← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 75

Sashe 30

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kamar ya sani muna gama waya da shi cikin murna da Farinciki na shirya na tafi saboda zumud'in da na ke ciki na fara fitata a karo na farko.
Gidan ba dadi Ummi na makaranta sai dai kuma akwai yan jere za'a kawo amarya a dakin da ke kusa da na Ummi zamu karu mu zama mu uku kenan.
Ban kira Add Fati nace mata zan zo wajenta ba, Amma kawai na fad'amawa da muka yi waya da Safe.
Itace ta tambayeni ko na nemi izinin mijina? Sai na ce mata baya gari.
Ita ta matsamin sai da na kirasa a waya na tambayesa cikin ikon Allah kuma ya bani izinin zuwa duk inda ya kamata.
Dubu biyu na dauka acikin kudin da ke hannuna Dubu shidda ne daman a hanya na tsaya na siyama yaran Biskit sannan na karisa koda naje ma Adda Fatin bata nan taje kai Hanif asibitin madarkaci ta yara Habibun ne kad'ai a gida sai da na zauna na jirata sannan.
Sai dai ta dawo ta ganni kamar Daga sama ko da bata fad'a ba sannan taji Dadin ganina.
Hankalina kwance sannan har kiba nayi, Hanif yaji sauki zazzabi ne da Mura na ba su Tsaraban su shi da Hanifa sai bayan azahar Habiba ta Dawo daga makaranta ta na ganina ta Hau ihu ta zo da gudu muka Rumgume juna.
Adda Fati na gefe ta na mana mirmishi.
Ranar ni na yi mana girkin rana har miyan tuwon dare ni na Daura mata, Sai kallona Adda ta ke yi ta na mirmishi ganina cikin natsuwa da walwala kuma hakan ya na nuna ina cikin kwanciyar Hankali a gidan aurena.
Mun sha hira duk da rabin Hiran na Amma ce ina ta ma Adda Shagwaban ya kamata mu shirya muje mu Duba Amma, Adda Fati tace Amma tace kowaccen mu ta zauna gidan mijinta ta yi biyayyan Aure ita lafiyanta kalau.
Ba ni da tacewa tunda nima haka Amma ta fad'amin ammh mganar gaskiya ina kewarta sosai ina kewar cinyarta in da na ke kwanciya naci kuka na har sai na koshi.
Sai da biyar ta gota ne Adda Fati ta fara min mganar na zo na shirya na tafi gida.
Ina Tura baki nace"Kai Adda kamar ki na kora na? Duba fa agogo shidda ma ba ta yi ba"
Adda Fati tace"To kafin ki shirya ki fita ai shiddan ta yi kuma kinga in yamma ta yi wahalan abun hawa."
Jin haka yasa Sai ban yi gaddama ba naje na shirya na fito ina ce mata zan tafi sai taje na jira Habiba ta Dawo taje siyomin kayan miya ne da zan tafi da shi.
Sai na zauna saman Hannun kujera ina Fadin"Ina so naje gidan Adda Rukayya ina tsoro."
Na fad'a cikin wani yanayi Adda Fati ta kalleni kafin tace"Kada ki je yanzu ki bari sai nan gaba."
Kai na jinjina mata kafin nace"Shikenan gobe sai naje gidan Ramatu na yi mata yini."
Adda Fati ta kalleni cikin mamaki kafin tace"Gobe kuma?
Na gyada mata kai ina yar dariya cikin Harara tace"Baki da Hankali ne? Ai sai ki bari a kwana biyu ko Hasiya?
Kai tsaye na fara bata labarin yadda muka yi da shi a waya yau da Safe.
Sai ta jinjina kai kafin tace"Baya gari kenan?
Da kai na amsa mata alamun Eh kai Tsaye ita kuma tace"To wani gari suke zuwa shida megidan nasa?
Na yi shuru kafin nace"Wlh bansani ba Adda."
Adda Fati itama sai ta yi shuru sai a lokacin ta fara wani tunani anya ba su yi kuskure ba? Ba su san komai fa da ya Danganci Abubakar ba kuma ba'a aure cikin Duhu.
Ni kuma iya gaskiya ta na fad'a mata tunda bai taba fadamin ga inda suke zuwa ba, muna cikin hakane sai ga Habiba ta kawo min kayan miyan sai na mike ina ma Adda Fati sallama.
Har kofar gida ta rakani har na fita sai ta saka baki ta kirani na juyo na dawo kai tsaye tace"Kun yi mgana da shi akan ya kai ki chan garin na su ki ga yan'uwansa?
Shuru na yi kafin nace"Eh yace zamu je ammh ba yanzu ba."
Adda Fati tace"Ba yanzu ba sai yaushe?
Kai tsaye na kalleta kafin nace"Bansani ba Adda."

Sai kawai ta girgiza kai kafin tace"jeki Allah ya tsare sai mun yi mgana."
Da haka na wuce Habiba ta rakani na samu mashin tunda yafi sauki muka rabu ina ce mata ina jiranta wannan Satin ranar da ba makaranta.
Maganar da Adda Fati tamin ya tsayamin arai nima kuma sai naga ya kamata zuwa yanzu nasan waye na ke Aure.
Duk da auran namu bai gama cika matakin kowani aure ba, ammh dai akallah tunda an kwarari wattani ya dace ace yan'uwansa da suka Rage masa su san da ni.
Irin yadda ta min mganar haka ma Ramatu ta min washegari da na je mata yini.
Duk da ban fito na bayyana mata baya kwana a gida ba na, in kuna ya kwana to muna mabambamtan muhalli.
Ammh itama ta nuna min zuwa yanzu ya kamata na san wanda na ke aure sannan kuma yan'uwansa suma susan dani.
Da farko bana wannan Tunanin ammh sai da Adda Fati da Ramatu suka ankarar da ni sannan na ga cancantar haka.
Na kuma kuduri niyar zan masa mgana ya kai ni garinsu naga Danginsa.
Abun sai kuma ya fara Damuna acikin raina haka ma Adda Fati ita Damuwar nata ma guda biyu ne, na rashin sanin takammman Sana'an da Abubakar ya ke yi.
Damuwar ta bayyanan mata har a saman Fuskarta har sai da Baban su Hanifa ya fahimci ta na da Damuwa sai ya tambayeta.
Cikin damuwa tace"Baban hanifa Sai yanzu na fara tunanin anya bamu yi kuskusren biye ma Amma ba?
Kai tsaye yace"Kuskuren mene?
Cikin Alhini tace"kan mganar auran Hasiya da Abubakar. Ka duba ka gani bamu san komai a kanshi ba babban abun tunanin ma bamu san sana'arsa ba ya dai ce shi mutumin Shinkafi ne sannan karatu ya kawosa nan da kuma Buga bugar sana'a."
Habibu ya yi shuru bai ce komai ba, ya na nazari kafin ya nisa yace" Yanzu me ne mafita?
Adda Fati tace" Na rasa mafita kaina duk ya kulle mun yi mgana da Hasiya ta ce itama batassn ina ya ke zuwa sana'ar tasa ba, kuma maganar ya kaita taga danginsa yace ba yanzu ba to sai yaushe? Tunda an riga an zama Daya, ai yakamata ya kaita ta ga Ahalinsa tasan wanda ta ke aure."
Habibu ya jim kafin yace" Nima da farko da naji mganar auran Hasiya sai da wannan tunanin ya fad'omin sai dai jin abun daga Amma ne yasa ban ce komai ba ammh mafi a'ala acikin aure mu bi dokikin da Annabi muhammadu salallahu alaihi wasallam ya sanar damu ya yin bada auran ya'yanmu sana'a da sanin mu'amala tare da sanin Ahali shine ginshikin aure."
Adda Fati sai ta zabga Tagumi ta kasa mgana sai a yanzu ta tabbatar ma kanta sun yi kuskure Halin da Amma ta ke ciki na Tsaka mai wuya shi ya kaita ga yanke wannan Hukuncin da zai shafi rayuawar Hasiya gabadaya.
Chapter 30 · 0% Book details