← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 68

Sashe 2

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wata Majalisar ce guda suke kafata a wajen sabo da Mero tana zuwa ta Jikin wajen suna Jin Muryar mace,Mero da Azima suka zo ta wajen Mero ta kwala da karfi Salamu Alaykum harda rige rigen amsawa,Goje yace Kai Muryar mace duniya ce wannan yarinya Allah ya mata albarka tana kwantar min da zuciya tana sani nishadi,rabon da naji Muryar mace tun Jamilu Tantiriya tana nan,Mero tace Kai Yan Maza har naji warin ku na gardawa ta nan,irin na ubanki cewar wani me Suna Balarebe,Mero tace Ubana Yana can Babata ta takura Masa shine ka zage shi ai abin yayi Masa yawa Allah ya isa,Ina ma zaki iya shugowa gidan nan bangaren mu,Mero tana dariya tace uban me zan muku in na shugo,Schola yace madarar Nido za a Baki iri iri harda me bulkodi ahayye ni dai Allah ya tsare ni neman Yar uwata mace,Mero da Azima suna ta dariya,Azima tace wayyo gashi bana kwana da wando,Goje yace ku jefa ni ciki Dan Allah,I love you a jefa ni ciki,Hanif ne yazo wucewa ta wajen yaji suna ta ihu da dariya,da izzarsa ya dan tsaya yaji Muryar Khadija ta daki dodon kunnensa tana cewa a gidanmu ga shimfidita ga Kaza taka kyankyasar 'ya'yanta a kauye,ni fa a birni na koyi tsafta a gidanmu sai mu gama wanke wanke mu wanke kafar mu da soson wanken Kwanon,su Goje suna ta dariya sabo da Fadi ba atambayeka ba din da Mero ke yi kullum sai ta fada musu abinda suke yi a gidansu na kauye.

Balarabe yace tab Allah yasa bakwa abincin siyarwa,Mero tace cab ai kuwa wallahi muna yi awara da Koko,tsohon dankwalina babata ta dauka da shi take tace gasarar Koko da awara,har skert dinta na ciki mun taba amfani da shi,Schola yace wayyo kunya ku matsa na boye kaina ni Schola Ina zan sa kaina Yar uwa tana ta bankada,Goje yace to ke Khadija baki da kanne ne? Me kace bana ji sai kayi da karfi,da karfi yace Baki da kanne? Mero tace daga ni sai kanina Yana kauye wani Dan banza shashasha nake ganinsa yanzu Kuma a haka sai kaji watarana wata har kasa bacci zata yi a kansa Allah ya kiyaye wacce taso kanina Muneer tayi asara,Azima tace ke muje dalla lokacin makaranta Kinga ke kike koyon Addini muje ko Kya samu ki daina wannan iskancin zancen naki,Dan Allah karku tafi cewar Muler muna Jin dadin mu kamar mu rungume ku,Mero tace wayyo Dan ma Baku ganni ba,Goje yace Allah? tace Allah da kunji a cike muke kamar ana bamu kaji,Goje har da dafe Kai yace Kuma fa da gaske ne Yana magana da sauran mazan,Hanif kallon su yayi kawai wani takaici ma ya kamashi mene abin dadi a nan,yace gaskiya ku Baku San ma mene abin dadi ba,Goje yace Kai ai sabon zuwa ne baka wani Dade ba shi yasa kake fadar haka da ragowar turirin mata a jikinka ka shugo bai gama barin jikinka ba shi yasa,ka kyale mu Muji dadin mu,Hanif yace Goodluck,Yana kudu Dan uwarka Yana Niger Delter, Goodluck ma ya sauka daga mulki karewa cewar Schola Yana ta faman cakaki,yace tun yaushe nake binka Ina naci Ina sonka ka zama budurwa ta kaki yarda wai Kai me tsafta shine yanzu zaka zo ka takura mana, Kai kudin naka ma ba kyauta kake ba, tunda kazo gidan Nan sai girman Kai sisinka ba Wanda ya taba ci,Hanif yace Allah ya kiyaye irinka Dan neman takashi yaci kudina,taka dai da alama baza tayi haske ba tunda dai ba irin mugun farin nan bane Kai ato farar takashi sai Spark,dariya Hanif yayi yace ko waye wannan Spark din oho da an tashi gori da shi ake kwatance.

Sai dare Mero ta gama surutunta zuwa dare ta koma dakin da bama a shiga Inda ta fasa,Hanif an kawo Masa take away hadadde da nama Yana ci Yana ta jira yaji muryarta sabo da da ta Saba zuwa Yana Jin surutunta Yana samu Dan sauki a ransa,sallama tayi ya amsa da kyar,tace me kake ci ne? yace nama,masu kudi Allah ya Kara budi,Ameen ya furta yace ba waje da na San miki,tace ga kafa dinga sako min Yan siri iri ta wajen zanci haka,yace to ya mike ko wanne Yankan nama sai ya raba shi gida uku ko hudu sannan ya samu ya Dan turowa Mero kamar wata tururuwa ta karbe ta cinye Kuma.

Naila ce ta fito tana rike da mara tana Nishi ta samu Spark a palon sama Yana kallo tace wash Allah Baby wayyo marata,zan mutu ta durkushe a wajen tana murkususu,a firgice Spark ya mike ya rike Naila yace me ya faru? Yanzu naji ciwon mutuwa ne wannan, Spark ya rude ya dauketa da sauri sauri suka tafi asibiti,Naila tana kuka tana bige bige a mota da kyar ma ya iya driving.
Suna zuwa aka karbeta aka fara bata agaji,sai da aka Dade Sannan mace Likita ta fito ta samu Spark hankali a tashe Yana jiran amsa meke faruwa.

Likita tace Sir Alhmdllh taji sauki amma kayi hakuri ciki ta samu baifi 4weeks ba Kuma ya zube,Spark yace ke likita ance bari yafi nakuda azaba kalau matata take? Indai matata kalau take shike nan Dan ciki taje gobe ma nayi sabo,dariya ya bawa likitar tace kalau take yace to Alhmdllh nan da jibi ma zan mata sabo Inshaallah,yanzu me ake bukata? Likita tace ai tafi karfin Pad sai dai pampers babba ake siyawa matan da suka haihu ko bari,Spark yace ban gane ba nufinki yanzu Jinin jikinta zubewa yake baku da hankali kuka ce kalau take,Likita tace ya gama fita cikin amma ai dole zata danyi jini kafin a samu ya dauke a hankali duk abinda ya dace anyi,Spark yace nifa shi yasa bana son matter din Nan ta ciki-ciki,ya fita yaje ya siyo abinda tace ya kawo mata,ta bawa nurse Dake asibitin kudi ne ko ba Yar jinya akwai masu yi.

Naila jikinta ta gyara ta shirya ya kawo mata wasu kayan ta canja ta fito kamar ba ita ba fes,waccen kayan Kuma data cire sabo da wadata sai tace ban taho da me wanke min ba ni na bar miki ko ki zubar,sai da ta fito Spark yace Ina kayan da kika cire? Ni wlh bazan iya wankewa ba na barwa nurse in bata so ta zubar.

Spark yace kut kayan da nake so nace dinkin Yana miki kyau yau fa ni nace ki saka su shine kika bayar wlh ba Yar iskar da zata saka,Naila tace sun baci fa sosai,yace ma wanke,sabo da baki San zafin nema ba in siya miki Abu me tsada kice a zubar kin San nawa ce atamfar? Kudin banza gareni,Naila kuka ta fara Dan kar a karbi kaya tasan halinsa ba kunyar uban kowa yake ji ba,kaina Yana ciwo kana ta min fada,Spark ba yanda ya iya yace sorry muje amma indai naga Nurse din nan sai na kalleta tunda ta sa min kaya ta shiga uku kurwata baza ta kyaleta ba,Naila tace ka kalleta Kuma? Tace kwarai ai asibitin nan sun shiga uku sun dinga ganina kenan,juyawa Naila tayi ciki da sauri tace Nurse kiyi hakuri ki bani kayana mijina yace bai yarda ba,Nurse tace ba komai gasu ma an zuba su a Leda in kinje gida Kya wanke,Naila ta karba ta koma mota a boot ya saka ledar kayan suka tafi gidan da magungunanta,suna zuwa gida ya bawa me aiki yace a wanke su tas in anyi normal da hannu a zuba su a washing machine tace to tana ta yiwa Naila sannu gata babba dama tasan komai

Tana gamawa ta hadawa Naila ruwan wanka ta gasa jikinta tayi wanka sosai tare da gyara kanta sannan tazo tayi kwalliya cikin wata fitted gown ta Leshi brown,abinci taci ta koshi Sannan ta Sha magani ta kwanta ta hau kiran waya Hello Ana gaisawa zata ce wlh bari nayi yanzu amma da sauki Alhmdllh mun dawo gida, kowa sai da ta fada Masa tayi bari,Spark ma haka har da kiran Mima yace Naila ce tayi bari, subhannallah Kuna asibiti yanzu? ai Abin yazo da sauki kalau take muna gida,to bari muzo cewar Mima.
Kafin wani lokaci gidan Spark ya cika da Yan Uwa su Chika,Ikhram duk sunzo,Naila ita barin ma sai murna take kamar wacce ta haihu,sai dare daga Chika sai Ikhram a gidan,Naila tana tsakiyar bed suna ta hira Spark ya shugo bedroom din,zama yayi a gefen Naila ya kalleta dariya ta bashi yanda take faman murna tayi bari,Chika tace wai korar mu zaka yi ne ai ka jira mu tafi kana babban Yaya Sam baka yin yayan Kai,Spark yace wai Yaya manya da wa zanyi wani Yaya wannan Dan iskan mijin naki da ya fini duniyanci,Arham ne ya shugo yace Chika ance ku fito na kaiku gida,Aunty ya Jikin? Naila tace Alhmdllh da sauki,Spark ya kalla yace Yaya Allah kawo wani da wuri,Spark yace a'a ba yanzu ba ai yanzu sabon Ango zan dawo,Naila ta zaro ido,Chika tana jinsu tace Kai Arham dan Allah muje"tafiya suka yi,Naila tace bari nayi wanka Yau bacci har da makara,Murmushi Spark yayi tare da furta zaki murmure ne dole na kwalbe,Naila yau dai bani da amfani ba mamora a jikina sai ayi hakuri Kuma,Spark yayi murmushi kawai.
Chapter 2 · 0% Book details