← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 68

Sashe 28

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan Beauty uku da haihuwa Nabeel ya sake kawo Hidaya da kansa,Abba Yana kofar gida shi da Jauro duk me zuwa barka a idon su take wucewa ta fito,Jauro yace gaskiya Dana ya iya kiwo har tana ta zama gwazarma,Abba yace uhm gata nan dai wlh tsila tana ta kauri,Hidaya tace Abba sannunku ta durkusa ta gaishe su,Abba yace wato Hidaya kasa zaki watsa min a Ido,kin nuna a gidana kafin ayi miki aure wahala kike Sha wato baki da kwanciyar hankali,gidan miji yafi gidan Uba,Anya in na mutu kuwa zaki yi kuka? sai da kika je gidan miji kika nuna kinfi Jin dadi acan,Ina rabaki da gorin da namiji yace a gidansa kika yi kiba,Jauro yace ai mu kowa ya shugo gidanmu sai ya canja.
Nabeel ne ya karaso suka gaisa basu ce Masa komai ba anyi sa'a yau.
Mohsin shopping mall ya shiga Yana yiwa me jego wasu siyayya da tace tana so,Hanan ce ta tsaya a kusa da shi da Mijinta Jibson suna siyayya,Jibson Yana cewa karki dauki abinda yafi karfina fa,a'a mayar da wannan wallahi ko kin dauka bazan biya ba,Hanan tayi murmushi tace to da uwar kudi na ni zan biya,Jibson Yana rike da hannunta,Mohsin ko kallon su baiyi ba Kuma yaji Muryar ya gane Hanan ce,Sai da zai bar wajen Yana Juyowa suka hada Ido da Mohsin,Hanan wai tunaninta zata cusawa Mohsin takaici ganin tayi kiba da kyau harda sake makalewa a Jikin Jibson ta furta my love muje,Mohsin tuni ma yayi gaba abinsa ko a gefen takalminsa.
Yace a ransa dan kin auri me kwal kwal har wani birga zaki min ni da nake da me kayan arziki,aikin banza kin dameni a raina zan barki ki auri wani,ya biya kudi ya wuce da ledojinsa,Yana fita suma sun fito ya tsaya a Jikin tsaleliyar motarsa,Hanan ta saci kallonsa takaici ya kamata tace da tuni ni zan shiga motar Nan na cuci kaina,wai mene a kishiya da na zauna na dinga kishin hauka,gashi yanzu ni a Napep zamu koma gida mijina ko Lifan baida shi,kishin hauka baiyi ba na cuci kaina,anzo min da arziki na kasa hakura,matar tasa taso mu zauna lafiya amma naki" gashi yanzu ban samu ko Wanda ya kama kafarsa ba,Mohsin motarsa ya bude zai shiga ya juyo suka hada Ido da Hanan tana tafiya da Jibson zasu shiga napep Amma Mohsin take kallo,gwalo ya mata ya saki murmushi ya sake mata gwalo karo na biyu,da sauri ta dauke kanta kamar zata yi kuka,Mota ya shige ya ja sai ya Kara gaba sai dariya yake Yana driving yace kinyi asara Hanan yarinya yaro me kama da Nailan sa kyakyawa gashi yanzu gidana wow ga mota Alhmdllh,dama ni ba ajinki bane kuruciya ce ta sa na nace Ina sonki,sai da Abba yace ban iya zabe ba amma lokacin Ina yaro ban San ciwon kaina ba yanzu kuwa sai Beauty,wacce in ka kirata kace Beauty mutane zasu juya harrr kallon wace Beauty ana kallonta za a tabbatar da taci sunanta,ke kuwa da kika dace ma da suna Larai aka taimaka aka saka miki Hanan.
Kidansa ya karo Yana bin wakar da yake ji har da rawa da kai yace Hanan kin mutu kin lalace an kare a me kwalkwal ko banza sanda kina matata ai kina shafa gashina,yanzu kuwa me zaki shafa kina kamowa zaki ji kamar kin shafa bayan kwarya,Mohsin sai dadi yake ji Hanan bata ci gaba ba, Yana Allah ya Kara, wannan dabiar Maza ce dama.

Annoor Iman dinsa ya daga sama ya cafe ta tare da dorata Saman bayan motarsa ya tsaya a Jikin Kafafunta hannunsa daya a gefenta dayan ma haka suna karewa juna kallo suna Hira a cikin gidansu,ya dawo daga unguwa ta fito tarensa shine ya Dorata Saman bayan motar.
Iman tana magana tana shagwaba kamar wata Yar yaye,tace Mamana tazo dazu wai kaji auren Sudan zata yi sun gama magana,yace mene na damuwa to yanzu ki gwada a kanki kice a ni da ke Hakan ta faru Dan na dawo baza ki aure ni ba? Iman tace da gudu ma ba wanda ya isa ya hanani wlh sai na aureka ba yara ba ko sabon gari market na Haifa dole na aureka,ai sai dai a sani a taskar labarai amma aurenka ya zama lahu,in aure abina in bar yaran suyi ta fushinsu,yace to ki kyaleta tayi aurenta duk abinda zai faru ya riga da ya faru,Haidar ya zama Yaya a gaske Kai jama'a Haidar surukina Dan iska ko gaishe shi bazan dinga yi ba,Iman tayi dariya tace Yayan guda,Juyawa yayi ta haye Bayansa suka wuce ciki abinsu.

Kwanan Babar Haneef biyu ta tafi,tana tafiya a ranar Mero ta Sha wanka ta shirya cikin Abaya me kyau ta fito,Ihsan tana Palo Shima Haneef Yana Palo tazo ta wuce ta tsakiyar palon ta wuce kitchen,gaba daya hankalin Haneef ya koma kanta,Ihsan ta kalle shi tana mamaki,Mero tana sani ta wuce kitchen ta fito da ruwa Wanda ba Sha zata yi ba,ta fito again Haneef ya kura mata Ido Yana so ya fuske amma ya kasa,zata wuce yace Dan taimaka min da juice,Mero ta ajiye ruwan a gefe ta kalle shi suka hada Ido kasa tayi da kanta ta dago da iya idonta murmushi suka yi a tare,har ta tafi ta juyo tace juice kace ko? yace yes,wanne kalar tana kashe Masa Ido,Haneef yace dole na Kara aure ba waliyyi bane ni wlh,a fili yace Apple,tace haba me za ayi da wani Apple gaskiya ni na Strawberry zaka Sha yafi dadi,kasa musawa yayi sai me cewa yayi Allah? yafi dadi ko? Mero tace sosai ma,kamar nafi son Apple din ni,shagwaba ta fara Allah a'a ni gaskiya strawberry pleassssssssse kaji....tsigar jikinsa ce tace wani yarrrrrrrrr.....yace okay it's fine kawo min to shike nan? Kai ta daga a shagwabe,Ihsan mikewa tayi tsaye tace wai meke faruwa ne a gidan Nan? Mero tace da aka yi me fa? Yar aiki ce ni nazo miki da shawara kika ki ji,ai mu indai muka Bada shawara aka ki dauka to mutum sai yaga tsiya wlh,bama son mutum ma da ya yake karewa damu bare yayi mana,abinda kika kasa nake miki a aikace Kuma Baki ga komai ba,duk kudinki da kike ji da shi da iliminki ni ba ruwana da shi aiki zan miki wlh.

Baiwar da Allah yayi mana ita ake fitowa da ita ana sarrafata tunda ke kin kasa kin wulakanta taki ta zama Bata da amfani,Ohhh kice dama son shi kike yi? ya halatta mana in ma Hakan ne ai ba haramun bane,wlh baza ki iya kishi Dani ba na tabbatar ko a kishiyarki nazo wlh sai kin sallami kanki,muke sa mutum yayi laifin dole fa,ki bar Raina mutun ko ya kika ganshi,ya kike so ayi miki? An fada miki gaskiya kinki ji,an miki fada an miki ta lallashi kinki to zama zaiyi yana jiranki ko me? bazai Mori kuruciyarsa ba jiranki zaiyi,so kike sai furfura ta fara feso Masa tukun,Yana da bukatar yara Yan dagwai dagwai,Haneef yace madalla da samun Yar aiki irinki wlh,ke Alkhairi ce,kina da hankali da hangen nesa.

Ihsan tace haka ka ce? Dama Amana ta kuke ci ka kawo min Karuwa a matsayin Yar aiki wlh Iyayenka sai sun San wannan zancen,Mero ta juya ta dakko lemo ta kawo Masa,ya karba Ihsan ta ja tsaki ta juya tace fasikai wlh sai ka sakeni bazan zauna da mazinaci ba,Mero tace ai kinji Illar baki San ma waye mijin ki ba zai iya Zina ko bazai iya ba baki sani ba har kin fara zargi.

Haneef tv ya canja channel yace sun fara film din nan,Mero tace ai Bata mutu ba? Bata mutu ba yarinyar to tunda bata mutu ba zanci gaba da kallo,Mero ta zauna suna Kallo abinsu,Ihsan ta shige daki tana kuka tana faman kiraye Kirayen kawayenta tana fada musu halin da take ciki.
Haneef yace Khadija Aure fa zanyi na dauki shawararki, gaban Khadija ya Fadi dam,tace wace zaka Aura din? yace akwai wata Yar kawar Mamana ta Dade tana son na nine naki yarda Kuma har yanzu tana nema na a waya,Mero tace ba irinsu zaka nema ba ai sai ka Kuma auro irin Ihsan,yanzu karka nemi kowa addua zamu tashi a tsaye mu fara Allah ya kawo Maka ta gari to daga nan Kuma ko kawarka ce kaji baka so ku rabu sai ka aure ta,Haneef yace Kawa? Ni bani da Kawa sai ke kadai fa,Mero tace ko nice ba addua za ayi ba kan wacce ta fada ayi da ita,Nima ko ba na so zan taimakeka,harka ce ta taimako kana cikin wani hali,Haneef yayi dariya a ransa tunanin Mero zata iya Masa wayo,kawai kallonta yake,ta kwanta Masa a rai ne kawai,yace to shike nan Allah ya tabbatar da Alkhairi,tace Amin ni Yar taimako ce abokina nane Kai zan iya taimaka Maka a ko wanne irin lokaci,yace da gaske tace to in Kuma wata ce Allah dai ya baka ta gari ni bana bakin ciki,dama Ina da saurayina a kauye,Haneef yace wanne irin kauye ana zaune lafiya kina da aboki kamar ni.
Ihsan ce ta fito a fusace ta haura sama ta shige bedroom din Haneef tayi Shirin bacci ta kwanta a Saman bed dinsa,Mero tunda taga ta hau sama tasan da dalili,dariya ta dinga yi a ranta tace tun ba a je ko Ina ba kenan.
Haneef sai da ya shige dakinsa ya samu Ihsan a bed dinsa a kwance tayi mala mala cikin rigar baccinta me kyau.

AsmaBaffa
[2/23, 8:35 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

36-40

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKI NE
~aminaidriskafe
Chapter 28 · 0% Book details