Sashe 30
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Uban waye yace ka taba mata jiki? Iro yace Salamatu ce tace na taimaka Kuma ma Allah ya so sau hudu na gwada daukanta Ina ajiyewa Ina dauka nauyinta ya baci sai kace nauyin gawa,Haneef ya Masa tsawa yace fita ka bar nan,Iro ya fice a tamanin Yana cewa ni Kam naji dadi dama nauyi ne da ita.
Haneef yace Me ya faru da ita Yana tattaba Jikin Khadija,Salamatu tace ranka ya dade yanzu kace ba kyau ka Kori Iro sabo da ya dauke ta Kai Kuma kana ta tattaba jikinta,Haneef yace ni na daban ne,ni da Iro daya ne? tace a'a yace to bana son sa Ido zan iya sallamar mutum daga aiki,Salamatu tayi shuru tace dama matarka ce ta turota daga bene,Haneef daukan Khadija yayi kamar tsinke ya fice da ita ya sata a mota,Iro hannu ya dora a ka yace Oga kamar dangin samudawa ji yanda ya dakko ta kamar buhun auduka ba wani wahala.
Asibiti Haneef ya Kai Mero Allah ya kiyaye Bata karye ba amma wani wajen kasusuwanta sun tsage wani Kuma kashin ya goce da sauransu a ranar ya biya komai aka gyara Mero Inda za ayi dressing aka yi mata komai,ta Sha wahala wajen gyaran,Likita yace sai tayi kwana uku sannan a sallameta,Mero tana kwance a Saman bed Kafafunta da hannaye duk ya Sha gyara,Haneef ya kalleta ya furta sannu tace yawwa sai hawaye sharrr,yace to mene na kukan gani fa ni zanyi jinyar ki,Yanzu ma gida zanje tunda ga Salamatu in nayi wanka Sai na dawo kinji,Kai ta daga Masa,Salamatu tace Ina Nan zan kwana ma a wajenta yanlabai,Mero tace a'a ni ko babata ce tayi zamanta gaskiya ga abokina ya fiye min,Salamatu tace uhm ai shi yasa matarsa ta jefa ki a wannan halin.
Washe gari Arham za a daurawa Aure kowa a dingi sai shiri ake yi duk da ba yanzu za ayi bikin ba,Ango kuwa Papa ne ya kira shi 'Yan uwansu na kauye Dattijai sunzo sun cika palon Papa, dukkan mazan gidan yaran Papa suna nan su Spark kaf an kira su a gaisa da Yan uwa na kauye,Arham ne kawai baya ciki sai yanzu ya shugo palon,Papa yace yawwa ga Angon ma shine Ango ai na gaji da halinsa, tashen balaga yake ji da ita Yana neman ya lalata yaran jama'a shi yasa nace a daura Masa auren kawai a huta,yaran jama'a yake bi kamar fan akuya gashi Nan kun ganshi na gaji da halinsa,Dattijan kauye suka saki salati da sallalami, Kai dai baka ji dadin halinka ba,wani tsohon yace da ganinsa anga tsagera wannan dama bazai kyale mata ba,Spark yayi dariya da su Rafeeq,Ai dama idan da hali in kaga yara na irin wannan sun taso da lalata haka kawai ayi musu aure shine maganinsu,na masara ma ya ishe su,da siyen Maggi aka barsu ma shike nan kawai anyi maganinsu,sannan abinda suke hange gashi Nan a basu macen,kayi daidai ka kyauta General.
Wani tsohon Shima yace ai duk yaran General haka suke Yan banza gasu nan a zaune kamar na kirki ba abinda baza su fada ba a gaban mutum wannan dan iskan ana cewa Da na biyu Shima babba ne to wallahi babban banza ne Spark kake ko wa,Rafeeq Yana dariya yace ni yanzu Allah ya shiryeni da matata nake yi tunda na samu kawar yi,Misam Yana jinsu baiyi magana ba waya ya daga Yana tambayar Chika ya dana yau me yaci kuwa?suna jinsa tsofaffin suka ce kunji ko sai kace yaron yazo duniya Allah ya shirya.
sai da ya gama wayar sannan Papa yace a shirya lokaci ya kusa,Arham yace to tsohon kaya zan saka? tunda yi min auren za ayi ai kayan da zan sa ma kamata yayi a bani a dinke,yanzu ni da tsohon kaya zanje,gaskiya Indai tsohon kaya zan saka bazan je ba wlh,Papa yace akwai kayanku Kai da su Shaheed an dinko muku ai nasan hali shi yasa an gama komai suna bedroom dina ku dauka kuje ku shirya.
Ango farar shadda aka Dinka Masa harda babbar riga ta zamani tayi kyau,su Shaheed kuwa wata kala ce me kyau daban,tafiya suka yi kowa yana shiri a gidan har mata sunyi wanka sun saka sutura me kyau,Yan uwan Mima kaf sunzo suna gidan,Naila da su Chika duk sun zo yanzu,na nesa ne basu zo ba sabo da bikin ba yanzu bane,Amarya Basma tana kwance tana ta baccin rana abinta ta manta ma ance yau za a daura aurenta.
Katafaren masallacin ya cika abokan Arham sunzo da yawa duk da ba shiri abin,suna ciki gaba bayan an idar da Sallar Juma'a aka fara yanke sadaki,dangin Amarya da suka zo wani Dattijo da kanin baban Basma suka yanke dubu dari biyu,Arham Wanda kamar a sace shi sabo da kyau,bai taba kyau irin na yau ba ya Kalli Papa yace yanzu wannan har kudinta ya Kai haka,me ta sani sai tona asirin tsiya ita za a biya kudi haka,ko girkin kirki ta iya ne? daga tuwo,danwake,Dambu,wake da shinkafa,dafaduka nasan karshen kwarewar girkinta kenan,Papa Yana jinsa kamar bai ji ba yace kawo kudi karka bata mana lokaci ai kana da su,Arham yace to wa zanwa transfer? dangin Basma kaf babu me accnt,a accnt din Liman aka tura, nan take Liman yasa yaronsa ya ciro kudi a POS an cire dubu daya charges,Arham ya zaro dubu a aljihu yace ku ungo kar a bini bashi ace saura dubu daya, gashi Allah ya hana babu,suka karba aka cika kudi dai dai chass sannan Liman ya fara Khuduba,Arham yace Innillahi wa innailayhirrajun za a zargeni yanzu,Papa Yana jinsa abinda yake fada sabo da suna kusa gaf ba me ji sai Papa,Arham yana ji aka tambayi Ango Yana da wakili ko shi zai karbi aurensa,yace Ango ni zan karbi Abina tunda ba taimaka min da sadaki ba kuwa babu me karbin min aure yana magana Yana hararar Spark wai nai ce ya bari ya biya Masa Sadakin ba,Spark yayi murmushi kawai Arham ya karbi aurensa da kansa aka daura aure ana ta dariya Wanda suke kusa sunji me yace shi zai karbi aurensa tunda ba a taimaka Masa ba,ana daurawa Arham yace shike nan har an gama? aka ce ae an gama Kuma,yace Ina Tausayin Amarya Kun daura mata alakakai,bacci ma wlh sai an kwantar dani,Papa yace ka gaji ma ka kwanta da kanka ku tashi mu tafi.
Arham ya fito ana ta gaisawa da shi ana Masa fatan Alkhairi,ana cewa to Ango ayi ta hakuri,Arham yace ba nine da hakuri ba Amarya ce" ita hakuri ya kama,Papa ya chaka wa Basma dansa,ai mu indai ka auri Dan gidanmu to an Chaka maka,Spark yace wlh karya kake mu matanmu ba a Chaka musu ba ka tambaye su kaji basu da kamar mu.
Naila ce tace wai ni Ina Amarya ne? Mima tace tana ta bacci an tashe ta taki tashi, ni wannan ango da Amarya na rasa irinsu wlh,Naila ta nufi dakin Basma ta sameta ta wargaje kafa daya can daya nan tana bacci,Naila tace ke Basma tashi tana girgizata taki tashi,ruwa ta dakko ta watsa mata a fuska da sauri ta tashi tana Murza idanuwa,Naila tace an daura aurenki kina wani bacci sabo da shirmenki,ki tashi kiyi wanka,an daura Allah?Basma ta tamanya, Ke baki ji a jikinki ba? Naila ta ce, Basma tace naji me? ba abinda naji tab,ke ki tsaya ki nutsu aure shi daban ne fa ba irin wannan rayuwar ake yi ba,ki koyi sirri ba a fadar sirrin miji,ko me ya taba miki ko yace miki ba a fada shuru ake yi,duk yanda kuke da mutum ba a fadar sirrin miji,yanzu ya zama mijinki ki girmama shi ki Masa biyayya,ki kula da abinki,kiyi tattalinsa,karki barshi shi kadai,Yar hira da kalamai masu dadi,iya magana,Kinga kwalliya tsafta,in ya dawo ki rungume abinki ki chafe dan mijinki,kissa da kisisina,iya shagwaba, Basma tana Jin Naila tace kema baki wuce a fada miki haka ba,baki wuce ayi miki irin wannan fadan ba kina yarinyarki da nawa kika fini,Dan kin rigani aure,wa yasan me kike shukawa Spark din naki,yanzu da zai warware mana abinda kike Masa kare bazai ci ba,amma dai gaskiya kika fada min Kuma zanyi abinda kika ce,Naila dariya tayi Basma akwai son girma ita bata yarda ba baza a fita shekaru ba.
Wato baki yarda da abinda nake fada miki ba ko? Basma tace na yarda Allah Aunty zanyi Kuma duk abinda kika ce Kuma zaki gani,Naila tace yawwa ko kefa,tace Kuma ai nace koma ba a daura aure ba ko me yayi min bazan fada ba tunda naga babansu masifaffe ne,Kai muna da siriki a wajen Nan,shi kadai watarana muzurai yake yanzu Kuma Mima a haka suka soyayya ei Aunty? Naila tace Ina zan sani wlh ki rufa mana asiri sirikan mu ne,Basma tace bamu yi dace ba,ni da nake so na samu lusarin siriki Wanda ana min in na kawo Kara zaice Basma kece da gaskiya Allah ya miki Albarka,sai na hadu da Soja,Naila tace to nidai ba ruwana wlh,Basma tace ke wato baza ki gulmar su ba? Ai Spark ya mallake ki,Kai Naila zaki ci gado in Spark ya mutu Allah kawota da wuri mutuwa tono dadi kekam,ni kuwa nawa Allah sarki da zai mutu ko tumuni bazan samu ba haka zan koma gidan iyayena naci ga da agolanci na babu ko bukka.