← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 75

Sashe 21

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mika masa kulan Hannunta ganin yadda ya wani Daure Fuska ta na fad'in"Ok ga shi na ta ne." Ba musu ya saka hannu ya karb'a Lokaci daya ya na fadin"An gode." Daga haka bai jira cewarta ba ya maida kofar ya Rufe a saman Fuskar Ummi da ta rike baki ta na bin kofar da kallo. A ranta tace Mijin Hasiya ba shi da Fara'a daga haka ta wuce ta koma Dakinta itama ta maido kofarta Ta rufe. Kitchen din ya shiga da kansa ya ijiye mata kulan, sai kuma ya tsaya ya na Dube Dube sai ya fahimci ta na bukatar cefane tunda ga yan kayan miyan nan ma duk sun bushe da ta shanya a kasa kuma ma ba su da yawa sosai. Fitowa ya yi daga kitchen din ya na wani nazari hakkin sa ne cafane da komai da komai ammh kuma shi bai san yadda tsarin zai tafi daidai ba. Wasu abubuwan bai san su ba tunda shi bako ne a harkan. Har sai da ya zauna sannan ya tuna da cewa Bai tasheni ba. Sannan ya kara mikewa ya koma Bedroom din daga bakin kofar ya tsaya bai shiga ba ya na kiran sunana a Hankali. A cikin barci naji kamar ana kiran sunana ban tashi ba domin na Dauka ina cikin mafarki ne. Sai na juya har ina gyara kwanciya sai naji an ja kafata lokaci daya ana fad'in"Bazaki tashi ba? Sai alokacin na tabbatar da cewa ba mafarki ba ne. A sannu sannu na bude idanuwana sai ga shi fes a kansa ya na tsaye ya harde hannayensa saman kirjinsa ya na kallona, kara lumshe idanuwana na yi saboda har Lokacin barci ne acikin idanuwana. Ganin haka yasa ya kara ja min yatsan kafata ya na fadin"Tashi ki yi sallah mana." Kasa ta shi nayi sai naji gabadaya gabbaina sun saki sai na kara juyawa ina Umh.! Ammh na kasa ta shi batare da Tunanin komai ya saka hannunshi Guda d'aya ya Dago kaina sai gani zaune kan Duwawuna a saman gado ina raba ido cikin tsoro da mamaki. Kai tsaye ya kalleni ya na fadin"Kin yi sallah ne? Kai na girgiza masa ina sosa idanuwana alamun a'a. Bai kara mgana ba sai da ya juya zai fice sannan yace"Ki tashi ki yi salla" Kai tsaye kuma ya fice na bi shi da kallo na dad'e ina zaune kasala ta Rufeni kafin na rarrafa na sauko daga kan gado na fad'a Tiolet na dauro alwala sannan na zo na yi sallah. Bayan na idar sai na fara gyangyad'i saman Darduma har da jin jigina da jikin gado. Sai naji kamar Danwaken da naci ne duk ya bi ya kashemin jiki na kasa jin karfin jikina. Sai kuma wani barcin ya kara kwasheni bai dadi cike da mafarkin wai gani da Amma muna ta Hira. Shi kuma ya na falo aikin da ya ke ya Daukesa lokaci mai Tsawo kafin ya gama. Ya lekani ya ganni saman Darduma ina barci sai kawai ya yi mirmishi abunda yasa bai kara tadani ba ganina saman Darduma yasa yasan na yi sallah kuma shi a tunaninsa tsoro da kadaici baya barina barci shiyasa yau na ke ta yin na rana. Shiyasa bai tadani ba har aka kira sallar mangariba. Lokacin ya gama amfani da Laptop dinsa ya maidata jaka agogon Fatan dake hannunsa ya duba ya na auna Lokaci gwara yazo ya tafi kada dare ya yi masa ammh gobe zai Dawo Saboda ya yi min cefane abunda ba ni da shi. A toilet d'in dakina ya shiga ya Dauro alwala sai da ya fito sannan ya yi amfani da Ruwan hannunsa ya yarfamin a fuska da yasa Dole na mike zaune ina faman mutsakan ido. Cikin yanayin maganarsa yace"Kinga an kira sallar mangariba" Da sauri na waro ido cikin Muryan barci nace"Mangariba kuma? Na fad'a da Sigan tambaya. Mirmishi ya yi min yana maida agogon hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"Eh ki ta shi hakanan ki yi sallah kada ki koma barci ki bari sai kin yi sallar isha'i sai ki koma ki kwanta." Ban samu zarafin mgana ba naji yace"In na fita daga chan zan wuce sai gobe zan dawo" Har ya juya zai fice sai kuma ya juyo ya na fadin"Na manta ki rubuta abubuwan da ki ke so na cefane gobe zan zo kin ji ko? Kamar wata gaula haka na gyad'a masa kai. Sai ya fita daga dakin inaga yaji ni shuru ban biyosa ba me yasa ya kara lekowa ya ganni na zaune na kasa ta shi. Cikin mamaki yace"Ki zo ki rufe kofa zan tafi ne." Sai a lokacin na yunkura na mike jikina duk ya mutu, na bi bayansa salau salau. Har zuwa bakin kofa ya na rataye da Jakarsa ya fita sannan ya juyo ya na kallona inaga ya fahimci har lokacin barci bai sakeni ba ne yasa yace"kada fa ki koma ki kwanta baki yi sallah ba." Nace Toh ina Hamma, kai ya kad'a kafin yace"Sai da Safe." Nima cikin muryan barci nace"Sai da Safe." Sai da ya wuce sannan na maida kofata na kulle na dawo falo na zauna kan kujera ina faman lumshe ido. Sai da na bata lokaci a zaune kamar bazan ta shi ba sannan na tashi naje na Dauro alwala na zo na yi sallah. Kiran wayata ya fito da ni daga Daki zuwa Falo ina Dauko wayar naga shi ne ke kirana. Da Sauri na Dauka haka kurum sai naji gabana na fad'i. Kafin ma nayi mgana naji muryansa ya na fadin"Ina fatan kin yi salla ba barci ki ka koma ba? Sai da na amsa masa da kai sannan na Tuna baya gabana sai da na yi saurin cewa"Eh na yi." Shuru ya biyo baya kafin yace"Ki Rubuta duk abunda ki ke so kin ji ko? Sai na amsa masa da Toh. Yace sai da safe nima nace sai da Safe. To wayarce ta sa na watsartsake daga barci na fara game. Yau ko Amma ba mu yi mgana da ita ba, naa kira da Safe network bai sa na sameta ba. Bansan Ummi ta aikomin da abinci ba sai da na shiga kitchen na gani sai na samu tabbacin sanda ina barci ta kawomin shi kuma ya karb'a Dambun shinkafa ne da Zogale shi naci na sha ruwa na kwanta. Da safe da muka hadu a bakin Famfo bayan mun gaisa na mata godiyan abinci. Sai ta yi mirmishi kafin tace"Ashe megidanki ya dawo jiya? Da Eh kawai na amsa mata daganan sai na Datse maganar. Bani da takarda da Biro wajen Ummi na ara kafin ta fita na Rubuta masa abubuwan da na ke so na Cefane. Kayam miya me sai kayan lambu sai mangyad'a da ya kusa karewa sai kayan maggi su kenan na Rubuta masa. Sai flower saboda ina so na rika Dan sululu da wainar Fulawa. Ina da tabbacin zai zo tunda yace shiyasa ko kafin yazo na yi wanka na har da kwalliya na yi na saka Jan baki da Hoda da Kwalli. Sannan na Fesa Turare yau ma kamar jiya daga wajen aiki ya biyo ta nan ya iske na Dafa Shinkafa da wake da mai da yaji ammh shi sai na soya masa manja saboda yace min da shi ya ke so yaci. Ammh bai fara ci ba sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci saboda Rana ta Daga yasa yace sai la'asar zai fita ina gani ya kwashe wayarsa ita kuma Na'urar yau na cikin Jaka bai Fito da ita ba A gajiye ya ke yasa a kan kujeran da ya ke zaune barci ya kwashe shi. Abun mamaki ana fara kiran sallar La'asar ya tashi. Takardan ya karb'a ya duba baice komai ba ya saka a aljihu ya fita zuwa masallaci. Bai gayamin dagachan zai wuce cefanen ba shiyasa da naji shuru sai nayi tunanin ko ya tafi ne? Ammh ya tafi kuma ya bar jakarsa a nan? Ashe cefane yaje ya yo sai ga shi da ledoji niki niki kuma kamar na sani ban rufe kofata ba. Dakyar ya bani Leda Biyu yace wai bani da karfi bazan iya ba. Ni ya na bani mamaki wai bazan iya ba? Kayam miya ne da kayan lambu sai abubuwan da nace. Sai kifi da Nama da ya siyo sai dankalin Turawa da na Hausa sai mangd'aya king na karamar Roba. Shi ya tayani muka jera komai a muhallimsa kifin da Naman yace na soyasu kada su lalace tunda bani da Fridge. Bansan bayason karnin kifi ba sai da naga bayan na wanke na fara Soyashi ya bar Falon ya koma bedroom dina har ya na Turo kofa. Sai da na shigo ya fara Toshe hanci ya na cemin na rufe kofar baya son karnin Kifi amai ya ke saka shi. Cikin mamaki nace"To kasan baka so meyasa ka siyo? Kai tsaye yace saboda ni baisan ko ina so ba. Sai naji raina ya yi wani haske jin haka yasa ina gama soya kifin daman naman na fara Soyawa na dake na goge kitchen din da omo har Falon ma na share na goge na kunna Turaren wuta na tsinke da na Rushi da Adda Rukkaya ta kawomin. Sannan Ummi ma ta dibar min nata yau bata dawo da wuri ba kila gida ta Biya. Ina so na yi wanka ammh ya na Dakin kuma in na shiga zai ji karni Saboda kayana da ni kaina ina karnin kifin ne. Sai kawai na fara greetin din kayan miya na Dora girki Shinkafa da Miya na Dora sai kuma na fara yanka kabeji da zan yi salat da tun tuni na iya shi a gidan Adda Fati. Ina kitchen din ya fito yace zai je masallaci. Ina jin haka na fito da Sauri sai dai ban zo kusa da shi ba daga kofar Kitchen din na Tsaya ina fadin"Ammh ba dagachan zaka wuce ba ko? Kai tsaye yace"Dagachan zan wuce me ya faru ne? Sai na samu kaina da marairacewa ina fadin"Don Allah ka dawo kaci abinci." Shuru ya yi kamar mai nazari ganin haka yasa na kara sauke murya ina fadin"Kaji ASSADIQ. Don Allah na ce in ka ci sai ka tafi." Kallona ya yi cikin ido kafin yace"Bazaki
Chapter 21 · 0% Book details