← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 68

Sashe 57

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Beauty kuwa Mohsin Bai fada mata zai dawo ba amma ya fadawa Abba,yace kar ya fada mata,amma Abba ya shugo gidan sai da yaga Beauty ya dauki jariri yace an fada min wata magana ance kar na fada inji mijinki,Kamar na fada kamar kar na fada,Kubra tace ka fadi me? Dan Allah kazo dama Ina son magana da Kai duk wai Dan kar ya fada ta janye shi,da kyar aka samu Mohsin ya dawo Abba Bai fada ba sai Jin Sallamarsa aka yi da yamma Umma Kubra ta dakko Danta a airport cikin sabuwar motar Abba, Beauty murna kamar me amma a gidan sirikai ne wani abin ba dama,sai kallon juna suke ita da Mohsin kamar zasu cinye juna,suna magana da Ido,yaga ta Sha kyau,Abba yace mutanen Makkah dama yau suka je aka gyara ko Ina na gidanku gashi kayanta ko kunya duk ta kwashe ta Maida gidanku tana sa rai miji ya kusa dawowa sai ku tafi gidanku ai,dama haka ta dinga tafiya gyaran jiki duk sabo da Kai ake yi na sani,shuru nayi kawai ban nuna ma nasan Dan Kai ake yi ba,ta zaci wai ta kife ni,yau mun huta muma zan samu tattalin arzikina ya dawo,Mohsin yayi dariya ya zauna sun dade suna hira,sannan yaci abinci yayi Sallah,Kubra tace ga key din motarka normal an mata komai,ya karba,Abba yace ya labarin su kubri (Saman gada) da su dukkani(Kanti)? ya ka gane min idon takari a can ana korar su suna likewa?
Mohsin yayi dariya sosai yace suna can Abba,yace ya Darul tauhid ka ga Darul Salam a Madina ko? ai Yan biyu ne Hotel din,ya su bakiya anje ziyara? Mohsin shi dai Yana ta dariya Abba a dole yasan ko Ina,shi burin Mohsin a tafi gida ya gana da matarsa da dansa,Amal taga Abbanta sai murna take dama taje hutu wajen Hanan mamanta

Ranar Sunan Beauty yazo dai dai da auren Mufee da Haidar shagali kan shagali,Haidar yayi lefe na gani na fada.
Maryam kuwa kanwar Annoor sai da ta Sha jinya me tsanani ta fita a hayyacinta sannan ta warke a hankali,taci bakar wahala,maganin duniya yaki yi mata aiki.
Bayan ta warke a rame a kekashe tazo gidan Annoor suna Parlo suna kallon film ta shugo tare da zubewa a kasa ta fashe da kuka tana rokon gafara,Annoor Sam bai gane ta ba sai da tace Maryam ce Yaya baka gane ni ba,Annoor ya daka tsalle ya koma gefe Jikin Iman ya makale yace kece Maryam? tana hawaye tace nice,yace Allahu Akbar ko Dan wannan halin da kike ciki ai a yafe miki,na yafe miki,Iman tace ke kuwa ba Kya iya cin abinci haka? Sweet ka ganta sai hakoran kawai,skeleton a fili mun yafe miki duniya da lahira,tace na gode Allah ya saka da Alkhairi,yace Ameen ki daina fitowa haka ki boye kanki ki bari sai kin murmure Allah ya Baki lafiya jeki zamu zo gidan tace to ta mike iska na ibanta,yace zauna ki huta,Iman tace to Kinga dai duniya sai kiyi darasi,taje ta kawo mota abin ci da Sha,taci kadan,Annoor yace in zaki kici ki ci Nan ba wajen kunya bane
Sai da ta gama tace zata tafi,ta fita waje Wanda dama driver ne ya kawota shi ya Maida ta tana Jin dadi sun yafe mata.

Mero taji jiki tace yau sai dai a dauke ni yau ma ,ka gama ragargaza ni,yau na Sha wahala,yace sorry My Angel bari muyi wanka,Mero tace ka fara dai bani ragowar kaza ta naci da tea me zafi hadin Madara,dariya yayi ya mike ya kawo mata abinda ta bukata,ya shiga bata a baki tana korawa da shayi me kauri,gobe Kuma sai naci tsire, idan Allah ya amince jibi Kuma sai a siyo min nama me ruwa ruwa Shima ya Sha cabbage,Haneef yayi dariya yace za a siyo inshaallah,tace ya zama wajibi da yardar Allah,irin wannan wahala da naci ai sai da sinadari me kyau in ba haka ba sai na fara hakoran gaba,yau da kyar zanyi fitsari an min kaciya,Haneef Yana dariya a nutse yana bata tana lamushewa.

Ayi hakuri da wannan naje wajen aiki ne.

AsmaBaffa
[3/9, 9:21 AM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

81-85

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKI NE
Yar Gatan Annabi

Mohsin tun a mota Beauty take Masa korafi yanzu da ba'a gyara gidan ba fa? ai sai ka fada min,ni naga Umma tace Inzo muyi girki ana ta shirya girki na musamman Ina ta mamaki Ashe Kaine zaka dawo,surprise na miki, a'a ni bana so wlh ka daina min haka,sai da ya shiga gidan da motarsa ya rufe gate zata fito yace ki zamanki a mota a ciki zan bare sabuwar Amarya ta,Beauty tace ikon Allah mutum da bedroom da komai sai kace Yan iska,yace ba wani nan na gaji kullum Abu a daki,daga bedroom,Palo,toilet shike nan fa ai a dinga samun canji,yanzu wasu ma'auratan a duniya tunda aka aure su a waje Daya suke Abu daya,wasu basu taba barin bedroom ba,kullum a waje daya ba chanji,ai yanzu ma zamu fara yawace yawacen mu gari gari ko ba kudin fita waje ko su Lagos ai ma dinga zuwa,ga su Kwara state mu kwara kauna a can,Beauty tayi dariya yace ai kune wasu mata bama Kwa so a fita da ku,mijinki Yana da Dan budi ko katsina ai Kwaje kawai aci Aya ayi kauna,Beauty tace ai ni kasan ko nan da inane zanje indai da Kai,suka ajiye Baby a gaban mota suka shige bayan mota kamar Yan iska mota sai Lilo take a compound suna Kwalbewa.

Ranar Sunan Chika Yana zuwa yarta taci Suna Nasreen,an Sha suna anyi shagali.
Naila ana kan gaba har da wani Dj suka kawo sabo da bikin Mufee da Haidar, Iyalan Jauro Maza Abuja suka taho daurin aure,abokan Ango,Mohsin da Abba duk sun zo,Naila tayi tayi su Abba su kwana sun ki,Mohsin ya kawo mata tsaraba sosai,Chika ma an bata da Ikhy Abaya,harda kawowa Spark jallabiya kala biyu masu tsadar gaske fara da coffee color da turare me kyau.
Washe gari aka Kai Amarya Mufee hadadden gidanta kusa da su Iman abinsu sharr, su Iman sune masu tabbar Amarya gaba dayansu yara da su,bayan mutane sun watse Haidar Allah Allah yake ya fada dakin Amaryarsa,ga Mufee Jinin su Zeenatu ba wata kunya ce da ita ba,tayi tunanin wani dadi ne da first night din.
Sai da Haidar yazo suka gabatar da duk wani abubuwa na farkon aure sannan ya goge mata hadda gaba daya,Yar rashin kunyarta data kwaso daga Abuja duk ta Maida abarta cikinta ta hadiye,sai dai bata Sha wahala irin wasu ba,ba yanda ake tsammani ba,washe gari ma da kanta tayi komai tayi girki abinta,Mufee an dage an koyi girki kafin aure,Haidar har wani Santi yake yace daga Jin wannan girkin na tsohon hannu ne tun kina karama kike koyon girki? Mufee ta shararo karya tace ai mu tun muna Yan yara Mima take siyo mana Yan tukwane na yara muna gwada girki,tun muna yin na wasa har muzo ta kaimu kitchen,tana nuna mana zuba Maggi kaza,zuba curry,zuba gishiri kamar haka"a haka har a fara barin mu muna girki da kanmu abinmu.
Haidar Yana Jin dadi Yana washe baki yace ai da gani Kun samu tarbiyya sosai,haka ake son iyaye,Mufee tayi dariya a ranta tace shiryuwa kawai muka yi muka ga rayuwa haka baza ta kaimu ko Ina ba muka canja,a fili Kuma tace gaskiya sai dai mu godewa Iyayenmu,Haidar yace bazan taba godewa nawa ba sai dai Kawu Jauro da Umma Habiba,suyi min laifi na gode musu a wanne dalili,Ina dai ganin girman su Ina mutunta su a matsayinsu na iyaye,Kuma bazan yarda wani ya wulakanta su ba amma na gode musu akan me,me suka yi na bajinta a kaina, Allah ya kyauta dai,Mufee tace Ameen ai ba laifin mama,yace to da sauki dai,dariya tayi suka koma hirarsu ta kauna.

Bayan wasu watanni Naila cikinta ya tsufa sosai bata da karfin masifa yanzu sai kuka da fushi,yau da dare ta kasa kwanciya ta juya gefen dama taji bata Jin dadi,ta tashi zaune ta juya gefen hagu,Spark Yana ta latsa waya abinsa bai San ma tana yi ba Yana kwance a gefenta,Naila tace ayi bawa idan zai juya ma ba dama sai ya mike zaune kafin ma ya juya,da a baya ne sanda nake lafiya birgima nake yi harda kwanciyar banza amma yanzu idan na Isa nayi mana,Spark Yana jinta yayi murmushi bai ce komai ba,juyawa ta sake yi ta Kalli sama tace wayyo zan mutu ta mike ta jingina da Jikin gado sannan taji dadi,ta zauna a haka ta Kalli Spark haushi ya kamata ko sannu duk wahalar da take Sha,tace idan na haihu idan na kyaleka ka aiki yaron nan shegiya nake,wannan wanne irin Abu ne Allah yasa na haihu kazo daukansa bazan bayar ba,Kuma baza ka aike shi ba ko kofar gida,sai mace ta haihu ku damu mutane da Danku Danku akan me,sai an haihu ku zake kufi mata iko da yaran ku sai kace Kun San zafin su,Spark yace sannu yi hakuri,wayarsa ta kwace ta kashe gaba daya ta ajiyeta a gefe,hannun Spark ta jawo ta dora a Saman cikinta, yaji yaro Yana ta motsi a ciki ana ji,dariya yayi yace kin ji shi,Naila tace ae haka kuka iya ai dama,wlh watarana kamar na cinnawa kaina wuta haka nake ji sabo da halinka,na tsani kaina da kaina na gaji da cikin nan wlh ni bana so bazan sake haihuwa,ko na haihu nayi arba'in baza a kwalbe ba,duk dadinsa na hakura ai Kwalbewa ce ta jawo min,na damu kaina ban haihu ba ashe wahala ce bazan sake ba,Spark yayi dariya yace daga farawa ai kuwa na gaba Yan biyu ne zaki haifo Inshaallah,Naila ta fashe da kuka wlh bazan Haifa ba bana so,to kiji da wannan tukun yanzu tun baki samu na Yan biyun ba kike musu kuka? a guda daya ma Ina Jin haka Ina ga Yan biyu,a zaune tayi bacci Naila Allah sarki a jingine ta kwana,sai da Spark ya tausaya mata kamar ya mata kuka,ya dade baiyi bacci ba Yana kallonta tana bacci a haka.
Chapter 57 · 0% Book details