Sashe 29
Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tunda Tahir ya dawo bai kara barin Gefen Sadiq ba ballatana ya samu ya je gidan Hasiya.
Wajen aiki ne kawai kowa ya ke zuwa inda ya cancancesa.
In kuma suka tashi kafin ya samu ya biya gidan Hasiya sai Tahir ya kirasa a waya yace ya dawo gida ya na jiransa ba Halin kuma ya yi masa wata karyar balle ya samu yaje ya Dubata.
Sai dai kullum da Safe in yaje wajen aiki ya na kiranta sau d'aya a rana Domin yaji Lafiyanta.
Duk da ta tabbatar masa ta na lafiya ammh a kasan ransa sai yake jin wani iri da zama da Tahir sai yake jin kamar yafi samun annushuwa in ya na zaune da Hasiya.
Har maganar Laptop dinsa ta yi masa yace mata in ya dawo zai zo ya Dauka.
Bai samu kuma yaje ba sai da aka Rufe sati sannan ya samu ranar da Sassafe kafin ya wuce wajen aiki ya biya ya dauko saboda Tahir sai masa mgana ya ke yi ganin bai saba barin komai nasa a wajen aiki ba.
Bayan laptop bai dauko komai ba, ammh kuma ko bayan ganin Na'uran Tahir bai daina bincikarsa ba kamar yana zarginsa da zama a wajen Hasiya.
Bayan takalma ya lura ba wasu kayan Sadiq har da wata jallabiyansa.
Kai Tsaye ranar da Safe suna shirin Fita wajen aiki Tahir yace"Wai ni ko ina jallabiyar nan taka na daina ganinta ne kwata kwata.?
Sadiq na duke ya na Daure igiyan takalminsa na masu hidimar kasa da gwamamati ke ba su, yau laraba suna da CDS, Hatta Tahir shima shigar kayan su na Bautar kasa ya yi.
Cikin Halin ko in kula Sadiq yace"Wata jallabiya kenan?
Tahir yace"Wacce kace ka siyo ta a Saudiya sanda ku ka je tare da Innani."
Sai a lokacin ya tuna da ita ta na cikin kayan da ya baro gidan Hasiya.
Kasa mgana ya yi shi kuma Tahir bai damu ba sanin Halinsa daman kana mgana yaji kuma ya yi kamar bai ji ba.
Sai kawai yaji yace"Ta bace."
Cikin mamaki ya juyo daga saka rigar jikinsa ya na kallon Sadiq yace"Ta bace? A ina.?
Ba zato kawai Sadiq yaji bakinsa na fad'in"Wajen wanki mana."
Tahir cikin tantama yace"Wajen wanki kuma? Yaushe ka fara kai wanki kai da kace baza ka kara ba shi wanki ba.?
Sadiq ya runtse ido na wani Lokaci bayason ya na karyan nan ba Halinsa ba ne ammh kuma ya zama Dole.
Mikewa ya yi ya na fadin"Eh na ji na gaji ne sanda baka nan shiyasa na ba shi."
Tahir ya gyada kai kafin yace"To ka yi masa mgana?
Sadiq da sauri yace"Sharesa kawai ko an yi mgana ai ba ganinta zan yi ba kasan Halinsa zai ce zai duba ammh kuma shuru zaka jisa."
Tahir yace"A'a da dai ka yi masa mgana yasan abunda ake ciki ko?
Sadiq yace"Tahir ka bar mganar nan kawai kaji."
Tahir kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya jinjina kai kafin yace"Shikenan tunda kace haka."
Sai kuma bayan sun gama karyawa zasu tafi Tahir ya duba ma'ajiyar takalmansu yaga har alokacin ba wasu cikinsu cikin Maganarsa yace"Wai baka karb'o sauran takalman ka wajen mai Foolish din ba ne?
Sadiq yaji kamar ya kurma Ihu ya na rataya jakarsa ta baya yace"Naje an ce ya tafi garinsu.".
Tahir ya mike ya na fad'in"What!?
Sadiq ya fice daga dakin batare da ya kara ma Tahir mgana ba.
Shi ko Tahir mamakin Sadiq ne ya kamashi duk da yasan Halinsa na rashin ba ma wasu abubuwan Muhimmanci.
Ko a hanya ma Tahir korafi ya rika yi ma Sadiq na ya rika kula da kayanshi ko don yaga ya na da su da yawa shiyasa baya maida kansa?
Sadiq ya kallesa kafin yace"To Tahir."
So ya ke daganan mganar ta tsaya shiyasa yau yace su hau mashi.
Kowa kuma sai ya nufi inda za shi.
Ya na Office din su na yan Castelia Hasiya ta kirashi har gabansa ya fad'i ya zata ko wani abu ne.
Sai da yaji tace Yaron Adda Fati ne ba lafiya ta na so taje ta gaisheshi in ya bata izini.
Cikin muryansa ta sanyi da natsuwa yace mata duk inda ta ke son zuwa kada ta damu da sai ta tambayesa ya riga ya yi mata izini.
Da tl ya tambayeta ko ta na da kudi? Sai tace akwai wanda ya ke bata bata komai da shi sai ta yi amfani da shi na abun hawa
Da haka suka rabu da juna bayan sun yi sallama.
Sadiq ya yini Tunanin rayuwar da ya saka kansa aciki wato wata rayuwa ya ke yi, wacce kowa yasan ba itace ainihin Rayuwarsa ba.
Har ga Allah Saboda ya taimaki Hasiya ya aureta sannan saboda tsaida kuka da damuwa daga Idanuwan Uwa irin Amma.
Har kuma a zuciyarsa kuma ya na da Niyar sakinta in zai koma gida Saboda rayuwarsa ta zariya dabam ta ke da Rayuwarsa ta gusai.
Sai dai kuma da abun ya matso sai yake jin kamar in ya saki Hasiya bai yi mata adalci ba tunda tun farko bai kafa musu wannan sharadin ba.
Sai yake jin girman abunda ya ke so ya aikata zai iya shafe Ladan Taimakon da ya ke tunanin ya yi mata.
Duk sai ya kasa samun Mafita ya na cikin Tsaka mai wuya gaba kura baya Damisa duk iya hangensa da Tunaninsa ya kasa gano wata mafitan da zata bulle da shi bayan ya saki Hasiya ta kama gabanta shima ya koma in da Rayuwarsa ta dace.
Gashi Sauransu bai fi wata uku ba suna zuwa hutu gida suka dawo sai na tafiya gabadaya.
Ya kamata duk wani taimako da zai yi ma Hasiya ya gaggauta taimakonta cikin wannan wattanin kafin Lokaci yazo ya kure masa.
Suku suku ya yini kamar mara lafiya duk wanda ya yi masa mgana sai yace kansa ke ciwo har gida akace ya koma ammh sai yace a'a saboda yasan ko ya koma banda Tunanin da zai addabesa ba abunda kuma zai iya tsinana ma kansa.
Da ace Hasiya na nan ne sai yaje wajenta ya kwanta ya Huta ammh yasan tunda ta masa waya ya na da Tabbacin ta tafi in da tace zata je d'in.