← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 68

Sashe 59

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mima suna Murna suka ce Alhmdllh da lafiya ma Inshaallah,Sai da aka yiwa Naila duk abinda ya dace da Allurai da komai suka cire mata Jinin mararta,ga Allura taji karfi a jikinta Goggo ta sa tayi wanka a toilet din,Dake asibitin na manya ne kamar kana gidanka ko Ina kamshi,haka tayi wanka da sabulu me kamshi tace kayan da suka baci a zubar,Goggo tace baki isa ba tana fitowa aka canja mata daki bayan Goggo ta wanke kayan da suka Baci,babu ma abinda ta bata sai iya rigar jikinta,Naila ta shirya kanta tace da kyar nake Shirin Nan iska daukana take sai naji bani da nauyi,Goggo tace ai kin samu me sauki wlh kin haihu lafiya wata ai bata Isa ta iya tashi yanzu ba,Naila tace Chika sai da ta kwana ma sannan ta iya yin wanka.
Jariri Yana nade a cikin showel fari aka sa masa kayansa farare tas da shi Yana ta baccinsa.
Spark ya matsu yaga Nailansa amma Goggo ta hana shiga sai sun shirya.

Naila tunda ta canja kaya ta zura Abaya da wondonta dogo bayan ta shirya kanta ta kwanta bacci na son yin gaba da ita ga wahalar haihuwa,daga haihuwa ai baka isa kaji dai dai ba.
Goggo ce tace ta fito daga wani dakin ta kofar baya ashe aka canja musu room,ta tako da Dan Nisa tace muna Nan fa kuzo kuga jariri da Me jego an haihu lafiya anyi arziki,Spark ne a gaba ya wuce Goggo tace har tayi wanka fa yanzu abinci nake so taci kafin ta huta,Spark yace yanzu za a kawo ai,suna shiga ciki suka hada Ido da Naila Dake kwance,suka sakarwa juna murmushi harda wani signa da Ido wai su sunyi Da,Mima ta karbi jariri tana cewa Masha Allah lallai an samu Karuwa,Naila tace Allah ya nufa,Goggo ta make ta tace ku ko kunyar Dan fari bakya ji a gaban sirika,Maman Rafeeq tace Allah ya raya bisa sunna,Naila tace Goggo nace Ameen?nidai zance Ameen ai addua ce,dariya aka yi Spark yace Allahumma Ameen,Spark ya Kalli Naila duk har ta canja da Gani ta Sha wahala,hannu ya mika mata Yana zaune a gefen bed din ta saka nata ciki,yace sannu kin Sha wahala,Finally dai an haihu na huta da cizo da kuka da masifa,Naila tayi dariya tace kunya ma nake ji yanzu in na tuna,yanzu me kike so? Cikinta ta nuna Masa tace yunwa kamar zanyi me a bani abinci Dan Allah,Arham ne ya shugo tare da Basma da flask wurin kala hudu na abinci daban daban,ga take away Kuma da Spark yace ya taho da shi na fruits da nama me ruwa ruwa, yogurt da sauransu,shayi aka hada mata lafiyayye ta mike zaune Spark Yana Bata a Baki sauran suna ta hirar su,Maman Rafeeq ta Kalli Arham taga ya juya can wai gyara mata adon rigarta yake bayan adon a Saman Boobs dinta suke,rankwashi ta zuba Masa tace Kai dai Allah wadaran halinka,nifa Mima gaba daya yaron nan naki ya kwance min Dan iska fitsararre,Arham yayi dariya yace idan kishi kike yi kawo na gyara miki kema gashi Nan an miki tuta a wajen ai,yaron ya karba Yana Masa addua,Maman Rafeeq tace Allah yasa adduarka tayi Masa aiki badalallen yaro,Mima tayi dariya tace kin da damar min yaro Dan kinje gidansa ya Koro ki sai ki dame shi,Arham yace gani tayi ana soyayyar da ita a zamaninsu babu irinta shine take kishi,Maman Rafeeq tace kaji min yaro ni da mijina yake Dan Sudan mene bai sani ba,har ka fadawa Balarabe kauna.

Naila tana shanye shayi da nama kadan ta rage Naman,ta koma kan faten doya da wake taci taci ta koshi ta Sha fruits da ruwa ta Dan huta sannan ta kwanta sai bacci,tun dare sai washe gari da rana ma aka sallame su,Mima a motarta ta wuce da Naila da Goggon gidanta direct,Naila tasan Spark Bai sani ba ta dai yi shuru,sai da yaje gida shi yaga ba nan aka kawota ba,ya nufi gidan Mima Yana cewa ai dalilin dakko Goggo kenan tazo ta zauna da Naila.

Mima tace to ai na sani Malam ka bari dai ta huta ,yace shi wlh a'a,Goggo tace ka bari tayi wanka sosai ta gasa jikinta ayiwa Jaririn sai mu tafi,yace yawwa,Spark tunda ya dauki Jaririn ya Masa addua bai Kuma daukansa ba Yana hannun Yan uwa har so yake a ajiye shi ya dauki abinsa amma daga hannun wannan sai ya fada hannun wannan.
Nurse me jiran Naila ta haihu ta rama Marinta lokacin tashinta yayi amma jira take taki tafiya sai Naila ta haihu,tana can ta kwanta tayi bacci sai da me asibitin yazo ya dinga fada Dan me Bata tafi ba ya Kore ta gida,tace wlh Allah ya hada mu watarana a hanya ai na gane ta.
Naila wanka tayi Goggo ce da kanta tayi mata gashi,Naila har hawaye tayi ta Sha wahala a hannun Goggo da gashin towel,an zuba gishiri a ruwan sabo da kashe wasu kwayoyin cutar,Sai da ta gama Naila tasa shampoo ta wanke gashinta sosai sai kamshi ke tashi,tayi wanka da sabulu ta fito,Mima tayiwa Jariri wanka tas an canja Masa kaya,kayan Naila na asibiti duk da Goggo ta wanke Spark gaba daya ya kwashe ya zuba a washing machine ya sake wanke su,ya zuba na jariri ma ya wanke tas suna kamshi ya tattara a cikin bahon jariri ko kunya,ya saka a mota yazo duk ya kwashe abinda suka zo da shi kaf ya Kai motarsa,Naila ta saka kaya tana daure gashinta da ribbon gashinta yanzu yayi mugun tsayi Dake Jinin gashi ce har ya dawo bayan uwar daadaa da yasha a gidan yari.

Mima wani abincin ta shirya musu suka tafi da shi a mota tace ala raka taki gona ta fadawa Spark yayi dariya yace Ameen,zasu shiga mota Papa yazo ya dawo yazo ya dauki jariri ya Masa addua ya yiwa Naila murna,Spark yace sai fa kazo har gida Papa ban karbi wannan ba,Misam da Rafeeq har gida kaje ganin jariri Nima sai kazo,Papa yayi dariya yace zanzo Inshaallah,na Arham dai in za a haihu har asibiti zanje,dariya suka yi har Arham Dake ya fito shi da Basma zasu tafi,shi yasa Papa yayi zancen ma,Arham yace Allah ya kaimu,ai Bata da ciki wata nawa Amarcina nake Sha kawai ai haka yafi,Papa yace Allah ya bada na gari,yace Ameen yaushe zaka zo muyi hira ne?Papa yace sabo da yana son yayi hira da Spark da Arham,in suka zo ko banza yayi dariya,Rafeeq shi in yaga dama ma yaji yake ya daina zuwa,Misam ma basu Shaku ba,in yazo ma basa hira, Arham yayi dariya yace yau ma dan na gaji ne amma da tuni na zance ka da magana sai na dawo zanzo weekend ai Papa Soja sarkin fara'a,irin wai yasan baya fara'a sosai shine yace sarkin fara'a,Basma tace Papa mun tafi yanzu munyi hankali,Yace to Basma Haka ake so ayi ta hankali,tace to suka tafi, Papa yace a ransa Ina kuka ga wani hankali ai sai dai gaba kuyi hankali tare.

Naila tun a mota ta kira Yan uwa ta fada musu,Mohsin ta fara fadawa,ta fadawa Umma ,ta kira wayar Abba sai da yaji ance ta haihu ya daga wayar Yana murna,tace Abba na haihu,yace Inyee su Naila an girma za a fara koya tarbiyya,Allah ya raya bisa sunna tace Ameen,yace yawwa karki biyewa su Goggo da kauyenci baza a amsa addua ba, kowa yace Allah ya raya kice Ameen, kanki tsaye ki amsa Ameen idan ance kinyi fitsara kice ni na saki kakan yaro ne,Naila tace Nima dai shine na Gani,yace yawwa karki yarda da kauyencin su Goggo,Sannan karki matsawa mijinki da maganar kashe kudi akan kin haihu nasan ku mata in kuka samu waje sai Kun Kai mutum bango ki bari duk abinda ya siya kiyi godiya,Naila tace ai dama Abba ai ba kullum ake kwana a gado ba,Abba da sauri yace a'a Banda ni" Naila kullum a gado nake kwana tun Ina jariri akan gado karami na babata ake dorani" babata Kuma da Mijinta babana kenan suna kan babban gado ni Ina karamin gado,har na girma aka mayar min da gadona dakina gashi har na auri Yar Inna yau shekaru kusan arba'in ban taba fashin kwana akan gado ba,Naila tace gaskiya ne tana murmushi,yace sai bayan suna zamu zo da Yar Inna,su Hidaya dai da su Zarah zasu zo kafin suna,tace to Allah ya kaimu.

Suna komawa gida Naila tace yunwa nake ji da bacci,Spark wanka ya shiga yayi wanka sosai ya fito tare da saka sabuwar jallabiyarsa da Mohsin ya kawo Masa,Naila a dakinta Goggo ta sake yi mata wankan yamma,bata shirya ba sai da taci abinci dare yayi sannan kaya ta sake canjawa ta saka rigar baccinta doguwa me kyau me gajeren hannu Orange color, Goggo tace sai an daure ciki,Naila tasa abin daure ciki na Yan gayu Wanda a kasar waje ma aka siyo mata kala nawa da kyar ake matse ciki da shi na rage girman ciki,sai da ta saka sannan ta shafa turaruka ta Maida rigar Baccin kamar ba ta sa komai ba ciki ya lafe ya dame.
Chapter 59 · 0% Book details