← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 68

Sashe 8

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Annoor yau Iman taci sa'a ya kyaleta ta kwana lafiya,suna zaune Jauro ya kira Annoor yace Ko me kuke ku bari muje asibitin mahaukata Maman Iman ance ta dawo hankalinta,Annoor yace to bai fadawa Iman ba sai yace ta shirya suje gidan mahaukata su gano mamanta,sai murna take yi ta shirya,Annoor bayan ya shirya ya saka Shadda wata sky ya zuba kyau harda dora Yar hula a Saman kitsonsa yace zanje wajen surukata tunda ta warke ai taga surukinta kamili,Kansa ya kalla a mudubi ya juyo ya Kalli Iman yace ya kika ganni? tace Kamilu Sunan wani,dariya yayi yace tambaya nake nayi kyau please? tace to Kai akwai ranar da baka kyau ma ai kullum kyau kake yi,mudubi ya sake lekawa yace wow Allah yayi kira,dariya tayi ta ture shi tace kalle ni fa,me zan saka ne ma na sutura? Yace Abaya,ai kuwa ita ta zabo wata maroon Egyptian ta saka tayi kyau sosai kamar a sace ta.

Suna kamshi suka fita shi ke driving a wata sabuwar motarsa da ya siyo,Kawu suka dauka suka tafi can.
Suna zuwa aka kaisu wani daki na daban,sannan a kirata ta fito sanye cikin riga da zani na atamfa har da Hijab,kana ganinta kasan yanzu da hankalinta,shuru tayi tana kallon su,Nurse tace gata Hajiya ki musu magana su suke zuwa dubaki,Jauro yace sannu tace yawwa Dan Allah ku su waye ku kaini gidanmu,Iman farin ciki ya kamata,Maman Iman tace ni Yar kauyen Libiya ce tallan maganin gargajiya ne ya kawo mu kasar Nan da iyayena,Jauro yace zauna Dan Allah ki nutsu ki bamu labarin naki ko zamu San Inda zamu kaiki.

Zama suka yi sannan tace sunana Rahma,Jauro yace yawwa ko kefa Rahma suna me asali,taci gaba Babana sunansa Mahmood tun Ina karama ya rasu,Mahaifiya ta ma Ina karama ta rasu a wajen kakata na girma wacce a kauye muke da zama,tana bada maganin gargajiya,tana amfani da Aljanu,kasa kasa muke zuwa,watarana muka sauka a Nigeria a Daji muke zama da dabbobin mu shanu da rakuma,akwai wani bawan Allah Dan asalin Sudan ne zai wuce Abuja ya ganmu a hanya ya tsaya ya karbi maganin haihuwa a wajen kakata,ta bashi yace Yana so na sai tace baza ta bashi ni ba ya nace a haka dai sai da yasan inda muke zaune a Daji.

Watarana yazo wajena ya samu Kakata bata Nan ya bani wani abinci me dadi da nama tunda na ci ban sake sanin Ina nake ba Ashe magani ya bani yayi amfani dani ya lalata min rayuwa,Sai da kaka ta dawo ta sameni cikin wani hali na fada mata komai amma sabo da taurin Kai Ina sonsa yana so na tace baza ta bashi ni ba,ni Kuma nace tunda Hakan ta faru ai gwara kawai ya aureni a huta,shi Kuma dan Sudan Marwan kenan yayi min haka ne Dan Kaka ta bashi ni ya aureni amma taki yarda.

Ana nan watarana na dinga kuka nace wlh sai na bishi mun gudu,tace indai na sake na bishi sai ta Sa Aljanu sun haukata ni,ban yarda ba watarana muka hada baki da shi muka gudu ya dauke ni a mota,kwana daya tsakani na fara ciwon hauka ban San Inda kaina yake ba,da kansa ya dawo dani wajenta,ranar da ya kawo ni ranar Kuma ta bawa wasu Yan fashi magani sun gwada bai musu ba suka dawo a ranar a gabana suka yiwa kaka Yankan rago suka fece,har a lokacin bana gane abubuwa da dama hankalina ya fara barin jikina,daga nan nidai ban sake sanin Inda nake ba sai yanzu da Allah yasa na warke jiya kenan.
Jauro yace iKon Allah to ko dai Marwan din Dan Sudan shine uban yarki? Tace wa? Ya nuna mata Iman ya kwashe labarin komai ya fada mata,Rahma tace ya kamanninsa suke? Jauro yace Yana da haske dogo yana da gashin Baki goshinsa da tabo,Rahma tace wlh shine masoyina nane Ina sonsa har yanzu a Abuja yake zaune cikin gari yanzu Ina zan ganshi.

Jauro yace Yan uwanki fa? tace bari tukun wannan duk suna Libiya Kuma ma duk sun tarwatse bada magani yanzu burina a Nemo min Baban wannan da kuka ce Yata ce,yanzu wannan 'Yata ce?Jauro yace yarki ce gashi Nan Kuna kama ma,Iman sai murna take yi tace Kinga mijina surukinki ne wannan ta nuna mata Annoor, Annoor yace Ina Kwana harda kasa da Kai.

A ranar aka gama komai aka sallami Rahma suka wuce gidan Habiba aka Kai mata ita ta zauna a nan,sai Iman ake tayawa Murna.
Jauro yace Haidar ya shirya dama za aje wajen ubansa mahaifi a Abuja sai a tafi da Rahma ko za a ga uban Iman a can,Habiba tace ya kamata a bari ta murmure sai a je.

Mahaifin Annoor ya dawo daga US ya samu Yarsa Maryam tana cuta ta gaske an rasa dalili ta rame ta fike,ga wasu kuraje da suka cika mata jiki kamar me Karzuwa ba kyan gani,komai sai anyi mata,haka mahaifiyarta ba maganin da bata karbo mata amma shuru,yace Maryam me ya same ki haka? Maryam tana kwance Saman bed tana kuka ta kwashe komai ta fada Masa,salati yayi yace ai gashi kinwa kanki,Dan uwanki ne shashasha,Allah ya Baki lafiya amma abinda ya sameki kin cancanta ya same ki,bani address din Annoor din,tana numfarfashi ta bashi tace ga wayata Nan a jaka akwai number dinsa ciki.

Hanif zaune yake a dakinsa Yana Shan yogurt da Dan wani spoon na roba yaji dadinta yace Inama wannan Khadija din tana Nan a bata ta Sha taji,a fili yace to Ina ruwanka da ita wai,Mero ce tayi magana tace hello ta sake daukan Karfenta taci gaba da bulawa sosai yanzu ta Burma wajen yanda hannu zai iya shiga guda Daya tace Hakan ma ya isa.

Hannunta me kyau ta mika tace Yaya Hanif Inama sunana Hanifa sai aka sa min Khadija,Babana da kyar ya yanka min ragon suna ance sai da nayi Shekara uku a duniya aka yanka min Kuma wai Yar tinkiya ce ma,shi yasa ma akace bani da kan gado sabo da tinkiya aka yanka min,Hanif ya kwashe da dariya yace wai ke Dan Allah mene birgewarki Dan kin fada,bakya gajiya da surutu a rayuwa,Mero tace ai gaskiya ce dole na fada,yanzu gashi Ina ta koyon yanda zan kame harshe na,tsohon skirt ma da muke tatar Koko da shi ai an Dade yanzu da dankwali na muke yi,ai an samu ci gaba,Kuma da wlh kwandon wanka da muke saka soso da sabulu daga bandaki ake dakko shi mu tace taliyar mu muci Kuma gani lafiya kalau ba ko malaria,Kuma mu bama banbance botikin wanka Dana aikin gida sai muyi wanka da baho mu fito da shi mu kwaba danwake a ciki mu zilillika abinmu.

Hanif yace gaskiya ku kazamai ne,Mero tace ai na waye yanzu tunda aka kaini aikatau na gane komai,da naje ganin gida baka Gani ba yanda na dinga cin gyaran Innar mu,tasowa yayi yazo Inda ta fasa tace Miko bakinki kiji,Mero ta cuno Baki ta cikin kafa tace wlh bakina karami ne karka min kiss wallahi Allah ni bana son Kiss yanzu,ban shirya Shan yawu wani ba,ba a haifi Wanda zan Sha yawunsa ba ni ba Yar iska bace nidai,Hanif tsaki yaja yace ke me zanyi da bakinki baki da hankali,ko wacce zan aura kafin ta mutu ban taba mata kiss ba,Mero tace Alhmdllh Rabin wata ne,Khairat ba rabo ba tana murna tace gaskiya ka fado duk wayewarka ka bari ta koma ga Allah haka ko da yake ba rabo ba.

Share ta yayi Yana jinta tana dariya Spoon din ya sa ya ebo yogurt din ya miko ta kafar Mero ta bude Baki ya zuba mata ta shanye harda zaro harshe tana cewa wash dadi...dariya yayi yaci gaba da bata tana ta sha a haka,Mero kasa kasa tace na sace zuciyarsa saura furta I love you,Azima ta duba ko Ina Bata ga Mero ba dakin ta duba ta samu Mero manne a Jikin bango ana Miko mata yogurt tana Sha tana Santi.

Azima tace Mero me kike yi haka? Mero hannu ta daga ta baya tace ciyar dani ake yi,shi dai Hanif bai san me suke yi ba Azima tuni ta ture Mero ta mika nata bakin yaci gaba da antayawa Azima itama a baki,Mero tace Kai Hanif Kalli labbanta bakake bafa ni kake bawa ba Azima kake bawa haka labbanta suke bakake? Sai lokacin Hanif ya duba da sauri ya janye yogurt dinsa,ya hau masifa kin cuceni kin Bata min lokaci,Mero tace rashin fahimtarka ce amma ai ka dinga kula,Hannu Mika ciki tace ungo,Hanif ya kama yatsanta yaji Laushi,yace ke a haka Yar aiki ce? to gona nake zuwa me ka Mai dani so kake kaji kamar bayan kada,Hanif ya dan rike hannun Mero yace Bismillah zunubi a kanki,dariya tayi Azima tace Dan Allah kizo mu tafi.
Hanif yace wai Ina ruwanki ne kiyi tafiyarki kin takura mata fa,Azima kike ko wa ki shiga hankalinki.

Azima ta juya ta fice Hanif yace Khadija ya kirata a nutse,ta amsa Masa yace ki dinga zuwa kullum zan koya miki rayuwa naga baki Santa ba,ya zaka ce ban San rayuwa ba gashi Ina cikinta kace ban sani ba,Kaine ma zance baka San rayuwa ba tunda Kai kana da kudi rayuwar kudi ka sani,ni da muke talakawa mu muke cikin rayuwa,yace baki gane nufina ba,tace to zan dinga zuwa ai inshaallah.
Bayan kwanaki Mero kullum sai taje sunyi hira sun hade hannu waje daya ta Yar kafa wai kawaye ne.
Chapter 8 · 0% Book details