← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 75

Sashe 3

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuwa Lokacin har Ramatu kuka ta ke yi Hamma Isuhu ne ya yi jarumtar rikeni  yana kiran sunana da karfi ammh ina kuka kawai na ke yi ina fad'in"Assadiq ya sakeni yanzu ba na bukatar auransa a kaina."
Amma ce tace Ramatu da Adda Fati su fitar da ni daga Dakin haka suka Rikeni ina kuka ina kururuwa suka fita dani daga Dakin daman matan gidanmu suna fara jin kuka suka yi Dafifi ana son jin gulma.
Suna ganin an fito da ni suka yayyame mu suna tambayan ba'asi ba wanda suka tanka suka shige da ni Dakin Maman Boy.
Ramatu rikeni ta ke yi ta na Fad'in"Hasiya don Allah ki yi shuru"
Na kasa domin komai da ya faru da ni tundaga farko ne ya ke dawowamin da kuncin acikin raina na kasa Sarrafa kaina.
Kawai sai na Rungume Ramatu ina Fadin"Ramatu kamar na mutu haka nake ji. Gwara mutuwata da wannan rayuwar"
Baki ta Rufemin ta na Fad'in"Kada ki yi sabo Hasiya ki bari don Allah kin ga jama'a hankulansu ya dawo kan ki."
A tsakar gida kuwa Adda Fati sai shan Tambayoyi ta ke yi har da masu cewa ko wani abu ne ya samu angon?
Ita dai ta ma kasa mgana ta sulalane ta koma Dakin Amma ta isketa ta na ta kuka Inna Talatu na faman lallashinta har Adda Rukayya ta kasa tsaida kukanta.
Adda Fati Sadiq ta kalla da kansa ke kasa kanzil bai ce ba Tahir ne ke kallonsa a ransa ya na Tunanin shi ko Sadiq ya na da zuciya a kirjinsa kuwa? Duk yaji irin wannan bakaken kaddarorin ammh bai iya furtama yarinyar nan saki Lokacin da ta bukata ba? Shifa ko alama bai Tausaya musu ba su san su na da matsala meyasa suke kokarin gayyato wani cikin rayuwarsu?
Wannan abunda suka aikata ba Adalci  acikinsa sam itama yarinyar ai tasan gaskiya abunda aka aikata akwai cutarwa acikinsa.
Hamma Isuhu ya ji hon din mai Mota yasa ya fita da sauri ganin haka yasa Adda Fati ta kalli Sadiq ta na fadin"Amma yau zata koma garinsu gabadaya. Mganar Hasiya kuma kayan Dakinta suna hannuna kana da inda za'ayi mata jere ne yanzu.?
Tahir ya kalleta kamar zai yi mgana sai ya fasa ya jira Sadiq da ya kawo kansa yasan mafitarsa.
Kai Tsaye cikin natsuwarsa yace"Yanzu kam babu ammh za'a samar in sha Allahu. "
Adda Fati tace"Shikenan daman in tambaya ya za'ayi ne zaka tafi da itan ne?
Tahir ya yi tsam yaji amsar Sadiq yaji bai ce komai ba, kawai sai shi ya kalli Adda Fati ya na fad'in"Mu tafi da ita mu ijiyeta a ina? Bamu da inda zamu sauketa dakin da mu ke ciki Falle d'aya ne da ni da shi muke kwana aciki."
Tahir ya fad'a cikin jin Haushi Sadiq yasan Halin Tahir aka cigaba da mgana sai kuma ya sauya zencen yasa da Sauri yace"Zata iya zama a wajen ki na wani lokaci kafin na sama mata muhallin da zata zauna?
Ya fad'a lokaci daya ya na kallon Adda Fati wacce ta kalli su Amma sai suka gyada mata da yasa ta jinjina kai kafin tace"Shikenan bakomai. ga lambata in ka samu wajen sai ka sanar da ni akan Lokaci."
Ba muau ya fiddo karamar wayarsa ya mika mata ta saka masa lambarta shi kuma ya kirata saboda ta ga Lambar sai ko ga kira ya shigo wayarta dake cikin jaka ta Dauko ta na Fadin"Bari na yi Saving din lambar."
Bai ce komai ba ta na cikin Adana lambar Isuhu ya leko ya na fadin"Amma ya kamata mu tafi yanzu Direban ya matsa dare ya ke gudu."
Jin haka yasa Amma tace"Hakane to bari na fito"
Jin haka yasa Sadiq ya mike shi da Tahir a sanyaye yace"Allah ya tsare hanya Amma."
Amma ta mike ta na gyara Daurin zaninta Lokaci daya ta na fadin"Ameen nagode sosai Allah ya jikan magabata. Allah ya yi muku albarka."
Tahir ta kallah taga sai wani cin mgani ya ke cikin dan mirmishi tace"Shi  wannan abokin naka baya mgana ne?
Sadiq ya kalli Tahir kafin yace"Ya na yi ammh ba sosai ba."
Amma bata damu ba ta jinjina kai ta na fadn"Allah ya taimake ku. Allah baku yarda zaku yi ya kuma rabaku da Sharrin duniya da Mutanen cikinta."
Sadiq ne kadai ya amsa da Ameen banda Tahir duk tare suka fito daga Dakin Amma na ta ce ma su Maman Boy tafiya ta tashi fa.
Sadiq da Tahir kofar gida suka tafi suka Tsaya Sadiq na son ganin Tafiyar Amma shi kuma Tahir tsoro ya ke ji kada ya tafi ya bar Sadiq shi kad'ai domin ya fara jin Tsoron mutanen nan shiyasa bai tafi ba ammh ba domin haka ba Tuni bai san inda dare ya yi mishi ba Allah dai ya isa ba kowa ya Cucesu ba sai Sadiq haka kurum yau ya hanasu su kwanta su huta ya kawosu inda kwata kwata ko a Tsari Rayuwarsu bata yi daidai ba.
Har Dakin Maman Boy Amma ta biyoni ta dafa kaina ta yi min addu'a daga karshe ta mike ta na fad'in"Allah yaga kyakyawan niyyata Hasiya. ina miki Fatan alheri da samun ingantattaciyar rayuwa a gidan auran ki in kin huce ki ka nemi sai na yi miki nasihan da uwa kan yi ma yarta a lokacin da zata je gidan mijinta."
Daga haka ta fice ina jin Ramatu ma ta fita tasan ko tace na tashi bazan tashi ba jin irin kukan da na ke yi.
Yan gidanmu da makota na kusa da na nesa duk sunzo sallama da Amma Allah Sarki Sabo suna ta kuka itama ta na kuka Adda Rukayya kuka Adda Fati ma haka, Habiba ko ta makale Amma ta na ta kuka Dakyar aka Rabasu sai cigiyata ake yi ana fad'in Ina Hasiya?
Maman Boye ke ta fad'in"Ta na chan ta nata kukan a daki ita kad'ai"
Maman Salihi ta karbe da fad'in"Abu biyu ne ya had'e mata ga Aure ga tafiyar Amma."
Su kadai dai suke kid'an su suna rawan su Adda na ta kuka ba su bi ta kansu ba.
Gaba Amma ta shiga ita da Hamma  jama'a na ta daga musu Hannu.
Motar na wucewa Tahir ya fizge Hannun Sadiq suka nufi hanyar dakin su Sadiq na binsa a baya ya na mirmishi ya ke fad'in"Sake ni ba guduwa zan yi ba Tahir Yusuf Daura."
Tahir yace"Tunda ka iya aure batare da sanin kowa ba to shima ka gudun abu ne mai sauki a wajen ka"
Sadiq sai da ya yi dariya har Fararan Hakoransa suka bayyana.
Cikin kwarin gwiwa yace"Ba inda zan gudu Tahir.
Tahir bai sake masa hannu ba sai da suka Danganta da Dakinsu ya saka hannu daya ya bude kwadon dakin ya tusa kansa da Sadiq ciki ya maida koda ya Rufe.
Ya cire riga da wando ya bar kanshi Dagashi sai gajeren wando.
Wayarsa ya Dauko ya na Fadin"Sadiq ko ka saki yarinyar nan yanzu ko Billahillazi na kira Umma na fad'a mata duk abunda ke faruwa."
Ya fad'a ya na kallon Sadiq ido cikin ido Tunda ya zare bakin gilashin da ya sanya.
Sadiq ya yi zuru ya na kallon Tahir yanzu in yace zai yi wata mgana Tahir ba burga ya ke yi ba, zai iya aikata abunda yace din.
Kuma hakan daidai ya ke da ruguza duka Tsarinsa lallaba Tahir yanzu shine a gabansa kafin yaji da Hasiya Daga baya.
Mikewa ya yi shima ya zare Rigan jikinsa daga shi sai Farar Vest.
Cikin kwantar da Murya yace"Tahir na fad'a maka taimakonta zan yi. Da zarar na inganta mata rayuwa Zan SAKETA da gaske."
Tahir ya kallesa cikin shakku kafin yace"Zaka saketa ka ce ko?
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Eh zan saketa Ammh ba yanzu ba?
Tahir ya katse shi da cewa"Har na tsawon wani Lokaci?
Sadiq ya yi shuru kafin ya sauke ajiyar rai ya na fad'in"Ban sani ba ammh dai nasan auranta ba kamar Sauran aure ba ne Tahir tabbas zan rabu da ita ko saboda Ahalina."
Tahir yace"Me yasa ba yanzu ba?
Sadiq yace"Haba baka ganin halin Tsaka mai wuyar da na shiga ne? So ka ke na saketa yanzu na karya zuciyar Uwa mahaifiya ka duba mana Tahir."
Tahir ya yi dariyan Takaici kafin yace"ka faranta ma uwar wata rai kai kuma ka bakanta ma taka uwar kenan?
Sadiq ya girgiza kai ya na Fadin"Tahir zauna mu yi mgana"
Tahir nace ka zauna don Allah."

*Janafty*
*17/01/2024*
*TMWB2K002*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
Chapter 3 · 0% Book details