Sashe 21
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haneef kuwa har yaje Office Yana tuna Khadija Yana ta dariya shi kadai Yana Jin dadi,yace gaskiya fa yarinyar take fada na Kara auren nan yafi kawai,dama Mamana tana fada min ko waye ya bani shawara indai na duba naga ta kirki ce kawai nayi aiki da ita,kullum Ina bukatar mace amma ba dama,gaskiya zan dauki shawarar Khadija wannan ai me kaunata ce,Allah sarki tana so na samu nutsuwa Kuma gashi madarar Nido fa ta taru,wannan Yar iskar kuwa ko bata da lafiya wa ya sani ma ko aljani ya aureta oho,ba komai bari na dawo gida.
Mero tana kitchen ta dora abincin rana Ihsan ta shugo ta bangajeta ta wuce ta dauki lemo a fridge ta fita,tukunyar Mero ta sauke tace yau sai yamma zanyi girki kowa yaci nade da Mai yau kin jawo wa kanki,sai Haneef zai dawo nayi masa,ta kashe gas ta fito ta wuce dakinta da biscuits da Madara,taci ta koshi tayi Sallah ta kwanta ta dinga baccinta har da cire kaya daga ita sai vest da pant .
Yunwa ce ta damu Ihsan taga abinci shuru shuru gashi so take taci ta fita ta Sha wanka cikin material me tsada,fitowa tayi kwas kwas tana kwalawa Khadija kira,tafi karfin ma ta kira sunanta sai dai Yar aiki...Yar aiki ....Salamatu ce ta fito da gudu tace dalla ba ke ba ta gasken Yar aiki nake nufi,tsaki ta ja ta wuce dakin Mero da kanta ta ganta tana bacci daga ita sai dan guntun wando da vest,mamaki Jikin Mero ya bata kyau haka kamar ba Yar aiki ba,duka ta dannawa mero a cinya,ta bude Ido da sauri,Ina abincin dan uwarki? Me kika dafa nace? Mero tace nade da Mai,tsaki Ihsan ta ja tace Allah ya taimakeki kinyi girkin,wlh da baki dafa ba da Kinga rashin Mutunci,Mero dariya ta kamata wai Ihsan bata San mene nade da Mai ba,yunwa ce nade da Mai bata sani ba ta zaci wani lafiyyen girki ne.
Tana fita Mero ta sawa kofarta key ta koma baccinta,Kitchen Ihsan ta shiga taga tukunyar ba komai,ta buda flasks duk wayam,dining wayam,Salamatu ta kwalawa kira ta fito tana hammar yunwa,tace Ina abincin da tayi? Salamatu tace ban sani ba Hajiya,tace min ta dafa nade da mai cewar Ihsan,Salamatu ta shiga tafa hannaye tace Hajiya ai yunwa take nufi,ai in kika ji ance nade da Mai to ba komai naci yunwa ce,Ashar Ihsan ta dura ta koma dakin Mero taji kofar gam,key din mota ta dauka ta fita kawai ta wuce eatery lafiyayye taci acan,tana cin Abinci wani matashin mutum talaka,kana ganinsa kasan sai dai rufin asirin Allah amma kyakyawa ne Siriri bai ko kama kafar Haneef a kyau ba.
zama yayi a gefen Ihsan Ganinta babu mayafin kirki bata Masa kama da matar aure ba,sannu yace mata tayi murmushi ta amsa tana cin abincinta,order yayi ta fruits salat kawai sabo da baida kudin cin abincin,kallonsa Ihsan tayi tace ya fruits kawai? Murmushi yayi yace ba komai shi nake so ma,tace a kawo Maka irin wannan rice din akwai dadi,yace bata dame ni ba ne,tace a'a Kaci mana zan sa a kawo sai na biya Maka,yace nace miki bani da kudi Hajjaju? tace nidai nace ka dandana Kaci,okay fine ya furta Yana murna a ransa yau yayi gam da katar,tasa aka kawo Masa yaci ya koshi abinsa.
Yana gamawa ya mike yace thank you Hajiya ya fice da sauri,Bai tsaya ko Ina ba sai Dan gidan da yake rabawa dakinsa me dauke da toilet da dan gado irin na gwauraye.
Murmushi Ihsan ta saki ta mike ta wuce cikin rantsatsiyar motarta.
Spark suna zuwa gidan Rafeeq a can suka samu Khalid Yana zaune a Palo tare da Rafeeq da Ikhram,Rafeeq yace ya Lagos din? Spark ne ya zauna ya hakimce Naila ta zauna a gefensa suka gaisa da Khalid da su Rafeeq,Khalid yace Lagos tana can Ina Barack a daure Ina hutawa Allah yasa ma tare da matata nake,Rafeeq ya furta har yanzu bata sake haihuwa ba? Khalid yace akan me zata haihu yanzu ana zaune lafiya,Soja in kaga Bai nemi mata ba sai kiyayewar Allah,saura kadan rannan na afka,na tuna Dan bariki Misam yanda ya kasa dainawa sai na fasa na ja abata na Maida ta ciki,Ikhram da Naila sai da ya basu kunya amma su ko a jikinsu.
Spark tunda kayi aure banji ance kayi tafiya ka bar kasar ba bare kaki fadawa mutane,da kuwa kawai sai dai aji baka kasar Kuma baza ka fadawa kowa ba,Spark yace da kenan bani da nauyin kowa Gwauro ne ni Amma yanzu ko zan tafi kafata kafar me daki,Rafeeq Yana zaune Yana Shan fruits,Ikhram tazo ta kawo musu kayan Sha da na ci,Spark yace Tantiriya ga fruits Nan,murmushi Naila tayi tace bana son sha ni yau bana son cin komai,Why? ya tambaya tace haka kawai bana so.
Yau me kika ci kwata kwata? Daga fadar haka sai taji haushin Spark wai har taji haushi nan da nan mood dinta ya canja da kyar ta daure sabo da mutane bata ce ya dameta ba,Spark tunda ya kula da haka sai ya kama kansa,bai sake yi mata magana ba,suka ci gaba da hirarsu da su Rafeeq,Nan ma sai haushi anki kulata ta mike tana cewa mu tafi gida,Ikhram tace ke Naila kalau kike kuwa? Naila tace kalau nake tunda baza a kulani ba mene amfanin zuwana,nazo kin wani share ni ke da nazo wajenki,Ikhram tace yau naga ta kaina ni yanzu duk maganar da nake miki kina shareni banji haushi ba sai ke,Naila tace eh ai Kya ce haka mana yanzu bazan sake zuwa gidanki ba,Rafeeq Ido ya zaro yace wlh da kin kyauta min ni dama Kun isheni Allah raka taki gona,Khalid dariya yayi yace madam dai yau ba kalau take ba gaskiya Spark ba haka na Santa ba,Naila ta fice tayi waje,Spark bai ce komai ba bai tashi ba bare ya bita,horn yaji tana ta yi Masa yaki fita kawai suka ji ta fice da motar tayi tafiyarta,Rafeeq yace yau kaga ta kanka Spark,dariya Spark yayi yace rabu da ita taje na koma a taxi,Khalid yace sai na saukeka a gida,ka lallashe ta Dan uwarka maybe wani abin kayi mata,Spark yace ba abinda nayi mata ni.
Naila gidan Misam ta wuce,tana zuwa tayi parking kofa ta kwankwasa,Chika ta bude kofar tace au Ashe kece shugo,Naila ta furta mu gaisa a nan wucewa zanyi fa na biyo bai ma sani ba,Chika tace bai sani ba? baki Naila ta tabe tace ai namiji ba dan goyo bane ke rabu da shi duk ya sire min ma, halin Maza ai sai su,Chika tace Spark din? Naila tace me aka yi aka yi shi dan Allah canja zance,Chika tace to da dalili ko fada kuka yi? Naila tace ko daya ni wlh da zai barni na tafi gida sai nayi wata ban dawo ba ya ishe ni,Chika tace tab shi kuwa Spark lallai ba karamin laifi yayi ba tunda Naila dai tace haka,Naila tace ai mu dai mata sai dai Allah ya saka mana abinda Maza suke mana,babu na gari duk sun kare,na gari sun kare yanzu.
Chika ta rufe baki tace ai sai hakuri Naila dama watarana dole a saba,Naila tace hakurin da nake da bawan Allah Nan ya isa,badan Ina hakuri ba Chika da yanzu zuciyata ta buga,Ki Kara hakuri kinji,ya zanyi na hadu da kaddara,sai anjima ta juya ta tafi abinta,Misam Yana Palo Yana Jin komai.
Mamaki ya kamashi yace ke Honey Anya Naila kalau take kuwa tun kwana uku da suka wuce na je gidan naga tana ta fushi,Abu kadan sai ta fara fushi ta fusata,Chika tace Ina zan sani laifin Spark ne gaskiya duk yanda aka yi,Naila haka kawai baza tayi haka ba da dalili,Spark ba abinda zai mata tab wannan yanda yake sonta kamar ransa me zai iya tsinanawa bare ya bata mata rai,Chika ta furta dan kawai dan uwanka ne shi yasa.
Misam Spark ya kira a waya yace wai me kayiwa Naila ne? Kai a Ina kaga Naila din? Yanzu tazo nan ta tafi tace badan tana hakuri da Kai ba da yanzu zuciyarta ta buga,dariya Spark yayi yace kyaleta fada take nema ni Kuma baza tayi da ni ba,Misam yace dama me zaka iya Kai kam akan Naila ai tubabbe ne.