lokacin da yasan ya ci Amanarsu ya aikata babban al'amari batare da saninsu ko amincewarsu ba.
Mallam Tajuddeen ya daga Murya ya na fad'in"Alhaji ga Magajin gida ya iso fa."
Abba da ke waya yaji sanda Mallam Tajudden yace ga magajin gida ya iso.
Da Sauri ya juyo ya na kallon Sadiq cikin wani yadi mai ruwan kasa shara shara har ana ganin shatin Vest din jikinsa.
Sai dai ya na tsaye kansa a sunkuye kamar wanda ya yi ma Sarki karya.
Da sauri Abba ya ba ma Alhaji Jibril hakuri da fadin"Mu yi mgana anjuma Alhaji magajin gida ne ya iso yanzu."
Dagachan bangaran Alhaji Jibril yace"Au ya dawo ne? Shine ba Labari Alhaji?
Abba ya yi dariyan jin dadi lokaci daya ya na kallon Sadiq yace"Kasan halinsa zuwan bazata ya ke mana ni kaina jiya mun yi waya da shi, ammh bai Sanar dani yau ya na tafe ba, ba ri na gansa zan kiraka."
Daga haka ya katse kiran cikin Sauri ya fara takawa wajen Sadiq ya na Fadib"Abubakar..!"
Dalilin da yasa ya dago kenan shima ya fara takawa zuwa wajen Abba suka had'u da Sauri Sadiq ya rankwafa ya na gaida Abba shi kuma sai ya Rumgumosa ya na fad'in"Maraba da magajin gida maraba da Shalelen Innani."
Mirmishin ya ke Sadiq ya yi ya na kokarin kara sunne kansa yau dai Abba ya zama Surukinsa.
Shi ko Abba bai ma lura da shi ba Rikesa ya yi ya na fad'in"Shine baka gayamin yau zaka dawo ba? Da ka fadamin da na tura maka Direba ya Dauko ka."
Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Abba shiyasa ban gayamaka ba, meyasa da girmana sai na saka an bama wani wahala ya tashi daga Gusau zuwa zariya kawai domin ya Dauko ni?
Abba yace"Ka isa ne kada ka manta kai magaji ne kuma shi Magaji ya na da komai."
Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba ammh a ransa fad'i ya ke yi a gusau Sadiq ya ke magaji a zariya kuma Abubakar ya ke.
Dafa kafad'arsa Abba ya yi kamar wani abokinsa sannan Lokaci d'aya ya karbi jakar hannun Sadiq ya na fadin"Ina Attahiru?
Sadiq yace"Ya wuce Daura Abba."
Abba ya jinjina kai ya na fadin"Allah Sarki."
Sadiq ne yaga Abba na jansa zuwa Shashen Umma yasa ya kallesa ya na Fad'in"Abba ba fita zaka yi ba?
Abba yace"Masallacin jumma'a zani Direba na ke jira yaje Dauko yara nan daga makaranta."
Da Sauri yace"Abba to bari na shirya sai na tuka ka muje ko?
Kallonsa Abba ya yi Lokaci d'aya ya na bubbuga kafad'arsa kafin yace"Da zan so hakan Magaji."
Sadiq zame jikinsa ya yi daga na Abba Lokaci d'aya ya na karban jakar kayansa ya na fadin"Bani minti goma Abba."
Ya fad'a ya na wucewa bangaransa, Abba ya bi shi da kallon kaunar da Allah kad'ai yasan iyakarta Tsakaninsa da Sadiq.
Ya na da makulin Shashensa tare da key din dakinsu na zariya ya had'a waje daya ya na jin shashen a Rufe ya Dauko key din ya Bude ya shiga.
Ko'ina Tsab kamar ya na nan ya Tabbata kullum ake gyara masa bangaransa Saboda Halinsa na zuwan bazata.
Kayan hannunsa kawai ya ijiye ya shiga wanka saboda kada Abba ya gaji da jiransa.
Abba ko Umma ya shiga kwalama kira daga Haraban gidan da karfi"Salamatu. Salamatu.."
Da sauri ta fito a firgice ba ita kad'ai ba Hatta Mama itama sai da ta fito.
Dukkansu a tsorace har suna had'a baki wajen fad'in"Alhaji lafiya?
Ya na mirmishi jin dadi yace"Magajin gida ne ya dawo"
Umma ta washe baki ta na fad'in"Auta na? Ya na ina?
Abba ya nuna mata bangarensa da baki ya na fadin"Ya shiga ciki ya shirya yau tare zamu tafi masallacin jumma'a."
Umma ta saki kayattacen mirmishi kafin tace"Auta ya kyauta ya dawo Lokacin da gidan gabadaya ya yi kewarsa."
Abba yace"Barin ma Innani ko jiya sai dai tace wai magajin gida ko lafiyarsa lau? Sulaimanu bazaka je ka duba mana shi kagani ba."
Umma ta yi dariya kafin tace"Ina ruwan Innani."
Mama na gefe karamin Tsaki taja a ranta ta na mamakin yadda suka Damu da yaron da bai damu da ya zauna da su ba.
Ta na jin haushin yadda Daga Umma har Abba basa iya boye kaunar Sadiq ko a gaban waye.
Ballatana Innani da zata iya yin komai a kan Sadiq ciki har da Tozarta sauran ya'yan gidan gabadaya.
Suna nan Tsaye sai ga jar mota kirar Vibe ta shigo gidan Direba ne ya Dauko su siyama daga makaranta.
Motar na gama parking a Haraban gidan suka Firfito.
Siyama ce kan gaba Sai Sultana kowacce dauke da Jakarta.
Salima kuma na baya ta na yaukinta da ta saba.
Wajen su Abba suka karisa ganinsu dukkansu a haraban gidan kamar wani abu ya faru.
Direba ne ya kariso ya rankwafa Lokaci d'aya ya na fadin"Yallabai ka yi hakuri mun samu cunkoso ne a hanyarmu ta dawowa.".
Abba ya saki kayattacen Mirmishi kafin yace"Kada ka damu garba Magaji ya dawo tare zamu tafi masallacin"
Garaba ya washe baki ya na Fadin"Maraba maraba ina yi ma magajin gida maraba da dawowa."
Siyama ta ware ido ta na kallon Umma kafin tace"Umma Yaya Sadiq ne ya Dawo?
Umma ta gyad'a mata kai ta na yar Dariya ,Tsalle ta daka kafin ta saki ihu ta juya ta na fad'in"Sultana Yaya Sadiq ya dawo wayarmu tazo."
Mirmishi kawai Sultana ta yi mata ba ta yi mgana ba.
Salima ce ta saki tsaki kafin tace"Yara sai kun shiga SS2 ko za'a siya muku waya"
Siyama ta balla mata Harara kafin tace"Ina ruwanki damu? Ke ai kina SS1 a ka siya miki, kuma lokacin muma bamu yi mgana ba."
Salima da Saurin harzuka ta kalli Abba ta na fad'in"Abba ka ganta ko? Rashin kunya zata min"
Abba na Dariya yace"Siyamar Abba ki kyale Salima kin ji ko? Yayanku zai siya muku waya in sha Allahu kafin ya koma."
Mama ta tabe baki kafin tace"Ku wuce ku je ku cire kaya ku huta ko?
Suka amsa mata da Toh.
Sultana ce a baya su kuma sun yi gaba suna Rigimansu na sako zuwa Shashen Mama ita kuma ta nufi bangaran Umma.
Daidai Lokacin Sadiq ya fito ya na kokarim saka links din Rigar shaddar da ke jikinsa mai ruwan Dark Blue dinkin zamani da Hula kube wacce ta hau saman aikin kayan sannan kafarsa cikin Budaden Takalmi Kalan brown sabo ne yau ya taba saka shi sannan agogon Hannunsa ma Brown ne na Fata mai kyau da yarari.
Chapter 33 · 0% Book details