← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 75

Sashe 41

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka yafad'a lokaci d'aya ya na kallona cikin Kaushin murya kafin ya taso daga inda ya ke yazo gabana ya zauna ya tankwashe kafafunsa kamar mai Daukan karatu wanda har gwiwar kafafunsa na dukan gwiwan kafafuwana. Cikin Kaushin murya ya bud'e murya ya kira sunana "Hasiya." Na amsa masa cikin dashewar murya kafin naji yace"Dago kanki ki kalleni ina so zan yi miki mgana ne, kuma ina so ki bude kunnuwanki dakyau ki Saurareni." Ya fad'a ya na kallona kai tsaye sannan Fuskarsa ba Fara'a ballatana a yanayin muryansa na Fahimci babu wasa acikin mganarsa. Dagowa na yi ina kallonsa ina mai Tattara duka hankalina garesa. Cikin Tattausan lazafi yace"Hasiya waye ya Hallice mu? Kai Tsaye nace"Allah ne ya Hallicemu? "Waye mahallicin sammai da kassai? Nan ma na amsa masa da cewa"Allah ne" Ya kara cewa"Waye Mahallicin Tsuntsaye da Dabobbi? Cikin mamaki wannan karon na kallesa sai na ga da gaske ya ke tambayoyinsa ba wasa a saman Fuskarsa. Ni kuma tambayar ce na raina musu ai ko yaro dan shekara uku yasan Allah da abunda ya ke tambayana. Shi ya katseni da fadin"Kin yi shuru" Da sauri nace"Duka Allah ne Mahallicin komai da komai da ke cikin wannan Duniyar sannan shi ke da Duniyar gabad'aya da abunda ke cikinta." Cikin jinjina kai yace"Good. To kinsan haka Hasiya meyasa ki ke tunanin ke ce ki ka yi sanadiyar rasa Dukiyar mijin ki na farko? Sannan me yasa ki ke tunanin ke ce da alhakin Jinyar mijin ki na biyu? Sai naji na kasa mgana na yi tsuru ina kallon kafafuwana ina wasa da yatsun hannayena. Ganin na yi shuru yasa ya cigaba da fad'in"In dan har kinsan Allah ne Ubangijin duniya da abunda ke cikinta to ya kamata ki daina bari Tunanim mutane na Gurbata naki Tunanin Hasiya. Duk Abunda ki ka ga ya faru da bawa daga Rabbil Izzati ne shi ke da ikon aikata duk abunda ya so a kuma Lokacin da ya so sannan wani abu bai isa ya samu Dan Adam ba, face abunda Allah ya kaddara masa cikin Kaddarorinsa." Maganganunsa sun shigeni matuka da suka sanyayamin jiki. Cikin nadamar tunanin da na yi na kashe kaina na Dago idanuwana da suka cika da kwallah ina kallonsa kafin yace"Ba ni na ce ba Assadiq mutane ne ke fad'in haka a kaina Tun kafin ma na girma. Ana zargin ni ce Silar karayan arzikin Baba sannan ni ce silar mutuwarsa sannan ni ce Silar lalacewar Rayuwarmu har da Ciwon Amma da bayajin mgani." Sadiq ya yi shuru ya na kallona ina ta sharan kwallah kafin yace"baki amince da amsarki ta farko ba kenan Hasiya? Da Sauri nace"Na amince wlh." Kai Tsaye yace"Ke musulma ce kin shaida Allah Ubangiji ne sannan Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam Manzonsa ne ko? Nan na d'aga masa kai, cikin taushin muryansa ya cika da fad'in"Kin kuma amince da karban kaddara mummuna ko kyakyawa daga Ubangijin ko? Sai na kara gyad'a masa kai da Sauri ya rike hannayena cikin nasa hannayen muna masu kallon juna kafin cikin Muryansa mai yanayin kashe jikin mace yace" To ki sani wannan al'amarin daga Allah ne, sannan Faruwarsa kuma ta Sanadin ki, shine kaddara mummunan da ake mgana Hasiya, in kika yi hakuri zaki cinye Jarabawarki in kuma ki ka kaza to zaki fad'i daga wannan Gwajin da Ubangiji ke miki Saboda Auna imanin ki." Amma ta sha zaunar da ni ta yi min nasiha ammh mganganun Assadiq sun kara sanar da ni wani abu, sannan sun kara Budemin ido sosai na Fahimci Ubangiji shi ke da Alhaki da duka Rayuwar duniya da Komai da ke cikinta. Sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Allah na Tuba Astagfirullah na tuba Allah dazu fa har tunanin kashe kaina sai da nayi Assadiq" Ido ya bude da Sauri ya na kallona kafin cikin Daga murya yace"Ke baki da hankali ne? Kinsan hukuncin wanda ya kashe kansa ko? Wutar Jahannama Khalidina Fiha Abadan Hasiya." Jikina na rawa na kara Jimke hannuwan Assadiq ina kara fadin"Ai nace na Tuba bazan kara ba Assadiq." Cikin Kaushin Murya yace"Kada ki kara wannan Tunanin komai ya yi Tsanani mganinsa na wajen Ubangiji duk sanda wani abu ya so ya gusar miki Da tunani ki ambaci Allah shi zai kawo miki dauki a daidai wannan Lokacin kin ji ko? Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ina zubar hawaye. Cikin muryan kuka nace"Ka yi hakuri." Cikin Tausayina da ya cika Kirjinsa ya Saki hannayena, sai ji na yi saman Fuskata ya na sharemin hawaye cikin sanyin murya yace"Ki daina kuka ba abunda zai faru sai alheri kin ji ko? Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ammh hawaye na sun ki daina Fitowa da kwarmin idanuwana. Kawai batare da zato ko tsammani ba sai na kara tsintar kaina saman Kirjin Assadiq a karo na biyu. Lokaci d'aya hannayensa a bayana ya na Bubbugawa kad'an kad'an alamun lallashi da ban baki. Ni kuma na samu waje sai na kara baje kaina a saman kirjinsa ina shakan kamshin Turarensa da ya fara sanyamin natsuwa. Ban sani ba har barci barci naji na neman kwasata ammh yunwar cikina bata barni ba sai ji nayi cikina na kuka Kuwwyaahh..! Kunya ta kamani sai na fara kokarin Dago kaina sai ya sakeni jin na daina kuka. Ya na kallona yace"Cikin ki ke wannan kukan? Cikin kunya na daga masa kai da Sauri yace"kina da Ulcer sannan ki na zama da yunwa ko? Sai na kasa ba shi amsa saboda kunya illah fara kokarin mikewa da nayi, ammh sai jiri ya kwasheni da yasa na kusa Fad'uwa sai da ya mike ya tareni ya na fadin"Kin gani ko? Zaunar da nayi ya yi a kan daya daga cikin kujerun falon ya na fadin"Bari na sama miki ko ruwan zafi ne ya warware miki ciki" Cikin sanyin murya nace"Na dafa abinci ya na nan cikin tukunyar da ke kan gas." Bai kara cewa komai ba ya shiga kitchen din da kansa. Ni kuma ganin haka yasa na mike dakyar duk da ina ganin jiri na Kwashe jakarsa da akwatinsa da ke nan Tsakar daki na kai masa cikin Dakina. Ina fitowa muka Had'u da shi ya fito yana ganina yace"Ba na ce kada ki tashi ba? Da sauri nace"Kayanka na shigar maka da su ciki." Sai ya kalli inda ya watsar da kayan yaga ba su sai kuma ya Dawo da kallonsu kaina na cire Hijabin jikina karemin kallo ya yi yana ganin Ramar da nayi. Ni kuma ganin kallon da ya ke min yasa naji kunya na koma na zauna da Sauri ina Rarraba idanuwana kamar wacce ta yi karya. A saman kaina naji mganarsa" Gas bai kare ba ne har yanzu? Dagowa nayi ina kallonsa kafin nace"Ya kare ranar da Habiba ta zo na bata cikin kudin da ka barmin taje ta sakamin" Kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa ya koma kitchen din. Daman Dubu goma ya barmin kayan miya kawai nake siya da shi sai gas din da ta cikomin, sauran kudin na nan cikin Wadrope dina. Gas din ya kunna ya saka Ruwan zafi sai da ya jira ya tafasa sannan ya Juye ya zuba min a wani karamin kofi. Ruwan Bombita ya had'amin na fara sha saboda ya warware min ciki tunda ina da Ulcer ba na shan Lipton. Sai bayan na sha ne na ji na Fara Dawowa daidai sannan ya zubomin shinkafa da wakem da na Dafa na ci shi kuma yace sai ya yi wanka da ya shiga ciki yaga ba Ruwa a bambon makewayi sai ya fito ya na tambayana ban samu almajirin da zai fara zubamin Ruwan ba ne? Nace masa ban samu ba ni na ke zubawa da kaina. Kai tsaye yace"Shiyasa duk kika rame salon muje gaida Amma ki sa tace ba na kula da ke." Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba ammh a raina sai da nace ita kanta Amma tasan tun chan daman ni Ramammiya ce. Assadiq da kansa ya zake ya rika Fita chan wajen Famfo da botikai ya na Dibomin ruwa da na gama cin abincin nace ya kawo botiki d'aya na tayasa sai ya hanani yace naje na kwanta na Huta. A lokacin a wajen Famfon ne kuma ina da Tabbacin daga Ummi har Fadila suna leken mu ta windunan su. Ya Dauko Botikai biyu a Hannunsa da Ruwa na matsa masa ya bani guda d'aya kai tsaye ya kalleni kafin yace"Ba na ce ki je ki kwanta ki Huta ba ne? Zan yi mgana ya Dakatar da ni da cewa"Ba na son gaddama ki je ki kwanta." Jin abunda ya fad'a yasa na juya shi kuma yabi bayana zuwa cikin Daki. A falo na kwanta yace na tashi na shiga ciki bani da yarda zan yi tashi nayi na koma ciki na kwanta. Daman ya gama cika na Tiolet sai na Kitchen ne ya ke cikawa. Kamar ko ya sani barcin nake ji ina kwanciya sai barci ban farka ba sai Hudu saura. Naga abun mamaki Assadiq bayan Ruwa Sai da ya sharemin daki tas ya goge kuma ya kunna Turaren wuta daman jiya da yau dakin bai ga shara ba, na iskesa har ya yi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya ya na falo a saman kujera ya yi barci. Kunyar duniya ta kamani da naga har kitchen ya gyaramin sai dai bai yi min wanke wamke ba na ga dai shima yaci abinci tunda ga Filet dinsa nan alamun ya ci ba da jimawa ba. Kunya ta saka na koma ciki nima na zuba Ruwa a botiki na yi wanka Tunda garin akwai rana. Sai bayan na fito wanka ne ina Daure da zanin wanka na Daure gaba ya shigo Dakin. Da Sauri na yi kasa da kaina ina Raruman Hijabin da zan sanya. Bansan ko ya kalleni ba muryansa naji ya na fadin"Zan yi alwala." Ni dai har sai da ya dauro alwala ya fita sannan na iya sauke Numdashin da na rike da Sauri na shafa mai na saka Wata Doguwar rigata na Atamfa. Daman na yi alwala sai nima na Tada sallah na idar kenan naji shigowarsa kamar ya shiga kitchen sai na tashi na leka sai naga Pure water ne ya siyo
Chapter 41 · 0% Book details