← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 75

Sashe 18

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

INNANI da ita ta kasance mahaifiyace ga Alhaji Sulaiman, Sun jima tare ya na jin sunan magajin gida bai taba kawo ransa wannan magajin gidan D'a ne ga Alhaji Sulaiman ba sai a shekaran da ta gabata yasan ashe d'ansa ne sannan shine kwara d'aya tal d'a Namiji da ya Haifa sannan gatan Duniya yaron nan ya na da shi.
Komai fa in za su yi sai yaji sunan Magajin gida kamar ma Alhaji Sulaiman ba ya iya yanke wani abu kan Dukiyarsa ko kasuwancinsa sai da Izinin Magaji gida.
Bai taba ganin yaron ba ammh yasan matsayinsa ya wuce ya zauna ya na faman wani lissafi.
Innani kuma ya fahimci Umarninta ne Umarnin Alhaji Sulaiman ya na sonta kuma duk abunda tace ta na so shi ya ke so.
Alhaji Jibiril ya gyara zamansa sannan ya dauki ruwan zafin da aka kawosa ya kurb'a sau biyu kafin ya ijiye.
Shuru ya yi kafin kuma Lokaci d'aya ya saki dariya mai kayatarwa shi kad'ai..
Lokaci ya yi da zai kara bunkasa kasuwancina.
Lokaci ya yi da zai kara kusancin da Alhaji Sulaimam.
So ya ke ya fisa ido a kan wannan harkan kasuwanci so ya ke nan gaba kad'an ya shahara da kudi fiye da Alhaji Sulaiman.
Alhaji Jibiri mutum ne mai son kudi fiye da komai a duniya sha zumamu me baya rabar ka sai ya tabbatar da in zai karu dakai in yasan bazai karu dakai ba  to bazai yarda ya had'a inuwa da kai ba ko yan'uwan shi ne in yaga bazai karu da kai ba baya doguwar huld'a da mutum.
Ko da wanda suka fito ciki d'aya ne kuwa in yasan sai dai ka karu da shi to mu'amula ta zumunci sai in dai kai ne ka rike zumumcin ammh shi bazai damu da shi ba.
Mutum ne mai son abun duniya da ya gwammace son kudi fiye da komai.
Alhaji Jibirl ne mai Daraja kudi fiye da komai a Rayuwarsa.
Kud'i ne mutumcinsa su ne kimarsa in baka da kudi baka da wani kima ko Daraja a idanuwansa.
Saboda kudi kuwa zai iya aikata komai a rayuwarsa.
Alhaji Jibirl baya son asaran kudi ko ta na naira biyar ce in kuma asaran ta fara ji ya ke yi kamar ya Mutu saboda hakan.
Acikin gidansa macen aure d'ayace Hajiya Murjanatu da ya'yansa guda Biyar mata uku namji biyu.
Mubarak ne Babba sai Fathiha sai Zahra'u sai Kamal sai karamar su Fatima suna kiranta Bintu.
Mubarak ya gama karatunsa ya na aiki ne da Kamfanin Dangote da ke kaduna sai Fathiha ta yi aure a garin kano sai zahra'u da ke shekara ta biyu  a kaduna State university sai kamal da ke karatu a Buk kano ya na zaune gidan yar'uwansa Fathiha.
Autansu kuma Bintu ta na SS1 ne yanzu saboda tsakaninsu da Kamal akwai tazara mai yawa.
Ko acikin gidansa daga matarsa har ya'yansa susan babansu na Daraja kudi shiyasa suma suke tayashi Daraja shi komai na gidan nan ya na kan tsari ne komai na abun bukata a Farkon wata zai siya in kuma wani abu ya kare ba'a isa ya fito da wani kud'i ba sai wani sabon watan saboda ya riga ya gama Budget din wannan watan ko rashin lafiya ne kuwa sai dai yace Hajiya Murjanatu ta ranta masa in sabon wata ta shiga zai biyata.
Shi komai na shi akan Tsari ne in kuma ya kuskure ma tsarinsa sai dai a nemi wata mafitar.
Bazazzagi ne gaba da bayansa uwa da Uba aiki ne da Sauyin Rayuwa ya maida shi Dan kaduna.
Saboda makonsa yasa matarsa Hajiya Murjanatu kama sana'an saida kayan yara kuma Alhamdulillah ta na samu domin da shi ta ke Rufamana kanta asiri da ya'yanta.
Tunda ko sha'anin yan'uwanta in bata neman na kanta sai taji kunya shi kanshi Alhaji jibirl din bai yi ma na shi ba ballatana na ta.
Ita yar anguwan kabala ce nan aka haifeta kuma anan ta girma auran Saurayi da Budurwa suka yi tsakaninta da Alhaji Jibril.
Saboda son kud'insa yasa bazai iya zama da mace sama da d'aya ba
baya son kashe kudi ba gaira ba Dalili shi kan shi Dalilin nasa mai karfi ne shima in ya fita cikin Budget sai da ya jira sabuwar wata ta shiga.

Ya na kurban Ruwan zafi ya na mirmishi Saboda ya hango cigaba sasai a hasashensa.
Wayarsa ya Dauka bayan ya sauke kofin hannunsa saman teburin gabansa.
Kiran ya yi sannan ya saka a kunne bayan an dauka suka gaisa kamar ba a yanzu suka gama waya ba.
Cikin sauke Murya yace"Alhaji yanzu na yi wani tunani. Me zai hana mu kara fad'ada Zumumcim mu ta hanyar sanin iyalan juna?
Mgana ake masa ta d'ayan bangaran ya na ta mirmishi da annushuwa.
Daidai Lokacin da wani matashi ya yi sallama ya shigo falon.
Hannu ya daga masa alamun ya na waya a yadda Mubarak ya ga Baba na mgana cikin Dariya da Farinciki yasan cewa wata harkace ta karuwa in ba haka ba haka Kurum bazaka gansa ya na Farinciki da Dariya haka ba.

******

In yace Hasiya bata ransa ya yi karya, sai dai ya na boye tunanin hakane Saboda Tahir.
Tunda ya siya mata waya ba shi da ikon zuwa ya ganta sai Tahir yace ba ga waya ba in da matsala zata kirasa.
In ya dawo daga wajen aiki haka zai kwanta ya na ta Tunane tunane hakikanin gaskiya har rama sai da ya yi saboda zullumi
Gida ya ke so yaje ammh kuma kunya baza su iya barinsa yaje a wannan Lokacin ba.
In ya gan su zai kara shiga damuwa cin amanan da ya yi musu.
Sun kusa gama Bautar kasar su ba za su wuce wattani uku nan gaba ba. akwai bukatar kowa ya yi ma kansa tsarin da zai taimakesa anan gaba.
Yana da Burin ya koma gida in ma karatun zai cigaba da yi bazai kara yi a Zariya ba sai dai ya sauya muhalli kuma nan gaba.
Sun taba mgana da Tahir akan me zai fara yi bayan sun gama Hidimar kasar  su?
Kai tsaye Tahir yace masa gida zai koma ko saboda Hajja sannan yan'uwansa daman sun matsu ya dawo gida, zai koma yaga abunda zai fara sannan kuma Zai taba siyasar yankinsu.
Ba haka kurum Tahir ya ke karantar Siyasa ba, yana son siyasa shiyasa kaf Shafukansa na sada zumumta shi ne bin yan siyasa ya na musu comment da like karatu ya Dauke masa Hnkali daga Fad'awa siyarsa.
Kuma ya na da tabbacin in Tahir ya samu dama zai shiga siyasa tunda ya na da Ra'ayi.
Da ya tambayeshi mganar cigaba da karatu fa? Sai Tahir yace ko zai cigaba sai ya kama wani abun a hannunsa sannan.
Shi ko ya na da Burin cigaba da karatu in sha Allahu kuma ya na da Burin ya samu aikin da zai Dogara da kansa baya so ya zauna saboda mahaifinsa na da kudi.
Shiyasa duk inda aiki na ma su  irin karatunsa suke ya kan duba wajen sosai kamfanin da yake bautar kasa ma sun ce zasu daukesa aiki ammh bai amsa su ba saboda ba shi da Burin kara zaman zariya.
Ya na Tunanin in ma Mastars dinsa zai yi sai dai ya je BUK kano ya yi chan bazai kara zaman zariya ba.
Kuma Bazai ji dad'in zama ba Tahir ba.
Wata zuciyar tace ga Hasiya?
Sai ya ba kanshi amsa da cewa Hasiya sakinta zai yi ta koma wajen mahaifiyarta shima ya tattara ina shi ina shi ya koma Gusai gaban iyayensa Sultana na chan na jiransa.

Ko a waya da ya kira Hasiya Sau d'aya da bai kara kiranta ba ya na da Dalili baya so ya cigaba da kiranta har ta Fahimci ya yi mata karya gwara su tsaya nesa nesa da juna kamar yadda Tahir din yace.
Kuma sannan kunya yake ji in ya ganta ga Tausayinta sannan da kuma jin nauyin kansa da ya zama makaryacin karfi da yaji gabadaya wata Rayuwa ya ke yi ba rayuwa irin ta Abubukar Sulaiman Shinkafi ba.
Yanzu Rayuwa ya ke yi a matsayin Assadiq maraya wanda ba shi da komai kuma wanda yaci Amanar iyayensa da karya sannan wanda ya kasa kula da Hakkin matar da ke kansa.
Cikin wannan satin Tahir ya tafi Daura an kirasa Hajja ba lafiya har ta kai ga asibiti ya so ya bisa su tafi tare sai daga wajen da ya ke bautar kasa suna da wani aiki yasa ya barsa ya tafi shi kadai akan in ya samu Sarari zai biyosa sai su dawo tare.
Duk sai kadaici ya kamashi ya saba komai tare suke da Tahir.
Shekarun nan kusan tare suke sai ko in ya koma gida Hutu.
Kwanan Tahir d'aya da Tafiya ranar dakyar ya yi barci ya na ta faman juye juye.
Sai yaji Tausayin Hasiya ashe haka ta ke fama da kadaici bai sani ba?
Batare da Tunanin komai ba ranar ta biyu daga wajen aiki Gidan Hasiya ya wuce Direct da Niyar zuwa ya Duba lafiyarta har acikin zuciyarsa.
Baisan Allah da na shi nufin ya ke sarrafa namu zuciyoyin ba.
Sannan abunda ke rubuce a zanen kaddaranmu bamu isa mu kauce masa ba.
Chapter 18 · 0% Book details