← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 75

Sashe 52

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau ma bayan mun gama cin Tsiren da ya fita ya siyo mana da kayan Fruit muka zauna saman kujera muna kallo a karamar Computers dinsa.
Tun ba na Fahimtar fina finan har yanzu na Fara Fahimta nima.
Sanye ya ke da Riga da wando ammh wando 3quater rigar kuma mai gajerun Hannu.
Ni kuma na sanya wata Rigar barci na Doguwa mai kauri wanda Ramatu ne ta bani kyautar ta acikin kayan auranta Lokacin bikinta da ya ke a gida ban cika sakata ba, shiyasa bata ji wani jiki ba.
Ina zaune kusa da shi sai na yi matashi da kafad'arsa kamar yadda ya sabamin, bamu jima da gama jera kayansa acikin Wardrope dina ba da ya karbo daga wajen guga har da nawa, Da ba su da yawa sosai.
Na tuna muna cikin jeran kayan ya kalleni ya na fadin"Iya kayan sawan ki kenan ko kin bar wasu a gida?
Batare da Tunanin komai ba nace"Su kenan fa, don ma Adda Fati tamin Dinki Lokacin bikin mu."
Kai Tsaye ya kalleni ya na fadin"Daman an yi mana Biki ne?
Cikin ido ya kalleni nima ina kallonsa nace"Na manta Lokacin Tariyan mu zan ce."
Sai ya jinjina kai kafin yace"Kinga kuma nima akwai hakkin yi miki kaya a kaina fa."
Kai Tsaye nace"Ni na yafe maka Assadiq"
Da Sauri yace"Ni ban yafe ma kaina ba zan siya miki kaya masu yawa In sha Allahu."
A lokacin da zan kara mgana sai ya had'e rai yace baya son gaddama shiyasa na yi gum da bakina.
Ni yanzu bani da wata matsala sai wacce Ba'a rasa ba na yi kiba na kara Fari kamar bani bace wannan Hasiyar da ke Danwake a dogon gida da ke Samaru ba.
Ina yawan Tuna yan gidanmu in naga su Ummi na min wani abu sai na girgiza kai kawai, ni wani irin nau'in makirci da Ukuban gidan Haya ne ban sani ba ko nace ban gani ba ai sai dai na ba wasu Labari.
Sun gama yada min Habaici da karad'e anguwa da Sirrina shiyasa ba mai kulani ballatana ya shiga Sabgata.
Nima sai na kama kaina in ba Dalili mai karfi ba ko fitowa waje ba na yi.
Ni dai ina musu sallama da gaisuwa in muka had'u saboda Nasihan Assadiq da yace kada na Biye musu mu yi gaba da Juna mu sani Tunda Zama ya had'a mu waje daya ko da bazamu yi Huld'a da juna ba to ya zama Dole mu zama ma su yad'a sallama a tsakaninmu.
Shi ya kara nuna min cewa kada na Damu da mganar mutane a kaina abu daya zan yi yakini acikin raina shine Babu wani mai yi face Ubangijin sammai da kassai.
Zama da Assadiq na kara sani wasu abubuwan mutun ne mai Addini da Sanin ya kamata, ni kaina a gabansa gabadaya raina ilimi na ke yi, ya faramin karatun Qur'ani da asuba bayan ya dawo daga masallaci Domin ya Lura ina da Rauni ta bangaran sanin addinin ma gabadaya.
Sannan ya yi min fadan in na idar da sallah ba na tsayawa na yi azkar ballatana na yi addu'a ni kaina nasan gaakiya ya fad'a kwata kwata bani da Dakewa kan ibada da addu'a.
Ammh yanzu na fara Sauyawa ya sanar dani muhimmanci Addu'a da rike Allah Saboda duk bala'in da Mutum zai shiga in ka kad'aita Allah to shi zai sama ma mutum mafita.
K'aruwan da na samu sanadin zamana da Assadiq k'aruwa ce mai yawan da bazan iya kirga su duka ba.
Ni kaina nasan Assadiq ya shiga zuciyata da Duniyata gabadaya batare da na sani ba.
Idanuwana na wajen kallon ammh sam Hankalina ya tafi wani wajen sai da naji wayarsa na Vibration Gir! Gir alamun ana kiransa kenan, na yi mamakin ganin ana kira wayarsa sanin da na yi cewa in dai muna tare bai cika barin wayarsa a kunne ba.
Da Sauri ya Daukota daga gefe ya duba ganin Tahir ke kiransa yasa ya saci kallona ni kuma sanin baya barina ina sanin wasu abubuwan da suka Dangancesa batare da ya fad'amin ba yasa na kauda kaina kamar bansa ma ana kiransa ba.
Taba Fuskata ya yi Lokaci daya ya na fad'in"Kin fara barci ne?
Cikin kankance idanuwana nace"Eh na fara barci."
Kai Tsaye ya kashe kallon ya Dauke na'urar daga saman jikinsa ya ijiye a saman kujera ya saka duka Hannuwansa ya Dagoni.
Sumbatar goshina ya yi kafin ya dan Rumgumeni Lokaci daya ya na Fadin"To je ki kwanta ko?
Sai na gyada masa kai ya na rike da Hannuna har cikin Daki.
Ya gyaramin in da zan kwanta ni kuma na shiga tiolet na kama Ruwa ko da na fito ya na Tsaye yana jirana.
Na hau gadon ya lulluba min zani a saman kafata ya na fadin"Ki yi addu'a kafin barci ya Dauke ki "
Nan ma sai na kara Daga masa kaina har zai fita sai kuma ya Dawo da Dauri daidai fuskata ya Duko ya sumbaci labbana sannan ya juya ya fita daga dakin ya na fadin"Sai da Safe."
Ina jin ana ta kiran wayarsa bai Dauka ba, sai dai ya na fita ya jawomin kofar dakin ruf ya Rufeni.
Tunanina ya fara kai kawon abunda Assadiq ke boyemin wanda ban sani ba, Sai dai na bi mganar Amma da tace kada mutum ya matsa da sai ya san abunda ba'a so ya sani ba.
Gwara mutum ya yi shuru ya jira Lokacin da aka so ya san wani abun
Addu'an barcin nayi sannan na gyara kwanciya ba Dadewa sai barci.
Shi ko ba a falon ya tsaya ba, sannan ba'a a tsakar gidan ba sai da ya Bude gidan ya fita waje sannan ya Kira Tahir da ya ke ta Uban kiransa.

Tahir da ya gama Fusata ya na Daukan kiran da ya fara fad'in"Kai ammh dai dan wulakanci ne Sadiq."
Sadiq yace"Da na yi me kuma Dahiru?
Tahir ya kasa mgana Saboda Haushi Cikin Kufuluwa yace"Bansani ba. Nace bansani ba, ka manta kace zaka kira dazu?  Yanzu ma kira nawa na yi maka baka Dauka ba?
Sadiq yace"Ina wani abun ne sanda ka kirani yanzu, dazu kuma ai na fadamaka uziri na ko?
Tahir yace"Ah Lalle Sadiq me ka koma yi a zariya?
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Me kuwa? Karatu da aiki mana."
Domin daman Tunda ya rika ganin Kiran Tahir a kai akai a ransa yasan yaji Labarin dawowarsa zariya.
Cikin son sanin wani abu Tahir yace"Ammh shine baka gayamin ba Sadiq?
Sadiq yace"Ga shi yanzu ina fadamaka."
Tahir ya sauke Numfashi kafin yace"Anty Surayya ce ta kirani. Nan ya shiga gayamasa duk suka yi da ita.
Ya karishe da fad'in"Sadiq ka tabbata ba domin Hasiya ka dawo zariya ba?
Sadiq yace"Wata Hasiyar kuma? Akwai wani abu tsakanina da ita ne yanzu?
Tahir yace"Babu, ammh kuma dawowarka garin shima baya cikin Tsarin da muka yi mgana dakai."
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Tahir aiki na samu, kuma tunda na samu wannan damar sai na kara wata damar na Cigaba da karatuna"
Tahir yace"Shikenan ammh ka kula Anty Surayya tace ka sauya hali sannan ta Umarceni da na saka ido a kanka.".
Sadiq cikin Halin ko in kula yace"To ka yi mata abunda ta saka baka da matsala da ni."
Tahir na Dariya yace"Har da Labarin wannan Zabiyar na bata?
Sadiq yace"Duk ka yi daidai ne."
Tahir yace"Kace eh mana in ba Tsoro ba."
Sadiq yace"Ni cikakken Namiji ne kuma Tsoro ba shi da Gurbi a wajen Cikakun maza Tahir.".
Tahir ya sheke da dariya Lokaci d'aya ya na fadin"Namiji Maza!
Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Tahir. Tahir mu kwana lafiya."
Tahir ya yi saurin tare shi da fadin"To a ina ka ke zaune yanzu?
Sadiq yace"Uhm nan kusa da kamfani mu na samu wajen zama saboda yafi kusa."
Duk yadda Tahir yaso ya gano wani abu Sai da Sadiq yasan yadda ya yi suka Rabu Lafiya batare da ya gane wani abu ba.
Sadaf sadaf kamar mara gaskiya ya koma Daki ya Rufe kofa, Hasiya ya fara lekawa yaga ta samu barci karisa shiga dakin ya yi ya shiga makewayi ya kama ruwa sannan ya fito ya sauya kaya zuwa jallabiya ya koma Falo bayan ya kara gyarama Hasiya kwanciya saura kiris ta fado kasa.
Akan doguwar kujeran da ya saba kwana ya kwanta ya fad'a Tunani bayan ya yi matashi da Hannayensa.
Tunanin makomar wannan Boyayyiyar Rayuwarsa nasa ya ke yi, ya na da tabbacin yadda Big sis ta fara zarginsa bazata yi kasa a gwiwa ba sai ta Binciko komai kuma Faruwan haka daidai ya ke da Tsarwatsewan komai batare da ya Shirya ba.
Chapter 52 · 0% Book details