← Book details Tmw Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 75

Sashe 1

Tmw Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*TMWB2K001*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj

Kamar wasu zakaru haka suka tsaya a bakin hanya suna kallon juna.
Shi Sadiq ya Rufe kwayan idanuwansa ammh da ya bayyanasu da rauninsa ya bayyana, sakamakon Tahir da ke kallonsa cikin takaici da wani irin bakincikin da bai taba tsintar kanshi aciki ba.
har gwara ace Mutuwa a kayi da wannan Danyen Hukuncin da Sadiq ya yanke ma Rayuwarsa.
Tahir bakinsa ne ya yi nauyin da ya kasa mgana shi kuma Sadiq ba shi da kalaman da zai kare kansa a lokacin.
Har abokan aikinsa da ya gayyato Anas da Mudansir ba yan zariya ba ne dukkansu yan cikin garin kaduna ne.
Zuwa suka yi suka ba shi hannu suka yi musabaha tare da yi masa murna.
Duk da auran nasa ya ba su mamaki lokaci d'aya haka, Sannan ba kamar sauran aurarrakin da suka saba zuwa ba ne wannan sai ya zame musu kamar Dabam.
Ammh kamar yadda Sadiq ya yi musu gim da fuska Haka Tahir ya kallesu ya watsar shi ko hannun bai mika musu ba sai ya koma jikin Bangon gidan Baba Tanko ya jingina bayansa lokaci d'aya ya hard'e hannayensa a kan kirjinsa ya na hangen Sadiq yan Tsirarun mutanen da ba su watse ba suna ta faman yi masa Allah ya sanya Alheri cikin su harda Isuhu duk da shima ya yi mamakin faruwar auran da gaggawa haka kuma shi Adda bata fad'a masa da wani daurin aure ba ta kuma tabbatarsa masa Amma da Hasiya zai Dauko ya kawomata ammh ganin abunda ya faru sai yasan dole Lissafin ya sauya.
Bai jira sauraran Habiba ba ya hau mashi ya koma Samaru.
Ya bar su Sadiq a kofar gidan Baba Tanko Tsaye mai afkuwa ta riga ta afku shiyasa Sadiq ya ji gabadaya duka kalaman bakinsa sun kare shi kuma Tahir kafafunsa ne suka yi sanyin da suka kasa Daukansa ballatana yasan mafita bayan sun fito daga wajen da aka daura auran da har Abada ba yajin zai iya goyama Sadiq baya akan wannan Shirmen nasa.
Suna nan tsaye sai ga Adda Fati da Habiba sun fito tun daga nesa ta ke kallon Sadiq wanda ya coge a tsaye duka Hannayensa suna cikin Aljihun wandonsa kansa kuma na kallon kasa bazaka iya Fahimtar a wani yanayi yake ciki ba.
Ita kanta mamakin bai gama Sakinta ba tunda yaran Baba Tanko suka shigo da labarin Daurin auran Hasiya bata tsinke da Lamarin Amma ba sai da Baba Tanko ya shigo shima ya ke fad'in Daurin auran da kanshi.
Har Adda Fati tayi subutan baka tace masa"Da wa aka daura ma Hasiya aure Baba.?
Kai tsaye ya kalleta kafin yace"Da wanda uwarku ta aiko ki da shi mana"
Daganan sai Adda Fati ta Fahimci Tsakiyar labarin da Karshe. Farkon ne yanzu kad'ai ya rage ta sani shi kuma Amma ke da Hakkin da zata fidda kowa acikin Duhu.
Sanda ta kariso wajen ta na so ta yi mgana ammh itama sai bakinta ya yi mata nauyi kawai sai ta Rausayar da kai ta na fadin"Mu je ko?
Ta yi gaba Sadiq ya taka ya bi bayan Habiba wacce sai ta juyo ta kallesa ta koma kuma ta kalli gabanta ta kasa yi masa mgana shima kuma ya kasa ko sakar mata fuska yadda ya saba.
Tahir ne bai bi bayansu ba Sadiq ya juya ya na kallonsa kafin yace"Tahir.".
Tahir ya kallesa kai tsaye batare da ya taso ba, Ballatana kuma ya yi masa mgana.
Sadiq yasan daman haka zata faru zai Fuskancin Turjiya ta hannun Tahir. sai dai gwara Turjiyansa bayan Komai ya faru da Turjiyansa kafin hakan shine babban matsala tunda ya tabbata bazai taba barinsa ya cika wannan ladan na taimako ba.
Sai da yaje da kansa ya riko hannunsa Sannan ya biyosa. Suna tafe har bakin Titi Adda Fati ta sake tsaida musu abun hawa kamar na dazu suka sake shiga sai Samaru har kofar gidan su Hasiya.
Wannan karon da suka sauka Sadiq ya biya kudin adaidaitan.
Sun iske Ana ta loda kaya a budaddiyar motar da Isuhu ya kawo saura ma kad'an a gama. Sadiq ya manta da zencen ta shin su Amma shi kuma Tahir dariya ce ta kusa kamashi ya zata kayan auran Hasiyan ake lodawa sai ya kalli Sadiq ya na fad'in"Gusau za'a wuce da kayan auran ko Shinkafi?
Sadiq ya kallesa cikin mamaki shi kuma ya na dariya ya nuna masa motar kayan.
Sadiq ya yi tsam bai yi mgana ba Tahir kuma kai ya girgiza kafin yace"Na kasa gane abunda kuma muka sake dawowa nan muna yi a tsaye."
Sadiq dai bakinsa gum bai yi mgana ba Tahir sai k'ak'alan mgana ya ke Sadiq ya tankasa ya yi masa bore.
Adda Fati ko ta na shiga gidanmu matan gidammu suka yo mata caa fad'i suke yi ashe kuma an Daura Auran Hasiya? Cikin sakewa ta ke amsa musu da cewa Eh ko dai na munafunci ne suna ta fatan Alheri.
Ta na daga labulen dakin mu dukkanmu muna inda ta barmu labarin da muka samu baisa mun iya dagawa daga in da muke ba.
Amma ce dai ke ta zirga zirganta sai Inna Talatu da tare da ita aka rika fita da kaya ita da yara zuwa waje.
Amma na ganinta ta washe baki ta na fad'in"Fati ya aka yi ne?
Adda Fati tace"Amma su na waje"
Da Sauri Amma tace"To to..! Ni ta kallah kafin tace"Ramatu ku je dakin Maman boy ke da Hasiya. Zan kira ku daga baya."
Ina jin haka kamar Daman ina kan kaya ne na mike Zumbur  dauke da Hanifa domin ba ni da idanuwan da zan iya kallon Assadiq a daidai wannan lokacin.
Dakin Maman Boy muka shige ni da Ramatu da dukkammu muka kasa yi ma juna mgana.
Ita dai sai kallona ta ke yi ta na mirmishi ta kasa mgana ni kuma sai tunani da ya cika min kaina a raina nake ji Amma ta so kanta in dai tunaninta ne wannan bai kamata saboda jin dad'in ka kai ka jefa rayuwar waani cikin wahala da ukuba hakan ba daidai ba ne.
Bamu san yaushe suka shigo ba an d'an juma sannan Adda Fati ta leko tace mu zo dakim Amma ni da Ramatu.
Daman da Hijabi a jikina tunda kayanmu gabadaya an had'a su waje d'aya sai dai nawa akwatin Amma ta hana a fita da shi ta na jin dadi tace kayana a bar su tukunna ba da ni zata tafi ba gidan mijina zan zauna in sha Allahu.
Hanifa ce ta tashi sai na ari zanin Maman Boy na goyata Ramatu kamar zatayi min mgana sai kuma ta fasa ammh ina ganinta ta na kunshe Dariyanta.
Itace gaba sannan ni ita kuma akaji sallamanta ni dai a saman lebena sallamar ta tsaya kuma har muka shiga na samu waje na zauna ban yarda na dago fuskata ba.
Kusa da Ramatu na rabuke kamar wata marainiya. A sace na kalli mutanen Dakin Adda Fati sai Adda Rukayya Hamma Isuhu da bansan yaushe ya shigo ba. sai Habiba da Inna Talatu ban kalli Barayin Assadiq ba ammh naga kamar ba shi kad'ai bane ne zaune akan Dauduma daga gefen Amma.
Muna zama Amma tayi gyaran murya kafin ta fara fad'in"Hasiya tun jiya ki ke tambayata me na Tattauna da Abubakar ko?
Sai alokacin na Dago kaina ina kallonta a jiyan ne zuwa da Safe na ke neman karin bayani ammh daga dazu zuwa yanzu ba na bukatar wani karin bayani.
Sai dai ban ce mata komai ba na maida kaina kasa ina wasa da yatsun hannayena acikin Hijabina.
Amma ta cigaba da fad'in"Bayan Hasiya ina so kowa anan ya zama Shaida kan mganata. Nasan zuciyarku na cike da Tunanin ta ya ya haka ya faru? mganar gaskiya ni ce na kira Abubakar da kaina na kuma kwance masa komai na labarin Rayuwarmu da Halin da Hasiya ta tsinci kanta aciki sannan ni ce nan na yi masa tayi auran Hasiya batare da Tunaninsa ko cewarsa ba."
Nasan kowa ya kalli Amma alokacin ban da ni saboda nasan daman za'a zo wajen ai tatsuniyar gizo daman bata wuce ta kok'i in ba Rokomsa ta yi ta ina Rayuwata ta dace da Rayuwarsa?
Sai dai na jira ta gama ne duk da ta na mahaifiyata bazan fasa gayamata gaskiya ba abunda ta yi son kai ne sannan ba ta yi daidai ba.
Ba wanda ya tambayeta dalilinta na aikata haka da kanta ta cigaba da fadin"Rauni irin na uwa ita ta sakani aikata haka. Hasiya yata ce na santa fiye da kowa acikin ku. Abubuwa da dama sun faru da ita a kananun Shekarunta wanda ba da son ranta ba ne ina son Hasiya ina kuma kaunar itama ta samu natsuwa da ingantattaciyar rayuwa a gidan auran ta kamar yadda yan'uwan ki suka samu, wannan Kwad'ayin yasa fara ganin Abubakar da Natsuwarsa da Hankalinsa yasa rauni irin na uwa batare da wani Tunani ba na yi masa tayi auran ki Hasiya."
Amma ta karishe fad'a muryanta ta fara rawa alamun kuka.
Sadiq ya dago ya na kallonta mganarta a jiya ta na dawo masa.
Chapter 1 · 0% Book details