← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 75

Sashe 31

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habibu ya dinga lallashinta da ta kwantar da Hankalinta ba abunda zai faru sai Abunda Allah ya so.
Za'a bincika har chan shinkafin domin a san ko waye shi ammh yanzu dai Hasiyan ta fara matsamai sai ya kaita garinsu tasan Yan'uwansa.
Da wannan shawaran na Baban su Hanifa ta kirani da Safe ta na gayamin na matsamai sai ya kaini chan Shinkafi na had'u da Danginsa.
Ni dai sai na bita da toh kawai bani da wani zabi sai dai ta yadda zan yi masa mganar ne na rasa yadda zan yi.
Kada yaga kamar na nuna zakewata da yawa ne.
Adda Fati sai ta yi karambanin kiran Adda ta sanar da ita tunanin da ta yi Adda kuma ta bata goyan bayan cewa ya kamata a bincikan aure ba mganar wasa ba ce kuma tun farko da Amma ta yi shawara da ita baza'a yi auran nan sai su san waye Abubakar da abunda ya Dangancesa gudun auran wanda bai dace ba.
Adda ce bayan sun gama mgana da Fati ta sanar da Amma komai da kuma yadda Adda Fati tace Hasiya zata matsa masa ya kaita chan shinkafi in ya nuna ba yanzu ba sai a tada wani yaje chan ya bincika ya gani.
Amma na jin haka ta saci idon Adda lokacin da ta shiga makewayi ta kirani a waya ta gargad'eni kada na sake na matsama Abubakar kan maganar sai ya kaini garin su domin naga yan'uwansa na bari in har shi da kanshi ya yi min maganar sai na shirya ya kaini.
Cikin mamaki nace"Amma me yasa? Ai ya na da kyau nasan komai game da shi"
Cikin kaushin Murya Amma tace"In lokacin da yakamata ki sani ya yi zaki sani Hasiya. Kada ki matsa ma kanki kan sanin abunda ba'a so ki sani ba. Zaki iya zuwa kisan abunda zai iya hana ki zaman lafiya ki jira shi Lokaci da ya so ki san komai a kansa shi zai sanar da ke da kansa."
Da wannan kalaman Amma ta katse wayar ta barni sake da baki sai maganganunta suka sarkeni na kasa gane inda ta dosa.
Me ta ke nufi da cewa kada na matsama kaina da son sanin abunda ba'a so na sani ba? Ko ta san wani abun da mu bamu sani ba ne?
Ita ko Amma ta yi hakane saboda d'inke wata baraka abunda Fatin ta saka Hasiya ta yi gaggawa ne kuma shi gaggawa aikin shedan ne in a auransu gaggawa ya shiga bai kamata a zaman su kuma gaggawa ya shiga ba, a bi komai a sannu in sha Allahu alheri ne zai faru sannan kuma zai faru a yadda Ubangiji ya Tsara Faruwarsa ne.
Maganar Amma yasa na binne mganar acikin raina na kuma cire yakinin ko Assadiq ya zo bazan masa mganar Ahalinsa ba, na bi mganar Ammaa zan jira lokacin da ya kamata na sani zan sani.
Ranar asabar aka kawo Amarya kusa da Dakin Ummi mai suna Fadila.
Yar cikin samaru ne a irin gidajen ma su kudin anguwan.
Fadila irin yamatan ne ma su kaud'i da Son karya sannan ga fariya da wulakanci tare da renin arziki.
Mijinta ma'aikaci ne a CVN a Abuja ya na gini bai gama ba ne yasa ya kama Haya kafin ya kamallah gidansa.
Fadila Farar mace ce Doguwa mai jikin mata ta na da kyau irin kyau mai Daukan ido sosai, iyayenta ma su kudi ne shiyasa kayan Dakinta ma sun taka na Ummi a komai da komai.
Tun ranar litini da Daddare da muka shiga ni da Ummi ganin Daki na tabbatar ma da kaina Amarya Fadila bata karb'eni ba.
Fuskarta ba Fara'a ta amsanin gaisuwa sannan ta na ta min kallon kasa kasa a wulakance.
Ammh ta amsa ma Ummi cikin Sakewa ko ma daga ganin yan'uwanta duka Dakin Ummi suka yi mu'amalansu kafin su watse na Fahimci wani abu.
Wannan rayuwar kwarya tabi kwarya ne in kana da shi sai ayi da kai in baka dashi kuma kai da banza duk d'aya ganin haka yasa ban kara shiga Dakinta ba.
Kuma ta shiga Dakim Ummi sannan ta bata Su kayan Fulawa ammh ni ko abunda ba'a so bata bani ba.
Ummin ce ma ta sanmin a nata sai ta boyemin da cemin Fadilan ce ta had'ama waje d'aya tace ta dibarmin aciki.
shuru kawai na yi mata ammh mganar gaskiya ko a fuska wanda ya ke yi da kai zaka sani.

*****

Har su Sadiq suka samu Hutu bai samu Sararin kara komawa wajen Hasiya ba sai ranar da zasu tafi.
Tahir zai wuce Daura shi kuma zai tafi Gusai.
Da safe sun gama shiryawa duk da ya na kiran Hasiya a waya lokaci bayan lokaci yana jin lafiyanta yasan bai kamata ya tafi batare da yaje ya ganta ba tunda zai jima kamar wata daya haka kafin su dawo.
Ya rasa wata karya zai ma Tahir ya samu ya je ya dubata sai dakyar ya samu karyan zai je ya ciro kudi yanzu zai dawo sannan ya samu ya yi wuf ya fita yaje ya hau mashin.
Da misalin karfe 9am na safe na Ranar jumma'a ya kwankwansa ma Hasiya kofa.
Ina cikin barci naji ana Bugun kofa sai kuma kasala da barci yasa na kara komawa sai kuma naji wayata na Ringing cikin barci na lalubota kasan Filo ban ko Duba mai kiran ba kawai dauka na yi na saka a kunne.
Sanyin muryansa ce ta Dake ni sanda ya ke fad'in"Ina kofar dakin ki."
Da haka ya katse wayar ai sai na wartsake na Diro daga kan gado da Sauri dagani sai rigar barci tun ta gida ce duk taji jiki sai na Rarumi Hijabi na saka sannan na fito nazo na Bude masa kofar dakin lokaci daya ina Murza idanuwana.
Yana Tsaye kofar d'akin sanye da Riga da wando ma su ruwan kasa ya sanya Jaket baka a saman kayan sannan hannayensa suna cikin Aljuhun wandonsa.
Na fahimci ya na son tsarin wannan Shigar sannan koda wani Lokaci yana jin dadin sanya hannayensa cikin Aljuhun wandonsa.
Hanya na ba shi Lokaci d'aya ina fad'in"Sannu da zuwa."
Ba amsa ba sai da ya shigo ciki sannan yace min yauwa.
A tsakiyar falon muka Tsaya bai ko Zauna ba ya juyo ya na kallona.
Ni kuma ina shirin juyawa zuwa kitchen ko ruwa na kawo masa a tunanina daga tafiyar suke yanzu suka shigo garin

"Hasiiyaa."

Sai naji ya kirani cikin Taushin muryansa tsayawa na yi kafin na juyo ina fad'in"Na'am!
Kai tsaye yace"Dawo nan gaba na."
Ba musu na dawo gabansa na Tsaya ammh kaina na kasa ina wasa da Hijabin jikina da Hannayena da ke cikin Hijabin.
Na wani lokaci ya tsaya ya na kallona ya rasa abunda zai ce min.
Sai kuma chan ya nisa kafin yace"Jiya da Daddare muka dawo garin Hasiya. Kuma yanzu ma wata tafiyar ta kama mu yanzu."
Kai tsaye na kallesa kafin nace"Yau? To zuwa ina?
Sai da ya ja Numfaashi kafin yace"Zuwa Gusai."
Mirmishi na yi kad'an kafin tace"Allah ya kiyaye hanya."
Kudi ya fiddo cikin Aljihunsa ba zato kawai naji ya riko hannuna ta cikin Hijabin ya jawo shi waje karo na Biyu da Fatayen Hannayenmu suka kara had'uwa waje d'aya.
Dukkanmu sai da muka ji wani yam! Dumin Hannuna ya gauraye da Sanyin hannunsa.
Duk da yaji yanayin ammh bai maida kai ba sai ya sakamin kudin da ke hannunsa a cikin hannuna ya matse Lokaci d'aya ya na fadin"Ki kuka da kanki kin ji ko?.
Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ammh na kasa mgana.
Hannunsa guda d'aya ya saka ya Dago habata lokaci daya ya na kallon kwayan idanuwana.
Cikin wani yanayi yace"Akwai kayan abinci ba su kare ba ko?
Kai na kara gyad'a masa ina so ya sakeni saboda ji na yi idanuwana sun ciko da kwallah suna shirin zubowa.
Ba shawara da ni kawai naji hawayen sun fara gangarowa saman kumatuna.
Wad'anda na rasa ko hawayen kewarsa ne ko na tafiyar da yace zasu kara yi ne?
Shi kuma hawayena su suka kara sakashi ya shiga wani yanayi har ga zuciyarsa da niyar ya lallasheni ya jawoni jikinsa ya Rungumeni, lokaci d'aya ya na shafa kaina zuwa bayana da Sigar lallashi.
Kansa ya kwantar saman kaina ya na fad'in"Sorry. Am sorry SIYA..!"
Ya ke fad'a cikin wani irin Taushin murya da sigan kuma lallashi.
Chapter 31 · 0% Book details