Sashe 16
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jummai tace to gidan aiki zansa a sake samo miki,Mero tace na samo ma wlh a Kano Inshaallah gidan me kudi ne har gida za a zo a dauke ni,Inna sabo da sakaki ko a jikinta babu ruwanta da waye za a je gidansa burinta a samo mata kudi,Baki ta washe tace Allah ya kaimu Khadija Allah ya miki Albarka,ki bari ki huta ki murmure tukun,Kai Munnir zo kaje ka siyo mata kifi taci taji Dan dadi dadi,Sani uban Khadija Yana kallo Yana Jin haushi amma bazai iya magana ba,da kyar yace Jummai da dai an barta a gida ai Ina ga zai fi ko? Shawara na bayar ba umarni ba a dai duba,na yarje mata ta tafi baza ta zauna a gida ba mene amfanin Hakan,to shike nan Khadija Allah ya tsare ki kula kinji,ki tsare mutuncinki a duk Inda kike tunda kinji dai Hajiya Jummai ta gama magana.
Khadija takaicin Abbun su ya kamata ayi mutum kamar ba mutum ba,a ranta tace anya kuwa Abbu mutum ne? Suna haka wata bazawara ta shugo gidan Zuhuriyya Yar babba ce haka amma ba can ba baka ce kyakyawa Yar Fulani,kawar Jummai ce kut da kut,Abbu Yana kallon Zuhuriyya ta shugo ya mike Tare da gyara sallayarsa a bakin kofa ya tada Sallar Nafila ta dole ya dinga Sallah ba ji ba gani,har sai da Zuhuriyya ta gama abinda take ta tafi sannan ya sallame,Khadija tace Abbu meke nan Hakan? yace hanyar lafiya a bita da shekara Khadija kar ma mace tace ni Sani na kalle ta,ba ruwan Sani da mata,Mero shuru tayi tace ita Aunty Zuhuriyya din ai Abbu ta kirki ce,kana gani kullum shawara take bawa Inna tana nuna mata hanya Ina ruwanta da Kai,Kai da ake so ka zama mijin mace hudu,Abbu yace mace hudu Khadija? Jummai Kuma inyi ya da ita? Itama tana cikin matanka Abbu,a'a Khadija barni da ita din kawai,uhm uhm Abbu yanzu yayin mata biyu ake shine gayu shine cinyewar,yace a'a ba ruwana ,Innar su Khadija tana kitchen bata San me suke ba.
Mero tunda ta dawo mutanen garin suke cewa Yar mace ta dawo, taki aure ta gandame a gida bata da me aurenta,ko ta kansu bata bi" haka tayi sati guda duk kauyen ya isheta tace ga Inda zan ta kallon Yan gayu da wanka ko ta Ina,ko ban samu samu miji hadadde ba ai yafi min akan zaman kauye.
Waya ta samu ta Nemo karama ta siyeta dubu hudu ta sa layi ta kira Haneef,tana shiga amma ba a dagawa, yini tayi tana kira ba a dagawa,da dare ma da ta kwanta haka ta dinga gwadawa amma ba a daga ba.
Bangaren Haneef kuwa tunda gidansa suka nufa direct matarsa Ihsan ya samu a katafaren Palonsa tana zaune ta Sha gayu cikin kana Nan kaya riga da wando tight milk and brown,ta Sha hular gashi me kyau tare da Dora Yar facing cap a kanta,tana latsa wayarta me tsada,ganin mutane Bai Sa ta canja kaya ko ta saka Hijab ba haka tayi zamanta,aji take ja da kyar tace sannunku,barka da fitowa,Su Hajji suka zauna Haneef ko kulata baiyi ba ya haura sama,kin tashi tayi ta bishi sai da Hajji ya gaji yace ke wacce sakarai ce ne? Wacce shashasha ce ke ne? Mijinki guda ya fito daga prison amma ba farin ciki ba komai,Sai lokacin ta mike ta bishi sama,tana zuwa ta samu ya shiga wanka,zama tayi a gefen bed dinsa hadadden gaske tana ci gaba da chat dinta,tayi mugun Dadewa kafin ya fito daga wanka,Yana fitowa ya ganta me ya kawo ki nan? Ihsan tace Hajji yace nazo kasan in ba cewa aka yi nazo ba bazan zo ba,ka sani ba wai niyyar kaina bace abinci yana dining Kuma me dafa maka abinci ce tayi ba ni ba" tana fadar haka ta mike ta fice.
Ita Ihsan tunda auren zumunci aka musu ba wai sonta yake ba itace ta damu da shi har aka yi bikin maimakon ta kwantar da Kai tayi biyayya baza tayi ba,tunaninta kullum shi Haneef sai ya gaji ya sakko da kansa ya kawo kansa da kansa,gadara take tana da kyau da komai da namiji zai so a jikinta sabo da haka ba sai tayi biyayya ba,itace mace itace take da aji,sai dai namiji yayi fadanci a wajenta ba ita ba,sannan tana ganin tana da babban aiki,babban matsayi ne da ita a company tana samun kudi sosai ba ruwanta da kudin namiji bata ga dalilin da sai tayi biyayya ba,shi yasa take abinda taga dama,yanzu ma company ne ya dawo da ita branch din Kano shi yasa aka ganta ta dawo gidan Haneef a nan amma ita a Adamawa take can gidan Haneef na can,sanda Wuta ta Kone Khairat ba karamar murna tayi ba a haka wai duk bata son kishiya Kuma,bata aikin fari bare na baki sai dai aikinta in tana gida Kuma chat ta fesa wanka ta zauna tayi Kallo,Bata fiye fada ba Kuma ita sabo da ajinta zai wahala kayi hayaniya da ita,tana da aji ita dole me aji ce,sai dai ta guma Maka takaici ta wuce.
Tunda Haneef ya aure ta sun Kai Shekara kenan amma sau uku zuwa hudu ta taba kwana da shi,har wani Abu ya shiga tsakaninsu,tunda taga in Bata je ba bazai neme ta ba,sai idan taje wannan zai nemeta normal sai ta daina zuwa tace sai ya kawo kansa da kansa sabo da ta isa itace me aji ba shi ba.
Shi Kuma Haneef Yana ganin abinda take yi haushinta ma yake Kara ji sabo da duk wani Abu na macen aure bata yinsa shi yasa baya kulata,ya Kai kararta sau biyu duk dangi ita Ihsan suke goyawa baya ai shi zai lallabata sabo da suna ganin auren zumunci ne ko ya Kai karar ba a daukan mataki shi yasa ya gaji ya watsar da zancen ya watsar da ita kowa yake Uzurinsa.
Sai da ya shirya ya canja sutura me kyau cikin jallabiya fara me tsada dai dai shi sannan ya fito ya samu su Hajji su har sun ci abinci tafiya ma zasu yi,ya raka su suka shiga mota yace a fadawa Ummi ya bata zo ba Danta ya dawo,Hajji yayi murmushi yace zata zo ne a satin nan ko na sama tace,yace shike nan zan kirata a waya,in Kun isa lafiya ku kirani,yace to driver ya kaisu airport suka wuce shi Kuma Haneef ya dawo ciki,dining ya duba gaja gaja an lalata me aikin ya kwalawa kira Salamatu" fitowa tayi da sauri yace ki gyara dining sannan zan kawo wata me tayaki aiki,bana son Yan aiki barkatai zaki dinga gyara gidan nan ita zata dinga girki,Salamatu tace to Oga Allah ya kaimu, babbar mace ce ita Salamatu,yace me gadi fa ana bashi abinci? tace kullum sai ya koshi Oga,yace Good job yana murmushi yace zuba min ta zuba Masa ya dauki plate dinsa ya koma Palo Yana kallo yace Kai sai naga plasma din ta Kara min girma ko dan a can babu ne"
ya Kalli gidansa yace Allah na gode Maka Ashe dai ba karamin hadadden gida nayi ba,sai yanzu na gano haka da naje prison,ga ac ta a can kuwa Ina wata Ac ta kirki,uhmmm ji Parlo komai me tsada ga kyau ahhh nasha wahala,shi yasa nake ganina kamar a Aljanna nake yanzu.
Yau da wuri ma zan kwanta sabo da na hau katon bed Dina naji dadi in more rayuwa ta,da ace waccen Yar iskar mutuniyar arziki ce ai da sai ta zo ta Sha madarar Nido Inji Scola,tunda tafi so a bar mata abinta haka kullum a lullube taje da abinta ta Shekara tana rufewa,Dan ta ni in taje wanka ma kar ta bude,ita kuwa Ihsan tana garden tana hutawarta Bata San me yake cewa ba.
Sai magriba yaje masallaci ya dawo Yana Sallar Isha ya kwanta abinsa,tunda ya dawo sai da ya kwashe sati guda Yana hutawa sannan ya koma aiki,Yana ganin kiran Khadija kullum amma bai San number din ba,yayi busy da yawa sai da ya cika 10days da dawowa sannan ya daga kiran Khadija,Yana dagawa yaji muryarta bai San ita ce ba,sallama tayi kana magana da Khadija ta gidan yari,Yana Jin Muryar ya gane dariya yayi yace wacce Khadija fa? Khadija me fasa gini mana dalla wacce kake ba Madara ta Yar kafa wai meye haka Dan Allah ka gane ni ka dinga wahalar da shari'a ,murmushi ya saki yace ohh Yar aikin da zan dauka?Mero tace duk Inda talaka yake sai me kudi ya nuna Masa rashin Kara kiri kiri ba komai itace ei itace Yar aikin,kin shirya ne? Mero tace tun yaushe Kuma na shirya na ma fada a gida sun yarda.
Har kin gama Shan kokon ya ishe ki da awarar taku,Mero tace na Sha mana Kuma na fika lafiya ba,yace to yaushe kika shirya? Nifa a shirye nake ko yanzu,yace to gobe da yamma ki shirya za a zo a dauke ki, Allah ya kaimu,ki bar wayarki a kunne kusa dake sabo da kwatacen gidanku,Mero tace sabo da rashin tabbas din karfen nasara bari na tura ma text ko da network yayi tsiyar kaga ai an San Inda nake,yace Alright Allah ya kaimu,badan yayi dariya ba sai Mero taji kamar bai San wace ce ba yanda yayi magana.