Sashe 65
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuwa yamma Naila ta Sha Bride material me shegen kyau da tsada,gown dinta ta Sha dinki sosai matuka tana wajen make up su Chika ma sun zuba anko duk sunje make up, Spark zuwa yayi ya dauki Naila da kansa driver ya kawo shi ya Sha shadda silver kalar takalmi da Jakar Naila,ta zuba kyau kowa ya zaci Amarya da Ango ne suke aure abin nasu yayi,Mota suka shiga sai Event center,mata da Maza har Yan school din su Naila,suna zuwa can Basma ta fito daga motar Arham jariri Yana kuka ta kawowa Naila mota,a motar Spark yace da driver Dan Allah Dan bamu waje,Driver ya fice sannan Naila ta bashi nono ya Sha,Tana gama bashi nono aka musu pics sannan suka shiga,mutane an hallara su Mima,yaro ya Sha kaya masu kyau white and silver,duk kidan Dake tashi baccinsa Jaririn yayi,kowa yaci abinda yake so anyi rawa an zubar da Naira sosai,su Chika an cashe da Beauty da Ikhy...
Kamal da Amaryarsa ma sunje,ana cikin riti Mero da Haneef suka dira a Abuja amma suna hotel masauki,Mero harda cewa an kawo motar taka kuwa? Haneef yace an kawo Madam driver Yana nan zai kaimu Inda kike so,tace to Allah ya kaimu.
Washe gari da Yamma suka shirya Mero an goge ta Sha kaya masu tsada Leshi kana gani kasan kayan ba karya a ciki dark green an Golden ne.
Mota suka shiga driver ya kaisu har gidan Mima,Allah yasa duk sunzo Sunan Naila basu tafi ba kowa da kowa Yana gidan Mima,da yamma su Misam,Rafeeq,Arham da matayensu duk suna gidan,suna compound sai kace yau ake Sunan,Badia tazo da Anam,motar Haneef me azabar tsada ce ta shugo gidan sun zaci ma Spark ne,Sai da Mero ta fara fitowa tun daga takalminta da komai na jikinta abin a kalla ne,ba Wanda ya ganeta har takaraso gabansu tayi Sallama suka amsa,tace Mima sai lokacin Maman Rafeeq tace wace haka kamar Mero Yar aikin Maman Spark,Mero tace nice tana murmushi,Mima tace Mero kece haka ai badan kinyi magana ba babu me gane ki,suka hau mamaki,kowa sai da ya kalle ta,tace dama da mijina muke munzo Abuja ne nace bari muzo mu gaisa,Mima tace to ya fito mana ku shugo ciki sannunku da zuwa,oh Ashe kinyi aure ba sanarwa,Mero tace abin ne ba shiri shi yasa.
Arham harda gulma kasa kasa ta furta Mero Yar aikin Mama mutuniyar Spark,Rafeeq yace ni naga dare Daya Allah kan yi bature yau,shi yasa aka ce ko ya mutum yake baka San me Allah zaiyi ba karka wulakanta shi amma su Mama basa ji,Arham yace ei kamar Mamanka wulakantani da take akan Ina soyayya Baki San me Allah yayi ba wlh Kinga dai Mero,dariya Maman Rafeeq tayi tace Dan banza ai Kai sai gyaran Allah.
Haneef ne ya fito ya Sha gezna Yar gasken milk sai shining yake,Sai sa Ido suke yi yaran Mima,mazan ya mikawa Hannu suka gaisa matan Kuma suka gaida shi suka shiga ciki,Anam tace guy din ya hadu ita Mero Dan ubanta Ina ta samo wannan haka ikon Allah kenan daga yau na daina wulakanta Yan aikina wlh naga ishara na tuba,Arham yace kuci gaba duniya ce ai zata bi da ku,ku akan Kuna yaran General sai iskanci,ai da kunce zaku wulakanta min Basma sawa zanyi ta zazzage ku,ki duba dai Maman Spark yau suna Ina,ga Wahida sarkin bakin jini anyi bikinta tana dakin mijinta uwar tana prison,yanzu Kalli Mero dai wannan Mero da ake gani a banza ana mata kallon mahaukaciya ce ma.
Basu dade ba suka fito suka musu sallama suka bar su da Cece kuce,gidan Spark suka je,Naila ta gama gyara kayan gift da komai Baki duk sun tafi har su Zarah sun tafi sabo da makaranta,Naman Sunan ma tace sai dai gobe a Kai musu,masu aiki suna ta soya nama a can compound sabo da sa ne da raguna biyu kamar me layya,Naila tana Palo ita da Goggo Sai taji sallama ta amsa,Mero ce ta shugo,Naila ta ganeta ita" tace Mero kece? Mero tayi murmushi ta shugo tace nice ta durkusa ta gaida Goggo,ta zauna suka gaisa da Naila tace ke Yar gari Ashe haihuwa kika yi? Naila tayi dariya tace ae jiya aka yi suna Mima ce ta fada min da naje,Allah ka sa Nima na sauka lafiya haka,Allah ya raya,Naila tace kema naga kamar kina da cikin Ashe da gaske ne,wai yaushe kika yi auren ba sanarwa? Mero tace Abu ne yazo cikin gaggawa,wlh ujula ujula aka yi auren nan,tare muke da shi ma Yana mota,Naila tace kice ya shugo mana,Mero ta fita ta shugo da Haneef,Naila taga miji rangadeden gaske,bayan sun gaisa tace bari na kira muku shi Yana nan,sama ta haura Spark Yana aiki a system tace kazo munyi Baki Mero da Angonta sun zo,Mero tab aure tayi? Naila tace har da ciki,yace ikon Allah,Naila tace zo kaga Mero ta goge me hali ta aura,Spark yace na tayata murna,ya mike suka fito,ahhhh bai zaici gogewar Mero ta Kai haka ba,mijin ma ya sanshi ashe ya Sha ganinsa a gidan yari in yaje ziyara,suka gaisa Sosai ya zauna suna ta hira,Naila ta kawo musu Abinci da lemuka sannan ta kawo musu Naman da ake soyawa a plate,suka ci kuwa sun Dade kafin su tafi, Haneef 50k ya bawa Naila suka tafi har mota Naila da Spark suka raka su,Naila tace sai mun zo muku muma inshaallah,Mero tace Allah ya kawo ku.
Wani satin Mero da Haneef sai prison wajen Maman Spark,tayi girki lafiyayye suka Kai,bayan Mama ta fito da Yar uwarta da kyar suka gane Mero,Mama ta nuna ta da yatsa tace me...me...Mero tace nice Mero da kika ce ban dace da suna Khadija ba sai dai Mero,to ga Mero Allah ya azurtata tayi sama ke Kuma gaki a wani hali,ni bazan miki abinda kika yi min ba,albarkacin naci na Sha a gidanki baki taba hanani abinci ba bazan manta da wannan Alkhairin ba,ko nama kika ci Ina ci,tace gashi ta mika mata Daya abinci da ta kawo mata,Maman Wahida ma suka gaisa suna ta mamakin ikon Allah,Azima ce tazo suka rungume da Mero sannan Mero ta bata nata abincin,Haneef harda kudi ya basu duka,sun Dan dauki lokaci sannan suka tafi,Mero tana cewa Azima ki gaida su Goje su Scola kice bazan manta da su ba,Azima tayi dariya tace zasu ji.
Naila tana yin Arba'in Spark ya dauke ta da Baby da Arham da Basma suka bar kasar suka tafi Germany,Arham sai murna yake zasu Shana,Rafeeq yaji haushi an bar Masa aikin Office a hannunsa,Misam kuwa ya biyawa Mahaifiyar Chika da Mahaifinta Makkah,ya canja musu gida me kyau.
Spark amarcinsa yake Sha kawai sai da suka kwashe watanni kamar baza su dawo ba suna zaga kasashe,suna dawowa Kuma Jauro ya biyawa Yar Inna da Abba Dolo Umrah da shi kansa Jauron da iyalansa kaf,suka tafi wai za ayi addua har su Haidar da matayen su.
Lokacin aikin hajji ya kusa Iman ta haifo Yarta mace kyakyawa,ba a Dade ba Hidaya ta haifi Danta Namiji itama,an Sha suna anyi shagali,Yar gidan Iman Sunan Maman Annoor aka sa mata tana kiranta da Nihad,ita Kuma Hidaya suna kawai danta ya ci Na'eem.
Naila da Spark,Rafeeq da Ikhy,Basma suka tafi sauke farali gaba daya Spark ne ya biya musu,Chika alkawari yayi zai biya mata dama,can suka hadu da su Abba Dolo,Abba Dolo da Yar Inna kamar Larabawa suna makale da juna.
Bayan Sallah suka dawo Mero ta Haifo Yan biyu mace da namiji kyawawan gaske kamar yaran Larabawa,kowa sai murna ake taya su,Spark ma yaje da Naila da Sha Tara ta arziki yara sunansu Nawwar da Nawwara ,su Mima sun je,Mufee da matar Kamal ma da yaron cikinsu.
Sai da Basma ta Shekara biyu sannan ta samu ciki,Arham ana ta murna da kamar baza ta haihu ba itama, lokacin su Chika ma yaransu sun fara tafiya dagwai dagwai,na Naila Yana Rarrafe ko Ina,ga matar Kamal ta haihu itama
Rayuwa na ja kowanne suna zamansu lafiya sai sabani Wanda ya zama dole da sauran kaddarorin rayuwa domin bawa baya zama babu kaddara da jarabawar rayuwa,cikin Basma ya tsufa itama gida ya dauke ta suka koma gaban Mima,satinta biyu a gidan da tsakar rana ta fara nakuda Arham Yana wajen aiki,Mima Bata fada Masa har suka Kai Basma asibiti ta haifo yarta mace kyakyawa,duk ba a fadawa mutane ba sai yamma likis aka sallamo su,tazo ma tayi wanka aka yiwa jaririya wanka suka shirya tsaf ta gwada bashi nono,Arham sai wajen dare yazo gidan ganin matarsa yaya take,Mima ya gani yace Basma fa ya jikin nata? Mima tace tana daki shiga mana ka ganta,Yana shiga ya ganta da jariri a hannu tana cin Abinci,Arham yace wai haihuwa kika yi? tana dariya tace gashi ka gani kuma,ya dafe kirji yace wayyo dadi, Alhmdllh Alhmdllh,Mima tana jinsa Yana hauka iri iri,na zama Daddy wannan yarinyar zata ga muzurai ince ke shiga gida,dariya Basma tayi tace ni Kuma nace wato baza ki shirya ki tafi school din ba sai kin makara wannan yarinya Allah ya shirye ki bari na fadawa Daddy,sai na kwala ma kira Daddy Daddy,Arham harda kausasa Murya na'am lafiya,ka zo taki ta shiryawa ta tafi school,sai na fito na mata wani kallo tuni Zata kama gabanta,dariya suka yi sannan ya zauna ya dauke ta yace a'a Kai nayi 'ya kuma
ni,Anya zan iya bacci ma,Basma tana ta dariya,Mima ta sanarwa dangi da kowa.
Su Arham sunga jama'a kullum cika akeyi yayye da sauran dangi da abokan arziki,ranar suna yarinya taci Sunan Mima suna kiranta da little Mima,Mima an Maida sunanta sai farin ciki take yi sosai yarinya tana gani gata,Papa yace matarsa guda ai sai abinda take so a duniya.