← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 75

Sashe 68

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammh fuskata cike da karin mamaki ni ba na kayan da ke jikina naga wasu yara Biyu mata sun fito daga Bedroom din Amarya da irin material din da na saka Jiya sakin baki kawai na yi ina kallonsu, sai ace wannan shima kawai had'uwa ce? Irin Atamfar d'aya fa harda Material din ba bu wani bambamci.
Sai wata zuciyar tace Hasiya Abun nasara ai ya na da iri da yawa da wannan Tunanin na shiga dakin da su Adda Fati ke ta salla su da sauran mutanen da suka zo daga gidan Baba Jibril.
Ina shiga Adda Fati ta fara tareni Adda Rukayya na sallah, Cikin mamakin ganina tace"ke da wa ki ka zo?
Cikin basarwa nace"Ni da Fatihatu ta matsamin sai da na Biyota."
Adda Fati tace"Ta kyauta damn yanzu nake tunanin mu koma gida, jakarki na Hannuna ana ta kiran wayarki ina Tunanin mijin ki ne."
Ta fad'a ta na mikamin Jakar na amsa ina kokarin Bude Jakar naji Diyar Goggo Kona ta na kallona tace"Hasiya Atamfarki iri d'aya da ta dangin Amarya da suka yi anko."
Sai na kalleta batare da na yi mgana ba, Adda Fati ce ta kara kallon kayan jikina kafin tace"Eh mun gani sai da Adda Rukayya ta yi mgana tace iri d'aya da na Hasiya."
Ni dai ban Tsaya sauraransu ba na cire wayata acikin jakata na sake mikama Adda Fati jakar na fice daga dakin daidai Lokacin da na ke duba Calls din wajen 20missed call kuma duka Daga Assadiq.
Ba a falon na tsaya ba saboda Hayaniya sai na fita zuwa Haraban gidan na samu chan gefen wajen tankin ruwa sannan na kira Assadiq sai naji line Busy da alamu ya na nema ne sai na d'an dakata.
Sai ko ga kiran shi ya sake shigowa da Sauri na d'aga kiran rabon mu da waya Tun jiya da yammah da muka iso kaduna.
Ina Dagawa yaji muryanta sai ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Siya ina ki ka shige ne? Kinsan kira nawa na yi miki baki daga ba?
Zan kira Adda Fati na nemi lambarta a wayana sai kuma na rasata."
Ajiyar zuciya na sauke kafin nace"Wayar na cikin jakata karama, kuma bata wajena ta na wajen Adda Fati, ita na ba ma ajiyar jakar tun safe."
Shima ajiyar rai ya sauke kafin yace"Hankalina ya tashi Sosai dazu na samu salama Tunda kina lafiya."
Daganan sai ya cigaba da fad'amin yadda ya yi kewata na yinin ranar gabadaya ni kuma kamar an yi min wani abu na kasa yi masa Fara'a haka Kurum na ke jin raina ba Dadi.

Muna cikin wayar ne wata mata tazo gefena itama da irin Atamfar jikina ta na mgana a waya itama.
Sai dai ni na rigata gama Wayar Tunda dagachan bangaran Assadiq na ji kamar ana mgana sai ya yi saurin ce min zai kara kirana ya kashe.
Dagowa na yi ina kallonta bata da wani Tsawo fara ce ammh ba Sosai ba ta na kuma d'an jiki kad'an na Hutu da jin Dadi.
In zama girmeni da kad'an ne ko kuma mu zo Tsaran juna ni da ita.
Ashe ta gama wayar itama sai taga ina kallonta sai ta yi min mirmishi nima sai naji kunya na maida mata martanin mirmishi.
Ni sai nake ganin su, da wad'anda na gani a falon nan da ita din suna kama da wani Fuska da na sani har matar nan da Tsohuwar nan a raina ina jin kamar ni dai yanayin fuskarsu kamar nasan wani ko wata da yanayi mai kama da na su.
Har ta wuce sai ta kara dawowa ta na kallona kafin tace"Allah sarki ga irin ankon mu."
Nima sai na yi mirmishi kafin nace"Eh nima ina gani nace komai iri d'aya."
Dariya ta yi kafin tace"To ai kamfani bamu kad'ai ya bugamawa ba. Sunana Saliha ke fa?
Ta fad'a ta na bani hannu alamun mu gaisa nima sai na mikamata nawa hannun muka sarke.
Cikin maida mata martanin mirmishinta nace"Ni kuma Hasiya."
Sai ta Bude baki kafin tace"Hasiya? Ko dai Asiya?
Cikin yar dariya nace"Hasiya dai domin shine sunan yanka na."
Sai ta Rausayar da kanta kafin tace"ko? Abunda yasa kika ji nace haka nasan sunan Hasiya ai Asiya ne"

Mirmishi na yi mata ban ce komai ba ita kuma sai ta kara kallona kafin tace"Ni yayar Salima ce Amaryan da muka kawo, Ina aure a Ibadan ya'yana biyu, Sha'anin nan ne ya kawoni da zarar an gama zan koma Ibadan."
Nima sai na samu kaina da fad'in"Ni ma ina da aure ammh ban haihu ba, kuma ni a matsayin diyar yayan mahaifin Ango ne daga Zariya muka zo."
Cikin Fara'a Saliha tace"Ma sha Allah naji dadin had'uwa da ke Hasiya kina da Fara'a"
Nima cikin dariya nace"Kema haka sannan ban kai ki fara'a ba."
Gaskiya na fad'a ta na da Fara'a ni kuma haka Kurum taji ta Burgeni.
Sai ga shi mun samu wani Dutse da ke wajen mun zauna muna ta Hira ni da ita.
Har ta na fad'amin ta gama Degree dinta ammh  bata aiki sai dai kasuwanci ta ke yi, nima na sanar da ina yanzu na fara karatun nawa ina shekarar ta Biyu ne in muka koma Hutun karshen Shekara.
Ban tambayeta ba da kanta ta fad'amin akwai nisa Daga Ibadan zuwa Gusai in dai ba Jirgi ta Biyo ba sai ta kwana a hanya.
Ni kuma sai nace mata ai yanzu in ta tafi sai ta jima bata zo ba ko?
Cikin yar dariya tace"Wane ni? Ai zuwa ya kamani in dai da rai da lafiya nan da wattani uku akwai Bikin kanin mu Sadiq, da kanwarmu Sultana da ya ke diyar kanwar Abba ne kuma nan ta girma cikin gidan mu."
Sai na jinjina kai kafin nace Allah ya  Sanya alheri.
Ina so ta na tambayeta Tsohuwar nan da Matar da na gani yan'uwan su ne?ammh sai na kasa yi mata mgana.
Sai dai a raina na yi Tunanin Tabbas tare su ke yan'uwan Amarya ne.
Mun jima muna ta Hira har aka kira Isha'i sai tace ko zan yi sallah ne?
Kai Tsaye nace mata ba na sallah itama ta na Dariya tace mun yi anko.
Sai kawai mu ka cigaba da Hiran mu, sai aka kira wayarta ta dauka ta na magana naji dai ta na ambaton sunan Mama, da Umma sai kuma naji sunan Innani a bakinta.
Sai da ta gama wayar sannan ta kalleni ta na fad'in"Mamanmu ce, ta na tambayata ya innani, kakarmu ce fa irin rigimamman tsoffin nan ne wai sai ta zo Abba ya yi ya yi da ita tace sai ta zo."
Sai na yi mirmishi nace"Na ganta ba wata tsohuwa mai gilashi ba sannan itama da irin Atamfar jikin mu ko?
Saliha tace"Itace a ina ki ka ganta?
Sai kawai na yi dariya na fara bata Labarin had'uwar mu, sai da ta yi Dariya kafin tace"Umma ce ta zo ta Dauketa domin tunda muka zo muka bar mata wahala da ita, Sadiq da shi kada'i ne ya isa ya hanata zuwa wannan karon da kansa ya sakata a mota, to waye zai dauki Innani daga karshe ta rika tsine masa kwata kwata bata san abun arziki ba."
In ta ambaci sunan Sadiq sai naji gabana ya fad'i ko don sunan Mijina ne oho?
Saliha sai bani Labarin Kakarsu Innani ta ke yi, ni kuma ina ta shan Dariya sai naji ina sha'awar zama da ita, saboda ni bansan dad'in duka zama da kakkani ba.
Ta na cikin bani Labarin ne wasu yanmata Biyu suka fito suma Haraban gidan.

Ina ji Saliha ta kira sunaayensu Siyama da Sultana ta kira su da Hannunta.
Sai ga shi sun kariso gabanmu ganina da Saliha kila shi yasa suka gaishemu dayar wacce bata da Tsawon ta fi Fara'a Doguwar kuma sam ba ta yi min Fara'a ba.
Kai tsaye ta kallesu kafin tace"Sai ina?
Siyama tace"Shago zamu fita nema  Amarya ta aike mu mu siya mata Coke mai sanyi."
Saliha tace"Shine sai kun fita? Ta kira shi Mubarak din fa?
Siyama tace"Ta kira sa wayarsa baya shiga."
Saliha bata damu ba ta kalleni ta na fadin"Kinga kanwar tamu da zata auri kanin namu nan"
Ta fad'a ta na nuna mara Fara'an nan, Sai Siyama da tace kanwarta ne itace auta a gidan su.
Mirmishi na yi musu Siyama ta kara gaisheni wacce aka kira da Sultana ce kwata kwata naji bata kwantamin a rai ba kamar yadda itama gani Daya ta yi min taji ban burgeta ba saboda Farin fatata har shiga ido ya ke yi.
Sai ma ta kauda kai kawai ta na wasa da gefen mayafinta.

Ina jin Saliha na gaya musu ni kanwar Mubarak ce cousin muke, Siyama ce har suka bar wajen ta na Fara'a Sultana kuma ko kad'an banga Fara'a a Fuskarta ba.
ita kanta Salihar sai ta ce min haka take wani Lokacin ta yi ta kunci kamar an yi mata wani abu.
Sauro suka Damemu da ya sa muka tashi muka koma cikin gida.
Ammh kafin mu Rabu sai da muka karb'i lambar juna Tunda na gayamata ba anan zamu kwana ba. kuma gobe da Safe zamu koma zariya.
Dakin Amarya ta wuce ni kuma sai na wuce dakin da su Adda ke ciki na iske sun shirya ni suke jira.
Da ya ke ba nisa a kafa muka taka zuwa chan gidan, na gaji so kawai na ke na kwanta daman Dakin Zahra'u na ke kwana Gyara jikina kawai na yi na kwanta, su Adda Fati suna dakin da aka sauki sauran yan'uwansu na Zariya.
Na yi mamaki har gari ya waye ban kara ganin kiran Assadiq ni kuma ban kirasa ba, da Safen bamu koma gidan Amarya ba muka yi shirin tafiya Adda Fati na wani mganan mu jira a tafi gabadaya nace to ni dai zan yi gaba sai sun zo.
Chapter 68 · 0% Book details